{"id":5533,"date":"2024-07-16T15:06:36","date_gmt":"2024-07-16T14:06:36","guid":{"rendered":"https:\/\/arewa24.com\/?p=5533"},"modified":"2024-07-16T15:06:36","modified_gmt":"2024-07-16T14:06:36","slug":"arewa24-na-sanar-da-sabon-jadawalin-shirye-shirye-na-wasannin-kwaikwayo-da-take-shiryawa-da-fina-finai-da-shirye-shiryenta-na-cikin-gida-a-yayin-da-kamfanin-ke-cika-shekaru-10-da-kafuwa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/arewa24-na-sanar-da-sabon-jadawalin-shirye-shirye-na-wasannin-kwaikwayo-da-take-shiryawa-da-fina-finai-da-shirye-shiryenta-na-cikin-gida-a-yayin-da-kamfanin-ke-cika-shekaru-10-da-kafuwa\/","title":{"rendered":"AREWA24 na sanar da sabon jadawalin shirye-shirye na wasannin kwaikwayo da take shiryawa, da fina-finai, da shirye-shiryenta na cikin gida a yayin da kamfanin ke cika shekaru 10 da kafuwa"},"content":{"rendered":"<p>AREWA24, tashar talabijin da ke kan gaba wajen ya\u0257a shirye-shirye masu nisha\u0257antar da iyali da tsarin rayuwa cikin harshen Hausa, wadda ke da ofishin samar da shirye-shirye a Najeriya da yammacin Afirka, tana sanar da wani gagarumin sabon jadawali na shirye-shirye, da fina-finai da wasannin kwaikwayo da take shiryawa da kuma kar\u0253ar wasannin kwaikwayo na Hausa masu dogon zango domin nuna su a mahajarta ta kallo kai tsaye, wato AREWA24 On Demand. <\/p>\n<p>Domin bukin murnar cikar AREWA24 shekaru 10, tashar ta kaddamar da sabon shirinta na matasa, wato, \u201cArewa Gen-Z,\u201d wanda aka shirya domin matasan Arewacin Najeriya masu \u0257inbin yawa. Matasa ne ke shirya wa, kuma gabatar da shirin \u201cArewa Gen-Z\u201d, wanda ke mayar da hamkali a kan irin \u0199alubalen da a yanzu matasa ke fama da shi kowacce rana. Shirin na mintuna 30 da ake gabatarwa a kowanne mako, zai dinga kawo labarun nasarori, da fasaha, da wa\u0199e-wa\u0199e, da kuma al\u2019adun matasa. Shirin zai kasance wata farfajiya domin abubuwan da aka san matasa da shi domin jawo hankalin matasa a fa\u0257in Arewacin Najeriya. <\/p>\n<p>Haka kuma nan ba da da\u0257ewa ba AREWA24 za ta fito da fim \u0257inta na farko mai gajeren zango,  mai sunan, \u201cThe Jaru Road,\u201d wani labari mai \u0199ayatarwa kuma na asalin Arewacin Najeriya, wanda aka shirya da harshen Turanci, kuma domin masu kallo dake fadin Afirka da ma sauran sassa na duniya. Kamfanin ya tsara shirya \u0199arin wasu fina-finai hu\u0257u a 2024 &#8211; 2025, wasu da harshen Hausa domin masu kallo a Najeriya da kuma Yammacin Afirka, wasu kuma da harshen Turanci domin masu kallo a dukkanin fa\u0257in Afirka da duniya baki \u0257aya. Bugu da \u0199ari, AREWA24 za ta \u0199addamar da shirin \u201cClimate Change Africa,\u201d wani shiri da zai yi duba kan tasirin da sauyin yanayi yake yi a Najeriya, da fa\u0257in Afirka, da sauran sassan duniya baki \u0257aya. <\/p>\n<p>\u201cWa\u0257annan sabbin shirye-shirye suna nuna irin yadda AREWA24 ta mayar da hankali wajen samar da shirye-shiryenta na cikin gida da suke da ala\u0199a da halin da al\u2019umma ke ciki, da wasannin kwaikwayo, da kuma fina-finai, sannan bisa matakin ingancin shirye-shirye a duniya.\u201d A ta bakin Shugaban Sashen Kasuwanci da Tallace-tallace kuma Mataimakon Shugaban AREWA24, Celestine Umeibe, ya bayyana cewa \u201cwa\u0257annan sabbin shirye-shirye suna nuna yadda muke iya samar da shirye-shirye masu \u0199ayatarwa domin masu kallonmu na cikin gida, da kuma shirye-shiryen da za su kai har zuwa kasahen duniya, da kuma nunawa sauran masu kallo na nahiyar Afirka da fa\u0257in duniya yadda asalin rayuwar Arewacin Najeriya da Yammacin Afirka take.\u201d <\/p>\n<p>Tashar AREWA24 za ta cigaba da samar da sabbin zango na fitattun wasannin kwaikwayonta da take shiryawa, wato \u201cKwana Casa\u2019in da kuma \u201cDadin Kowa,\u201d sannan tana kan aikin samar da wasu sabbin wasannin kwaikwayo masu dogon zango guda uku da za fito a \u0199arshen shekarar 2024 da kuma cikin shekarar 2025.  Na farko a cikin sabbin wasannin kwaikwayon masu dogon zango shi ne, \u201cJos Chronicles,\u201d wanda aka tsara a yankin jahohin tsakiyar kasarnan a Birnin Jos, kuma za a shi ne da Harsunan Turanci da kuma Hausar Jos. Shirin wasan kwaikwayo ne da ya \u0199unshi barkwanci \u2013 wanda zai mayar da hankali a kan ala\u0199a mai sar\u0199a\u0199iya da ke tsakanin wasu abokai biyar, kuma ana sa rai zai jawo hankalin masu kallo daga yankin jahohin tsakiyar Najeriya. Haka kuma AREWA24 za ta dora wannan wasan kwaikwayo na \u201cJos Chronicles\u201d a kan mahajarta ta kallo kai tsaye domin masu kallo talabijin a fa\u0257in Afirka da kuma duniya baki \u0257aya.<br \/>\nHaka kuma, AREWA24 tana aikin ha\u0257in guiwa da manyan masu shirya fina-finan Hausa na Kannywood da dama domin \u0257ora wasannin kwaikwayonsu masu dogon zango a kan manhajar AREWA24 ON Demand da kuma tashar AREWA24 television network.<\/p>\n<p>GAME DA AREWA24 (https:\/\/arewa24.com\/company-overview\/):  AREWA24 da Bangarenta na samar da shirye-shirye, An fara gabatar da shiryen shiryen AREWA24 a shekarar 2014 domin cike wawakeken gibin da ake da shi a fagen shirye-shiryen nishadi da tsarin rayuwa da ake shiryawa da harshen Hausa masu inganci, wadanda ke nuni da abubuwan da ake alfahari da su a rayuwar Arewacin Najeriya, da al\u2019adu, da kade-kade, da fina-finai, da fasaha, da girke-girke da kuma wasanni. A yau, tashar AREWA24 tana kaiwa ga mutane sama da milyan 40 masu magana da harshen Hausa a Najeriya da kuma Yammacin Afirka a kan tauraron dan dan\u2019adam na Eutelsat da ke kan tsarin kallo kyauta, da kuma kan tauraron dan adam na StarTimes da ke kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba 138), da kafafen tauraron dan\u2019adam na kamfanin Multichoice guda biyu da ke kan tsarin biya kudi, wato DSTV (tasha mai lamba 261) da kuma Gotv (tasha mai lamba 136), da kuma tauraron dan adam na Canal+ a kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba #297) a Jamhuriyar Nijar, da Chadi da kuma Kamaru, AREWA24 na amfana da masu kallo da ke kasancewa da dukkanin shafukanta na yanar gizo a kan AREWA24.com, facebook.com\/AREWA24, da Instagram.com\/AREWA24channel. Haka kuma AREWA24 tana yada shirye-shiryenta a tsarin kallo kai tsaye a ko ina a duniya a kan AREWA24 On Demand tare da hadin guiwar Vimeo.<\/p>\n<p>Domin samun damar kallo kai tsaye a ko ina a duniya a kan AREWA24 ON DEMAND, ku shiga http:\/\/tv.arewa24.com ko ku sauke manhajar daga kan IOS App Store, ko Google Play, ko Apple TV, ko Roku Channel Store da kuma Amazon Fire TV.<br \/>\nDomin karin bayani, sai ku tuntubi: info@arewa24.com            <\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>AREWA24, tashar talabijin da ke kan gaba wajen ya\u0257a shirye-shirye masu nisha\u0257antar da iyali da tsarin rayuwa cikin harshen Hausa, wadda ke da ofishin samar da shirye-shirye a Najeriya da yammacin Afirka, tana sanar da wani gagarumin sabon jadawali na shirye-shirye, da fina-finai da wasannin kwaikwayo da take shiryawa da kuma kar\u0253ar wasannin kwaikwayo na [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":5541,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":"","_links_to":"","_links_to_target":""},"categories":[69],"tags":[132],"class_list":["post-5533","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","tag-news-2"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5533","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5533"}],"version-history":[{"count":3,"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5533\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5582,"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5533\/revisions\/5582"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5541"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5533"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5533"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5533"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}