Game da mu

AREWA24

An kafa tashar Arewa24 a Shekara ta 2014 domin cike gagarumin gibin samar da shirye-shirye masu nishadantarwa da tsarin rayuwa a harshen Hausa, wadanda su ke nuna hakikanin rayuwa a Arewacin Najeriya, da al’adu da kade-kade da fina-finai da fasahar zane da girke-girke da kuma wasanni.
A yau, sama da mutane miliyan 44 masu magana da harshen Hausa a fadin Najeriya da Afirika ta Yamma na kallon Tashar AREWA24 kyauta akan Tauraron Dan Adam ta Eutelsat da StartTimes (Tasha Mai Lamba 138) da tagwayan Tauraron Dan-adam din ‘Multichoice’ ta DSTv (Tasha #261) da GOtv (Tasha Mai Lamba 136) har ila yau da Tauraron Dan-adam ta Canal+ (Tasha Mai Lamba 285) a Kasashen Niger da Cameroun masu tsarin biya.
A Watan Nuwamba Shekara ta 2019 – Tashar AREWA24, ta kirkiro sabuwar Manhajarta mai suna “AREWA24 ON DEMAND,” Wata sabuwar Manhaja mai dauke da tsarin biyan kudi a fadin duniya da zata ta nuna shirye-shiryenta da ake kira “Subscription video-on-demand” wato (“SVOD”) da “Over-the-Top” wato (OTT). A yanzu, masu magana da Harshen Hausa da dukkanin Iyalansu da ke zaune a ko ina a fadin duniya, za su samu damar more kallon shirye-shirye iri daban-daban da suka lashe lambar yabo, wadanda al’ummar Najeriya da na yammacin nahiyar afirka ke jin dadin kallonsu yau da kullum a kan tashar AREWA24 da ke nuna shirye-shiryenta a tsawon sa’o’i 24 a ranakun mako. Domin shiga sabon tsarin Manhajar “AREWA24 ON DEMAND SVOD,” sai ku tafi Shafin http://tv.arewa24.com ko kuma ku neme mu a kan Manhajojin IOS da Goggle Play da Apple Tv Da Roku Channel Store da kuma Amazon Fire Tv.

Kafafen Sada Zumunta da na Wayoyin Hannu na matukar taimakawa al’ummar da ke tare da wannan Tasha da dukkanin shirye-shiryen da tashar keyi a harshen Hausa tare da yada manufofin kamfanin wanda ya shafi “Alfahari da al’adu.” Za ku iya samun kafofin sada zumunta a shafin yanar gizon AREWA24.com da Shafin facebook.com/AREWA24 da Instagram.com/AREWA24cvhannel da kuma twitter.com/AREWA24channel.
Arewa24 ta samu jagorancin kwararrun Ma’aikatan Talabijin da na Kafafen yada labarai da suka samar tare da budewa da gudanar da wasu daga cikin Tashoshin Talabijin na Duniya (The Africa Channel, Discovery Health Channel), suka rike manya-manyan mukamai a fitattun kamfanonin dake samar da Tauraron Dan Adam (DIRECTV, StarTimes) da kuma Tasoshin Talabijin na cikin gida Najeriya (TVC, AIT, NTA).
Arewa24 ta yi nasarar lashe lambobin yabo tun bayan da aka bude ta a Shekara ta 2014, wanda suka hada da shaharriiyar lamban yabo ta 2016 “Africa Magic Viewers Choice Award” wanda shirin ta mai farin jini na “Dadin Kowa” ya lashe.

Ku turo mana da email a advertising@AREWA24.com domin sanin damar da kuke da ita wajen tallata hajarku a gidan talabijin din Hausa na farko a Najeriya.

Scroll to top