GAME DA MU 2017-12-01T01:57:41+01:00

GAME DA MU

An kafa tashar Arewa24 a Shekara ta 2014 domin cike gagarumin gibin samar da shirye-shirye masu nishadantarwa da tsarin rayuwa a harshen Hausa, wadanda su ke nuna hakikanin rayuwa a Arewacin Najeriya, da al’adu da kade-kade da fina-finai da fasahar zane da girke-girke da kuma wasanni. A yau, sama da mutane miliyan 80 masu magana da harshen Hausa a fadin Najeriya da makwabtan kasashe na kallon tashar Arewa24 cikin sa’oi 24 a dukkanin ranakun mako kyauta akan Tauraron Dan Adam. A yanzu haka, ana kallon tashar Arewa24 akan shahararriyar Na’urar Tauraron Dan Adam ta DSTv da GOtv masu tsarin biya. Ana iya samun dukkanin jerin shirye-shiryen tashar Arewa24 kyauta akan Shafin ‘YouTube’ kai tsaye bayan an nuna su. Manhajojin Tashar Arewa24 na zamani, da Kafafen Sada Zumunta da na Wayoyin Hannu na matukar taimakawa al’ummar da ke tare da wannan Tasha da dukkanin shirye-shiryen da tashar keyi a harshen Hausa tare da yada manufofin kamfanin wanda ya shafi “Alfahari da al’adu.”

Dakin shirye-shirye na tashar Arewa24 ya samar da shirye-shirye na sama da Sa’o’I 2,000 duk da harshen Hausa wadanda suka shafi tsarin rayuwa da kuma nishadantarwa da sauran nau’ikan shirye-shirye daban-daban, sannan zata ci gaba da samar da shirye-shiryenta masu inganci da nishadantarwa domin jin dadin masu kallon tashar.

Arewa24 ta samu jagorancin kwararrun Ma’aikatan Talabijin da na Kafafen yada labarai da suka samar tare da budewa da gudanar da wasu daga cikin Tashoshin Talabijin na Duniya (The Africa Channel, Discovery Health Channel), suka rike manya-manyan mukamai a fitattun kamfanonin dake samar da Tauraron Dan Adam (DIRECTV, StarTimes) da kuma Tasoshin Talabijin na cikin gida Najeriya (TVC, AIT, NTA). Arewa24 ta yi nasarar lashe lambobin yabo tun bayan da aka bude ta a Shekara ta 2014, wanda suka hada da shaharriiyar lamban yabo ta 2016 “Africa Magic Viewers Choice Award” wanda shirin ta mai farin jini na “Dadin Kowa” ya lashe.


SHIRYE-SHIRYEN MU

Shirin Tattaunawa Don Matasa

Shirin tattaunawa yakan habaka kwazo, kuma ya bawa matasa maza da mata damar amayar da abinda yake zuciyar su, zai cusawa matasan Are-wacin Nigeria alfahari akan al’adar su, sannan kuma ya basu kwarin gwiwa wajen dogaro da kai, hadin kai da girmama juna.

Shirin Al’Adu da Ra’Ayoyin Jama’a

Wadannan shirye-shiryen sun hada, da shiri don yara, shirin kumallon safe da sauran shirye-shiryen da suka hada da kade-kade, fina-finai, al’adu, salon kwalliya, wasanni da girke-girken Arewacin Nigeria.

Fina-Finan Hausa da Wasannin Kwaikwayo

Gidan talabijin na AREWA 24 zai kawo muku fina-finan Hausa masu yawan gaske da kuma wasan kwaikwayo na kashin kanta mai suna: Dadin Kowa.

Shirye-Shirye na Kasashen Waje

Zamu kawo muku shirye-shirye daga kasashen waje wadanda suka dace da al’adun mu kamar, fina-finai, wasannin kwaikwayo shiri don yara da tarihi wadanda aka yi ko aka fassara da harshen Hausa.


EMPLOYMENT OPPORTUNITIES

AREWA24 is looking for a part-time Accounting Consultant to set up and manage accounting system and transactions and advise on financial issues. Click here to download the job description.


ADVERTISE WITH US

Ku turo mana da email a advertising@AREWA24.com omin sanin damar da kuke da ita wajen tallata hajarku a gidan talabijin din Hausa na farko a Najeriya.


TUNTUBE MU a info@arewa24.com