AREWA24 ta kaddamar da sabon jadawalin shirye-shiryenta na zango

Tashar AREWA24, tashar Hausa da ke kan gaba wajen nishadantarwa da tsarin rayuwa a Najeriya, tana sanar da fitowar jadawalin sabbin shirye-shiryenta na zango na hudu a wannan shekara da kuma zangon farko na shekarar 2019, wanda ya kunshi sabon wasan kwaikwayon tashar da aka dade ana jira, wanda zai zo a watan Janairu, kari a kan wasan kwaikwayon “Dadin Kowa” da tashar ke nunawa a halin yanzu wanda ta dade tana nunawa wanda kuma ya samu lambar yabo. A halin yanzu ana nan ana shirya wannan sabon wasan kwaikwayo mai kayatarwa, kuma ana tsammanin zai kawo wani sabon sauyi da inganci a bangaren shirye-shiryen talabijin da harshen Hausa.
Sabon jadawalin shirye-shiryen tashar AREWA24 da zai fara a watan Oktoba, ya kunshi shirin “Amo daga Arewa”. Wannan shiri na kade-kade ya kunshi gabatar da wakoki kai tsaye da tattaunawa da fasihan mawaka daga fadin Arewacin Najeriya, da suka hada da mawakan gargajiya da na R&B da masu wakokin sanyaya ruhi da kuma mawakan addinai. Shirin “Amo Daga Arewa” ya tattara kada-kaden gargajiya na al’ada da dama da yankin Arewacin Najeriya ke da su, kari a kan shahararrun shirye-shiryen AREWA24 na
Hip Hop.
A zangon na hudu , shirin nan na “Matasa@360” zai sake dawowa da wani sabon salo da kuma sabbin masu gabatarwa. Shirin na “Matasa@360” shiri ne na matasa da yayi daidai da zamani kuma yake bi lungu da sako, tare da mayar da hankali a kan basira da kirkira da kuma fasahar matasan Arewacin Najeriya.
Haka kuma shirin zai dinga tattauna kalubale na zahiri da matasan yankin ke fuskanta da kuma wahalhalun da suke fama da su a yau da kullum. Bangarorin da shirin ya kunsa za su nuna yadda matasan Arewacin Najeriya ke rayuwarsu ta yau da kullum, da alakarsu da sauran mutane, da kafafen yada labarai, da sana’o’i, da wasanni, da al’amuran yau da kullum, da rayuwar makaranta, da fasaha da sauran bangarorin da matasa daga dukkan fadin duniya ke da alaka da su.

Haka kuma tashar AREWA24 za ta fara gabatar da shirin “Haske: Matan Arewa” kashi na hudu, wanda jajirtattun mata daga Arewacin Najeriya ke bayyana labarinsu cike da kwarin guiwa. Suke kuma bijirewa wasu dabi’u na zamantakewa da al’adu don su zamo shugabanni, ko yan kasuwa, ko masu sana’o’i, ko masu wayar da kai a yankunan karkara, ko masu shirya fina-finai da sauransu, Wadannan hazikan mata kan bayyana ci gabansu, da fadi-tashinsu, da matsalolin da suke fuskanta, da kuma nasarorinsu.
Cikon sabbin shirye-shiryen da tashar AREWA24 za ta gabatar a zango na hudu a wannan shekarar su ne sabbin fitattun fina-finan Kannywood daga kwararrun daraktocin masana’antar. A yanzu tashar AREWA24 ta yi fintinkau ga kowacce tasha dake yankin Arewa, idan ana magana a kan nuna fitattun fina-finan Kannywood.

Sannan kuma tashar ta samar da shirye-shirye don manyan gobe da ke kallon shahararrun shirye-shiryen yara a tashar safe da yamma.
Haka kuma tashar tana sanar da daukar manyan kuma kwararrun ma’aikatan shirye-shirye da ta yi a dakin shirye-shiryenta da ke Kano: wato Kadiri Yusef da Evans Ejiogu, wadanda kowannensu ya zo da irin kwarewar da ya dade yana samu da irin shuhurar da ya yi a fagen shirin talabijin da kafafen yada labarai a Lagas, zuwa kano.
Kadiri Yusef dai wani babban ma’aikacin shirye-shirye ne a gidan talabijin na Silverbird Television, inda ya yi aiki tun daga shekarar 2004 zuwa 2017. Kadiri ya zamo shugaban sashen shirye-shirye na tashar Silverbird Television a shekarar 2006 inda ya bada umarni a manyan shirye-shiryen Silverbird da suka ciri tuta, da kuma dukkanin shirye-shiryenta na kai-tsaye. A tashar AREWA24, shi ne mai kula da bangaren bada umarni da tsara dukkanin shirye-shirye daban-daban da ake gabatarwa a dakin shirye-shirye.
Evans Ejiogu ya kasance kwararren mai samar da shirye-shiryen talabijin, mai shiryawa, mai bada umarni, marubuci sannan kuma mai tace hotunan bidiyo. Baya ga wannan gogewa da kwarewa a fagen daukacin nau’ikan shirye-shirye da yake da su, Evans ya kawowa tashar AREWA24 dabarun kasuwanci da ya samu a tsawon shekarun da ya shafe a fagen sadarwa da tallace-tallace. Evans yayi aiki a babban dakin gabatar da shirye-shirye , da wasan kwaikwayo na talabijin, da gajerun fina-finai, da tallace-tallace, da gidan radiyo da kuma shafukan yanar gizo, inda yake taimakawa wajen kawo babban matakin kwarewa da inganta shirye-shirye a tashar AREWA24.

Babban Shugaban tashar AREWA24 Jacob Arback ya bayyana cewa, “Mun yi gagarumar sa’ar samun manyan ma’aikata da ke da irin wannan kwarewa da gogewar aiki don yin aiki a tashar AREWA24. Evans da Kadiri ba su tsaya iya bada gudunmawa ga jajirtattun ma’aikatanmu na shirye-shirye da suka tarar da kuma daga darajar shirye-shiryen tashar ba, suna kuma taimakawa wajen bunkasa bangaren aiyukan talabijin da kafafen yada labarai na Arewaci Najeriya.”

GAME DA TASHAR AREWA24: An kafa Tashar AREWA24 a shekarar 2014 domin cike wawakeken gibin da ake da shi a fagen shirye-shiryen nishadi da tsarin rayuwa da ake shiryawa da harshen hausa, wadanda ke nuni da abubuwan da ake alfahari da su a rayuwar Arewacin Najeriya, da al’adu, da kadekade, da fina-finai, da fasaha, da girke-girke da kuma wasanni. A yau, mutane masu Magana da harshen hausa sama da milyan 80 a Najeriya da kuma yammacin Afirka ne ke lallon tashar AREWA24 ta tauraron dan dan’adam na Eutelsat kyauta, haka kuma, a Najeriya ana kallon tashar akan StarTimes da ake biya (tasha mai lamba 138), da kuma kafar tauraron dan’adam ta StarTimes DTH (tasha mai lamba 538) sannan da kafafen tauraron dan’adam na kamfanin Multichoice guda biyu da ake biya, wato DSTV (tasha mai lamba 261) da kuma Gotv (tasha mai lamba 101).

Haka kuma ana dora ingantattun shirye-shiryen tashar AREWA24 kowanne mako a shafin youtube.com/AREWA24channel, sannan tashar na amfana da masu kasancewa da ita a shafukanta na AREWA24.com, da facebook.com/AREWA24, da Instagram.com/AREWA24channel, da kuma na twitter.com/AREWA24channel. Domin karin bayani sai ku tuntubi: info@arewa24.com

About the Author
A Website Developer and Digital Content Creator, CloudOps Engineer, Web Developer & Tech Community Lead
Scroll to top