Shirin “The 77 Percent” – Shirin Talabijin ne da DW ta shirya domin matasa – wanda tashar AREWA24 da ke Najeriya ta fassarashi zuwa harshen Hausa. Kamar yadda masu daukar nauyin shirin suka bayyana a ganawar su da manema labarai, tashar AREWA24 za ta nuna wannan shirin da harshen Hausa a lokutan da aka fi kallon tashar.
Shirin “The 77 Percent” ya samo sunansa ne daga kason matasan Afirka ‘yan kasa da shekaru 35, sannan aka tsara shi domin nuna rayuwarsu tare da “labarun mahimman abubuwan da suka fuskanta a rayuwarsu”. Shirin na tsawon mintuna 30, an taba nuna shi ne a baya da harsunan turanci da Portuguguese.
Shugaban tashar AREWA24 Jacob Arback, yayin da yake bayani game da karbar shirin, ya bayyana cewa,”Kara shirin “The 77 Percent” a cikin tsarin jadawalin shirye-shiryenmu wata babbar dama ce ga tashar AREWA24 wajen nuna batutuwa na zahiri, da kalubale da labarum nasarori daga matasa a kowanne bangare na fadin wannan nahiya. Muna alfahari da farin ciki da hadin guiwa tare da DW da kuma sadar da wannan shiri mai inganci ga matansamu masu magana da harshen Hausa da kuma iyalansu.”
Daraktan shirye-shiryen Afirka na DW, Claus Stacher, yayin da yake bayani game da kaiwar shirin kashi na 50 a wannan, ya bayyana cewa: “Mun tsara shirinmy ta yadda rukunin matasan da muka yi wannan shiri domin su za su fahimci shirin a matsayin shiri mai kayatarwa, da tsari sannan kuma an yi shi don ‘yan asalin nahiyar Afirka. Tsarin ‘yan Afirka, da tattaunawa da kuma samo mafita yana kara daraja ga abokan hadin guiwarmu na kafafen yada labarai na zamani, da radiyo da talabijin a wannan yanki. Muna da da tabbacin cewa wannan hadin guiwa da tashar talabijin kamar tashar AREWA24 zai kara budede kofofin samun hadin guiwa a nan gaba.
Tushi: DW.COM
You Might also like
-
Al Jazeera da AREWA24 sun yi hadin guiwa don fassara shirye-shirye na musamman da masu dogon zango zuwa harshen Hausa domin masu kallo sama da milyan 40 dake arewacin Nijeriya da kuma yankin Sahel
23 ga watan Nuwamba, 2021. Doha/Lagos. Nan ba da jimawa ba masu kallon tashar AREWA24 sama da milyan 40 da ke Arewacin Najeriya, da kasashen Nijar, da Chad da kuma Cameroon za su fara kallon shirye-shirye Al Jazeera na musamman da masu dogon zango na turanci, da aka fassarasu zuwa harshen Hausa, bisa wata sabuwar yarjejeniya da aka cimma kwanannan tsakanin Al Jazeera da kuma AREWA24.
Wannan yarjejeniya za ta bada damar kallon shirye-shiryen Al Jazeera na harshen Turanci a kan tashar tauraron ta AREWA24 dake kan tsarin kallo kyauta da kuma sauran kafafen tauraron dan adam na yankin da ke kan tsarin biyan kudi na: DStv, da StarTimes, da CANAL+ da kuma TSTV sannan kuma da tsarin kallo kai tsaye ta yanar gizo daga ko ina a duniya ta manhajar AREWA24 wato “AREWA24 On Demand.”
“Mun ji dadi sosai da wannan yarjejeniya, kasancewar shirye-shiryen Al Jazeera na harshen turanci za su dinga zuwa ga sabbin masu kallo dake yanki mafi girma a nahiyar Afirka da harshensu,” a ta bakin Mai rike da mukamin Babban Darakta mai kula da Sashen Sadarwa da Al’amuran Kamfanin a Duniya, Ramzan Alnoimi. Ya kara da cewa “Muna kokari muga mun fadada hanyoyi yada shirye-shiryen Al Jazeera da aka fassarasu da sauran harsuna a nan gaba.”
Shugaban tashar AREWA24, Jacob Arback, ya bayyana cewa: Tashar Al Jazeera da kuma kayatattun shirye-shiryenta za su samu karbuwa sosai a wajen masu kallon tashar AREWA24 na Arewacin Najeriya da kuma yammacin Afirka.”
Ya kuma kara da cewa “Mun yi matukar jin dadi game da wannan hadin guiwa, da kuma kasancewarmu tashar talabijin ta farko da za ta yada shirye-shiryen Al Jazeera masu inganci da harshen Hausa, harshen da sama da mutane milyan 90 ke magana da shi a Najeriya da kuma Yammacin Afirka.
Tahsar AREWA24 da sashen shirye-shiryenta, an kafa Tashar AREWA24 a shekarar 2014 domin cike wawakeken gibin da ake da shi a fagen shirye-shiryen nishadi da tsarin rayuwa da ake shiryawa da harshen hausa. Tashar AREWA24 taNA kaiwa ga mutane sama da milyan 40 masu magana da harshen Hausa a Najeriya da kuma yammacin nahiyar Afirka, sannan kuma kamfanin da ke da ofisoshinsa a Kano da kuma Lagos yana daga cikin kamfanonin ‘yan Afirka da ke kan gaba ta fuskar yada labarai, samar da shirye-shirye, da kuma yada shirye-shirye na talabijin.
Najeriya na daya daga cikin kasashen da aka fi kallon tashar Al Jazeera. Kai tsaye wannan yarjejeniya za ta bada damar fassara shirye-shiryen Al Jazeera zuwa harshen Hausa da kuma yada su ga daukacin masu kallo daga sassa daban-daban na yankin.
GAME DA TASHAR ALJAZEERA ENGLISH: Tashar harshen Turanci ta Al Jazeera tana gabatar da shirin labarun duniya da al’amuran yau da kullum da kuma sa mutane su san halin da ake ciki, wanda ya samo asali ta yin imani da cewa kowa yana da labarin da ya dace a saurara. Ta aikin jaridar da take yi na rashin nuna tsoro da kuma shirye-shiryenta da suka lashe labar yabo, tashar tana bada ingantattun labarai game da mutane a ko’ina, ba tare da la’akari da yankin da suka fito ko kuma al’adunsu ba. Tun daga lokacin da aka kaddamar da tashar a shekarar 2006, tashar Al Jazeera ta harshen Turanci ta samu yabo a fadin duniya bisa nuna rashin nuna son rai da kuma rahotanni na gaskiya, inda ta samu nasarar samun lambobin yabo daga bangarorin aikin jarida da aka fi girmamawa a duniya. Tashar da ke da babban ofishinta a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma wakilai a ofisoshinmu 69 da ke fadin duniya, ta kuma dauki wani sabon salo ta fuskar labaran duniya. Daga kasuwannin da suka ci gaba zuwa kasuwannin da ke tasowa, tashar tana kara gundarin abin da ya shafi mutane ta hanyar kasancewa a wajen da abu ke faruwa a gurare da dama. A yau, tashar AlJazeera ta harshen Turanci tana kaiwa ga gidaje sama da milyan 350 a kasashe 150 (Daga watan Fabrairun 2020), inda take yada ingantattun rahotanni da ke fadakarwa, karfafa guiwa da kuma kalubalantar yadda ake kallon abubuwa.
Domin karin bayani, sai ku danna wannan https://www.aljazeera.com/
GAME DA TASHAR AREWA24: Tahsar AREWA24 da shirye-shiryenta, an kafa Tashar AREWA24 a shekarar 2014 domin cike wawakeken gibin da ake da shi a fagen shirye-shiryen nishadi da tsarin rayuwa da ake shiryawa da harshen hausa, wadanda ke nuni da abubuwan da ake alfahari da su a rayuwar Arewacin Najeriya, da al’adu, da kade-kade, da fina-finai, da fasaha, da girke-girke da kuma wasanni. A yau, tashar AREWA24 tana kaiwa ga mutane sama da milyan 40 masu magana da harshen Hausa a Najeriya da kuma yammacin nahiyar Afirka a kan tauraron dan dan’adam na Eutelsat da ke kan tsarin kallo kyauta, da kuma kan tauraron dan adam na StarTimes da ke kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba 138), da kafafen tauraron dan’adam na kamfanin Multichoice guda biyu da ke kan tsarin biya kudi, wato DSTV (tasha mai lamba 261) da kuma Gotv (tasha mai lamba 101), da kuma tauraron dan adam na Canal+ a kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba #285) a Jamhuriyar Nijar, da Chadi da kuma Kamaru. AREWA24 na amfana da masu kallo da ke kasancewa da dukkanin shafukanta na yanar gizo a kan AREWA24.com, facebook.com/AREWA24, Instagram.com/AREWA24channel, and twitter.com/AREWA24channel.
Domin karin bayani game da AREWA24 sai ku ziyarci https://arewa24.com/company-overview/ ko kuma ku tuntubemu ta wannan adireshi: info@arewa24.com
Post Views: 30,450 -
Ina ma ‘KWANA CASA’IN’ na AREWA24 ya zama abin koyi
Fim din Kwana Casa’in, wato shirin Hausa dirama ne da a ke nunawa a tashar talabijin ta AREWA24, inda zubi da tsarin labarin ya sha bamban da finafinan da mu ka saba kallo, wanda ba su wuce tunanin yaro karami ba.
Labarin ya na magana ne a kan siyasar kasar nan da irin abubuwan da ke faruwa a jami’o’inmu da ma rayuwa ga bakidaya.
Tuntuni ya kamata a rika zakulo irin wadannan matsaloli, saboda su ne damuwarmu, amma sai finafinan da a ke kira na Hausa su ka duge ga rawa da waka da gasar nuna jiki da matsattsun wanduna.
A ciikin Kwana Casa’in, tsarin hoto kansa na daban ne, domin ya sha bamban da irin tsarin hoton da mu ka saba gani, saboda an yi amfani da na’urar daukar hoto mai matukar inganci ta yadda mai kallo zai ga kamar a gabansa abubuwan ke faruwa.Wuraren da a ka yi amfani da su irinsu asibitoci, ofisoshi, gidaje, makarantu ko gidan rediyo, nan ma abin jinjinawa ne, domin kuwa an yi amfani da wuraren da su ka dace ta yadda duk wanda ba dan kasa ba, idan ya kalla, zai ga tsantsar kama da gaskiya a cikin labarin, wanda hakan ma iyawa ce. Idan na nutsu Ina kallon Kwana Casa’in sai na ji tamkar gaske ne. Yadda masu mulki ke rayuwa da rayuwar talaka a wannan zamani da yadda a ke amfani da talaka, domin kama madafun iko duk an bayyanar da shi. Ina da yakinin kafin labarin ya kare mutane da dama za su dauki darasin rayuwa. Lokacin da na ga hotunan wasu jaruman Kannywood a cikin Kwana Casa’in kafin na fara kallon fim din, sai da na ji jiki na ya yi sanyi, saboda Ina tsoron kar su bata dirimar ta yadda za mu rika kallon ta kamar shirme, amma abin da ya burge ni shi ne yadda su ka shiga su ka bata a cikin shirin ba tare da kawo mishkila ko mayar da abin wasan yara ba. Hakan ya nuna ma ni kenan da za su sami labari mai inganci da kayan aiki, sannan su sako masu ilimin a cikin nasu shirye-shiryen, kila su ma za su samu su mike a Kannywood din kenan. Yadda jaruman su ka nuna dagiya da tsantsar kwarewa sosai, ya yi kyau matuka ta yadda ko wadanda su ka saba kallon finafinan kasashen ketare za su jinjina masu domin kasashen da su ka cigaba su na shirya dirama mai dogon zango ko finafinai kan matsalar da su ke fuska a kasar fiye da shirme irin wanda a ke yi a finafinan da mu ka saba gani. Da alama dai Kwana Casa’in shi ne labarin da ya ke kokarin taushe shirin dadin Kowa na Arewa 24 din dai, domin kamar yadda a ka kasa samun wani shirin dirama da zai yi karo da Dadin Kowa daga masana’antar Kannywood, watakila AREWA24 din ce dai kadai za ta iya yin karo shi da wannan sabon shiri tsararre na Kwana Casa’in. Tsawon lokacin da na dauka Ina kallon shirin Hausa na Kannywood lallai na gano wa Kannywood makarantar da za su kara ilmi. Sannu a hankali AREWA24 za ta maye gurbin shirin Hausa dirima, saboda su ne su ke tattauna abinda ya dame mu a kasa, ba rawa da juyi gaban allunan talabijin ba. Fadila H Aliyu Kurfi marubuciya ce mai sharhi kan al’amuran yau da kullum kuma ’yar gwagwarmaya.
Za a iya samun ta a imel: fadilakurfi@gmail.com ,
Facebook: Fadila H Aliyu Kurfi.
Read More at: https://hausa.leadership.ng/2019/04/18/ina-ma-kwana-casain-na-arewa-24-yazama-abin-koyi/Post Views: 9,090 -
AREWA24 Ta Kaddamar Da Sabon Dakin Shirye-Shirye
Tashar AREWA24tashar da ta yi fice wajen nishadantarwa da tsarin rayuwa da harshen Hausa a Kasar Nijeriya, na sanar da ku cewa, ta bude sabon Dakin Yada Shirye-shiryenta mai dauke da tsarika irin daban-daban da wasu sababbin shirye-shirye da za a fara a zango yada shirye-shiryenta karo na biyu. Sabon Dakin Yada shirye-shiryen zai taimakawa sabon salon shirin GARI YA WAYE da sabon salon shirin Sharhin Wasanni wato (Sport Central) da kuma sabon Salon Kayataccen shirin KUNDIN KANNYWOOD har ila yau, da SHARHIN FINA-FINAN KANNYWOOD. haka kuma, Tashar zata sake kawo muku shirin dake tattaunawa a kan lafiya da Cututtuka da Magani a cikin wani sabon salo da mai gabatar da shirin Lafiya Jari wanda za a rika gabatar da shi a Garin Abuja. wanda zamu karkare wannan sabon zango na uku na shirye-shiryen Nishadantarwa da kuma tsarin rayuwa da shirin ‘Haske; Matan Arewa’ wanda zai sada ku da shaharrrun matan Arewacin Nijeriyu. haka kuma, Tashar AREWA24 zata gabatar muku da sababbin Fina-finan Kannywood har karshen wannan shekara.
Bugu da kari, dan gane da sababbin shirye-shirye da Tashar AREWA24 ke kawo wa masu kallo, Tashar AREWA24 za ta kawo wa masu kallon sabbabin Fina-finan daga tashar ‘Zee World Series’ ‘Bhagya Lakshmi’ da wani fitaccen sabon Wasan Kwaikwawo daga Kasar ‘Turkish’ “Prisoner of love’ wato ‘Tarkon Kwana’ da wasu sabbabbin Fina-finan Kasar Indiya. kamar dukkaninn shirye-shiryen kasashen ketare masu lasisi na Tashar AREWA24. duk wadannan guntattakin Fina-finan na Series da na Fina-finan Indiya ana daukarsu ne da shiryasu da Harshen Hausa a Daikin daukar Sauti na Tashar AREWA24.
Babbar Mai Gabatar da Shirye-shiryen ‘GARI YA WAYE’ Aisha Lawal ta ce, ‘Masu Kallon Tashar AREWA24 sun cancanci a gabatar musu da kyawawan shiri da zai birge su, kuma ba dare ba rana mun kwashe wata da watanni muna ta aiki tukuru don ganin mun kawata sabon Dakin Yada shirye-shiryenmu mai fasali daban-daban. Sabon shirinmu na ‘Gari ya Waye’ ba zai tsaya ga sakawa masu kallo da sabon salon gabatar da shirin ka dai bane, Amma, har da saka musu da sabbabin masu gabatar da shirin wato Nana Musa da kuma Muhammad Abubakar Suleiman.’ An kafa tashar AREWA24 a Shekara ta 2014 domin cike gagarumin gibin samar da shirye-shirye masu nishadantarwa da tsarin rayuwa a Harshen Hausa, wadanda su ke nuna hakikanin rayuwa a Arewacin Najeriya, da Al’adu da Kade-Kade da Fina-Finai da Fasahar zane da Girke-Girke da kuma Wasanni. A yau, sama da mutane miliyan 80 masu magana da Harshen Hausa a fadin Najeriya da makwabtansu na Yammacin Afirika na kallon Tashar AREWA24 da ake haskawa a kan Tauraron Dan Adam ta Eutelsat a kyauta, a Kasa Najeriya kuma, ana iya kama ta a kan Dikodar Tsarin biya ta StarTimes Tasha ta 138 da kuma Dikododin Kamfanin Multichice masu guda biyu masu Tsarin Biya wato DSTV Tasha ta 261 da kuma GOtv Tasha ta 101.
GAME DA AREWA24: Tashar AREWA24 ( arewa24.com) tasha ce ta farko a kasar nan kuma tashar daya tilo dake shiryawa da kuma yada shirye-shiryenta a kan Tauraron Dan Adam cikin harshen Hausa Wadda kuma aka sadaukar da ita don nishadantar da iyali, Tashar AREWA24 ta Mayar da hankalin wajen bunkasa da yada shirin talabijin da harshen Hausa, domin cike gibin da masu magana da harshen Hausa ke fuskanta a fadin duniya, wadanda da yawansu ke dawowa kallon Tashar AREWA24 ta hanyar amfani da Manhajar Yanar Gizo a matsayin wata hanya da zata sada su da Al’adunsu da kuma Al’ummun Duniya.
Ana saka Shirye-shiryen Tashar AREWA24 a kowanne mako a kan shafin Youtube.com/Arewa24channel, haka kuma tashar tana samun matukar karuwa ta hanyar tattaunawa da masu kallonta a shafukanta na sada zumunta kamar Arewa24.com da Facebook.com/AREWA24 da Instagram.com/AREWA24channel da kuma twitter.com/AREWA24channel
Don karin bayani, sai ku tuntubemu a info@arewa24.com
Post Views: 8,591