Show Description

Bayanai

Lokacin wannan shirin:
Talata

Shirin:
AREWA24

Bayani kan shirye-shiryen mu

Taka leda shiri ne na musamman domin masoya kwallon kafa. Masu gabatar da shirin, Nomiis Gee da Abubakar Ahmad za su rika yin tsokaci a kan sakamakon da yafi shahara, da kuma hasashen magoya baya a filayen kwallon kafa da ke nahiyar Turai. Shirin zai rika kawo muku tattaunawa da ‘yan wasa da kuma masu horarwa don baku damar sanin wainar da ake toyawa a fagen kwallo tsakanin kungiyoyin kwallon kafa da ke nan gida, da kuma tattaunawa akan wasannin da suka gabata. Shirin na Taka Leda zai rika yin duba kan hanyoyin horarwa da kuma burin da ‘yan wasan da ma masu horarwar ke son cimmawa a nan gaba.