Habibullah

Wannan shahararran shiri ne domin yara, wanda ke nuni da tarihin Rayuwar Annabi Muhammad, Amincin Allah da Albarka da Salama su kara tabbata a gare shi tun daga kuruciyarsa har zuwa lokacin karbar wahayi.

Kashi na Farko da na Biyu na Shirin Habibullah, labari ne daya kunshi Shekaru na daukakar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) da sahabbansa, tare da nuni da dabarunsa a wajen yaki da Basirarsa wajen shugabanci.

Sauran kashin da zasu zo a nan gaba za su zo da wasu darasi masu daraja da suka tabbatar da matsayi irin na Fiyayyen Halitta, Manzon Aminci (Sallallahu Alaihi Wasallam)

About the Author
A Website Developer and Digital Content Creator, CloudOps Engineer, Web Developer & Tech Community Lead
Scroll to top