Al Jazeera da AREWA24 sun yi hadin guiwa don fassara shirye-shirye na musamman da masu dogon zango zuwa harshen Hausa domin masu kallo sama da milyan 40 dake arewacin Nijeriya da kuma yankin Sahel

23 ga watan Nuwamba, 2021.  Doha/Lagos. Nan ba da jimawa ba masu kallon tashar AREWA24 sama da milyan 40 da ke Arewacin Najeriya, da kasashen  Nijar, da Chad da kuma Cameroon za su fara kallon shirye-shirye Al Jazeera na musamman da masu dogon zango na turanci, da aka fassarasu zuwa harshen Hausa, bisa wata sabuwar yarjejeniya da aka cimma kwanannan tsakanin Al Jazeera da kuma AREWA24.

Wannan yarjejeniya za ta bada damar kallon shirye-shiryen Al Jazeera na harshen Turanci a kan tashar tauraron ta AREWA24 dake kan tsarin kallo kyauta da kuma sauran kafafen tauraron dan adam na yankin da ke kan tsarin biyan kudi na: DStv, da StarTimes, da CANAL+ da kuma TSTV sannan kuma da tsarin kallo kai tsaye ta yanar gizo daga ko ina a duniya ta manhajar AREWA24  wato “AREWA24 On Demand.”

“Mun ji dadi sosai da wannan yarjejeniya, kasancewar shirye-shiryen Al Jazeera na harshen turanci za su dinga zuwa ga sabbin masu kallo dake yanki mafi girma a nahiyar Afirka da harshensu,” a ta bakin Mai rike da mukamin Babban Darakta mai kula da Sashen Sadarwa da Al’amuran Kamfanin a Duniya, Ramzan Alnoimi. Ya kara da cewa “Muna kokari muga mun fadada hanyoyi yada shirye-shiryen Al Jazeera da aka fassarasu da sauran harsuna a nan gaba.”

Shugaban tashar AREWA24, Jacob Arback, ya bayyana cewa: Tashar Al Jazeera da kuma kayatattun shirye-shiryenta za su samu karbuwa sosai a wajen masu kallon tashar AREWA24 na Arewacin Najeriya da kuma yammacin Afirka.”

Ya kuma kara da cewa “Mun yi matukar jin dadi game da wannan hadin guiwa, da kuma kasancewarmu tashar talabijin ta farko da za ta yada shirye-shiryen Al Jazeera masu inganci da harshen Hausa, harshen da sama da mutane milyan 90 ke magana da shi a Najeriya da kuma Yammacin Afirka.

 

Tahsar AREWA24 da sashen shirye-shiryenta, an kafa Tashar AREWA24 a shekarar 2014 domin cike wawakeken gibin da ake da shi a fagen shirye-shiryen nishadi da tsarin rayuwa da ake shiryawa da harshen hausa. Tashar AREWA24 taNA kaiwa ga mutane sama da milyan 40 masu magana da harshen Hausa a Najeriya da kuma yammacin nahiyar Afirka, sannan kuma kamfanin da ke da ofisoshinsa a Kano da kuma Lagos yana daga cikin kamfanonin ‘yan Afirka da ke kan gaba ta fuskar yada labarai, samar da shirye-shirye, da kuma yada shirye-shirye na talabijin.

 

Najeriya na daya daga cikin kasashen da aka fi kallon tashar Al Jazeera. Kai tsaye wannan yarjejeniya za ta bada damar fassara shirye-shiryen Al Jazeera zuwa harshen Hausa da kuma yada su ga daukacin masu kallo daga sassa daban-daban na yankin.

GAME DA TASHAR ALJAZEERA ENGLISH: Tashar harshen Turanci ta Al Jazeera tana gabatar da shirin labarun duniya da al’amuran yau da kullum da kuma sa mutane su san halin da ake ciki, wanda ya samo asali ta yin imani da cewa kowa yana da labarin da ya dace a saurara. Ta aikin jaridar da take yi na rashin nuna tsoro da kuma shirye-shiryenta da suka lashe labar yabo, tashar tana bada ingantattun labarai game da mutane a ko’ina, ba tare da la’akari da yankin da suka fito ko kuma al’adunsu ba. Tun daga lokacin da aka kaddamar da tashar a shekarar 2006, tashar Al Jazeera ta harshen Turanci ta samu yabo a fadin duniya bisa nuna rashin nuna son rai da kuma rahotanni na gaskiya, inda ta samu nasarar samun lambobin yabo daga bangarorin aikin jarida da aka fi girmamawa a duniya. Tashar da ke da babban ofishinta a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma wakilai a ofisoshinmu 69 da ke fadin duniya, ta kuma dauki wani sabon salo ta fuskar labaran duniya. Daga kasuwannin da suka ci gaba zuwa kasuwannin da ke tasowa, tashar tana kara gundarin abin da ya shafi mutane ta hanyar kasancewa a wajen da abu ke faruwa a gurare da dama. A yau, tashar AlJazeera ta harshen Turanci tana kaiwa ga gidaje sama da milyan 350 a kasashe 150 (Daga watan Fabrairun 2020), inda take yada ingantattun rahotanni da ke fadakarwa, karfafa guiwa da kuma kalubalantar yadda ake kallon abubuwa.

Domin karin bayani, sai ku danna wannan https://www.aljazeera.com/

GAME DA TASHAR AREWA24: Tahsar AREWA24 da shirye-shiryenta, an kafa Tashar AREWA24 a shekarar 2014 domin cike wawakeken gibin da ake da shi a fagen shirye-shiryen nishadi da tsarin rayuwa da ake shiryawa da harshen hausa, wadanda ke nuni da abubuwan da ake alfahari da su a rayuwar Arewacin Najeriya, da al’adu, da kade-kade, da fina-finai, da fasaha, da girke-girke da kuma wasanni. A yau, tashar AREWA24 tana kaiwa ga mutane sama da milyan 40 masu magana da harshen Hausa a Najeriya da kuma yammacin nahiyar Afirka a kan tauraron dan dan’adam na Eutelsat da ke kan tsarin kallo kyauta, da kuma kan tauraron dan adam na StarTimes da ke kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba 138), da kafafen tauraron dan’adam na kamfanin Multichoice guda biyu da ke kan tsarin biya kudi, wato DSTV (tasha mai lamba 261) da kuma Gotv (tasha mai lamba 101), da kuma tauraron dan adam na Canal+ a kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba #285) a Jamhuriyar Nijar, da Chadi da kuma Kamaru.  AREWA24 na amfana da masu kallo da ke kasancewa da dukkanin shafukanta na yanar gizo a kan AREWA24.comfacebook.com/AREWA24Instagram.com/AREWA24channel, and twitter.com/AREWA24channel.

 

Domin karin bayani game da AREWA24 sai ku ziyarci https://arewa24.com/company-overview/ ko kuma ku tuntubemu ta wannan adireshi:  info@arewa24.com

About the Author
A Website Developer and Digital Content Creator, CloudOps Engineer, Web Developer & Tech Community Lead
Scroll to top