{"id":5571,"date":"2024-10-14T14:47:58","date_gmt":"2024-10-14T13:47:58","guid":{"rendered":"https:\/\/arewa24.com\/?p=5571"},"modified":"2024-10-14T15:33:06","modified_gmt":"2024-10-14T14:33:06","slug":"gangamin-wayar-da-kai-na-arewa24-a-watan-october-sauya-rayuwa-da-tattauna-%c6%99alubale-game-da-cutar-sikila","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/gangamin-wayar-da-kai-na-arewa24-a-watan-october-sauya-rayuwa-da-tattauna-%c6%99alubale-game-da-cutar-sikila\/","title":{"rendered":"Gangamin Wayar da kai na AREWA24 a watan October: Sauya rayuwa da tattauna \u0199alubale game da cutar Sikila."},"content":{"rendered":"<p>By Musa Abdullahi Sufi<\/p>\n<p>Cutar sikila, matsala ce da ta addabi duniya, da miliyoyin mutane ke fama da ita a fa\u0257in duniya. Kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta bayyana, kimanin yara dubu 300 ake haihuwa da cutar sikila a kowacce shekara, kuma mafi yawa an fi samun masu cutar a yankin Sahara na Afirka.<\/p>\n<p>A Najeriya ka\u0257ai, kimanin yara dubu 150 ake haihuwa da wannan cuta a kowacce shekara, wadda hakan ya sa ta zamo kasar da wannan cuta ta fi addaba a fa\u0257in duniya. Yankin Arewacin Najeriya shi ne ya fi \u0257aukar kaso mafi yawa, da kimanin kaso 20-30 cikin \u0257ari na yawan al\u2019ummar da ke \u0257auke da gadon cutar a jininsu.<\/p>\n<p>Sikila na ci gaba da kasancewa wata matsananciyar matsala a Najeriya, wadda miliyoyin mutane ke fama da ita, musamman a cikin al\u2019ummar da ke magana da Harshen Hausa. Domin da\u0199ile wannan matsala, AREWA24, tashar talabijin ta Hausa da ke kan tauraron \u0257an\u2019adam mafi girma, ta \u0257auki wani gagarumin shirin wayar da kai da kuma ilimantar da \u0257aukacin masu kallonta, ta yin wani gangamin wayar da kai na tsawon wata guda da ta ware domin tattauna batun da ya shafi cutar ta sikila.<\/p>\n<p>A tsawon watan Oktoba, AREWA24 ta mayar da hankali wajen nuna jerin shirye-shirye domin wayar da kai game da cutar sikila. Ba\u0199i na musamman sun ha\u0257a da likitoci, ma\u2019aikatan jinya, \u00a0masu larurar sikila, iyaye, shugabannin addinai, wakilan gwamnati, da kuma kwararru a harkar lafiya da sauransu, wa\u0257anda za su kasance a cikin sanannun shirye-shirye daban-daban domin tattauna ha\u0199i\u0199anin yadda rayuwa da cutar sikita take, da kuma mahimmancin gano cutar da wuri da kulawar da ta dace.<\/p>\n<p>Wannan gangamin wayar da kai, yun\u0199uri ne na kawo sauyi a rayuwa, kasancewar miliyoyin masu magana da harshen Hausa a fadin duniya za su samu ilimi mai mahimmanci bisa yadda za a kaucewa cutar da kuma yadda za a kula da wannan larura da ake gado a cikin jini. Yawan masu fama da cutar a wannan yanki yana da ala\u0199a ne da \u0199arancin kayan aikin kula da lafiya, da \u0199arancin wayar da kai, da kuma \u0199alubalen al\u2019adu, wa\u0257anda suka sa yake da mahimmaci a ya\u0199i wannan cuta ta hanyar wayar da kai, kamar irin wannan Gangamin wayar da kai na AREWA24 a watan Oktoba.<\/p>\n<p>Wannan gangamin wayar da kai, za a yi shi ne domin wayar da kan al\u2019umma, da samar musu bayanai na ceton rai, da fito da yadda za a yi gawaje-gwaje da kuma dabarun da za yi amfani da su da wuri wajen rage tasirin cutar ta sikila a Arewacin Najeriya.<\/p>\n<p>Ilimantar da Miliyoyin al\u2019umma: Gangamin wayar da kai na AREWA24 domin ceton rai, wani aiki ne da zai kawo sauyi a ya\u0199in da ake yi da larurar ta sikila. Yawan al\u2019ummar da wannan tasha ke kaiwa garesu, yana tabbatar da cewa miliyoyin mutane, a Najeriya da ma fadin duniya, za su ilimantu game da mahimmancin da ke akwai game da bu\u0199atar yin gwaji kafin aure. Iyalai da dama da suke fama da larurar sikila ba su da wayewar kai game da mahimmancin gwaji kafin aure domin kaucewa ya\u0257uwar cutar.<\/p>\n<p>Wannan gangamin wayar da kai, zai cike wannan gi\u0253in, ya kuma bawa masu kallo ilimin da zai taimaka musu wajen yanke hukuncin da zai iya ceto \u2018ya\u2019yan da za a haifa\u00a0 a nan gaba daga \u0199alubalen da ke da ala\u0199a da cutar.<\/p>\n<p>Bugu da \u0199ari, shirye-shiryen AREWA24 za su samar da mahimman bayanai a kan yadda za a kula da wa\u0257anda ke fama da cutar ta sikila. Kasancewar kwararru a harkar lafiya cikin shirye-shirye, kamar Gari Ya waye, da Mata A Yau, zai tabbatar da cewa masu kallo sun ilimantu dangane da tallafin da ake bu\u0199ata ta fuskar kiwon lafiya da damuwar masu cutar, domin kyautatwar ingancin rayuwar masu \u0257auke da cutar ta sikila.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kama daga ra\u0257adin da suke fuskanta lokaci bayan lokaci, zuwa fahimtar mahimmancin duba lafiyarsu akai-akai, wa\u0257annan shirye-shirye za su gabatar da shawarwari a aikace wa\u0257anda za su iya kawo tabbataccen sauyi a rayuwar mutane.<\/p>\n<p>Fa\u0257akar da al\u2019ummu ta hanyar shawarar \u0199wararru: Abin da ya sa wannan gangamin wayar da kai ya zamo na musamman shi ne, shigo da ba\u0199i daban-daban cikin wannan shiri. Kama daga likitoci da ma\u2019aikatan jinya da za su dinga bada shawarwari na kiwon lafiya ga masu \u0257auke da cutar ta sikila da kuma iyalansu, suna masu bayyana abubuwan da suka fuskanta.Gangamin zai yi duba a kowanne \u0253angare na ha\u0199i\u0199anin yadda rayuwa da cutar sikila take.<\/p>\n<p>Shugabannin addinai suma suna taka wata mahimmiyar rawa wajen wayar da kai, ta hanyar \u0199arfafa mahimmancin kula da lafiya da kuma alhakin da ke kan al\u2019umma wajen tabbatar da lafiya da kuma jin dadin yaran da za a haifa a nan gaba ta hanyar yin gwaji kafin aure.<\/p>\n<p>Kwararru a harkar lafiya da kuma wakilan gwamnati za su \u0199arawa shirin armashi ta hanyar bayar da \u0199arin haske a kan irin \u0199alubalen da ake da shi wajen shawo kan cutar sikila da kuma haska dokoki da shirye-shiryen da aka yi domin inganta hanyoyin samun kiwon lafiya.<\/p>\n<p>Wannan gangami na wayar da kai bai tsaya iya wayar da kai ba kawai, zai kuma yi wkira domin a samar da tsarin kula da lafiya kyauta ga wadanda cutar ta sikila ta shafa, wanda wani babban mataki ne na magance matsalar tattalin arziki da zamantakewa da wasu majinyatan da dama ke fama da ita wajen neman magani.<\/p>\n<p>Wannan wani mahimmin mataki ne na kawo \u0199arshen ya\u0257uwar cutar sikila: Mahimmancin wayar da kai game da cutar sikila ba zai misaltu ba. A sassan Najeriya, musamman Arewa, har yanzu akwai \u0199arancin fahimtar wannan cuta, wanda ke kaiwa ga ya\u0257uwar bayanai na \u0199arya da nuna \u0199yama.<\/p>\n<p>Iyali da dama ba su san wajabcin neman shawarwari dangane da gadon kwayoyin halitta da kuma gwaji kafin aure ba, wanda hakan zai yi matu\u0199ar rage ya\u0257uwar wannan cuta.<\/p>\n<p>Gangamin wayar da kai na AREWA24 wani mahimmin taimako ne, kasancewar kai tsaye yana cike gibi ta fuskar ilimi da kuma samar da wata farfajiya don tattaunawa ta gaskiya kuma a bayyane game da cutar sikila.<\/p>\n<p>Ta hanyar aiwatar da wannan gangamin ilimantarwa kyauta, AREWA24 tana yiwa al\u2019umma hidima ne. \u0198o\u0199arin tashar game da harkokin kiwon lafiya, musamman a bangarorin da ba a fiya basu mahimmanci ba, yana nuna irin sadaukarwarta wajen sauke nauyin al\u2019umma da kuma kyautata rayuwarsu. Yayin da Jaruman majinyatan da ke fama da cutar sikila da iyalansu ke amfana da wannan gangami, abu ne a zahiri cewa wannan gangami zai yi tasiri sosai a rayuwar milyoyin mutane.<\/p>\n<p>Labarun jaruman da ke fama da cutar sikila, da shawarwarin kwararru daga likitoci, da kuma samun kwarin guiwa daga shugabannin addninai, duk za su hadu su samar da wani gagarumin sa\u0199o da zai ceto rayuka.<\/p>\n<p>\u0198ari a kan wayar da kai, wannan gangami zai kuma zaburar da al\u2019umma domin \u0257aukar mataki. Ba\u0199in, za su tattauna game da shirye-shiryen da suke gudana a yanzu haka, wa\u0257anda aka tsara su\u00a0 domin samar da tsarin kula da lafiya kyauta ga majinyata masu larurar sikila, wanda zai ci gaba da \u0199arfafar rawar da AREWA24 ta taka a matsayin wadda ta kawo sauyi mai amfani. Wannan shiri yana nufin ceto rayuka, da kyautata rayuwa ga jaruman da ke fama da cutar ta sikila, da kuma kare yaran da za a haifa a nan gaba daga fukantar irin wannan \u0199alubale.<\/p>\n<p>Rufewa: Wani shiri gangami wayar da kai a watan Oktoba na AREWA24 domin Jarumai masu larurar sikila, wani gagarumin aiki ne a ya\u0199in da ake yi da cutar sikila. Ta hanyar hada kwararru a harkar lafiya, da shugabannin al\u2019umma, da kuma iyalan da abin da ya shafa, ba iya wayar da kai ka\u0257ai tashar ke yi ba, bar ma da sauya rayuwar al\u2019umma.<\/p>\n<p>Jaruman da ke fama da cutar ta sikila da kuma iyalansu suna matu\u0199ar godiya da wannan shiri, wanda zai basu fata, ya kuma \u0199arfafesu ta inda aka fi bu\u0199atar hakan.<\/p>\n<p>Wannan gangamin wayar da kai na tsawon wata guda, wata shaida ce da ke nuna jajircewar da AREWA24 ke yi wajen amfani da tashar don yin abin alkhairi. Kada masu kallo su bari wannan dama ta musamman ta koyon ilimi, da tattaunawa, da kuma \u0257aukar mataki a kan ya\u0199i da cutar sikila ta wuce su. Ta hanyar ilimantarwa da wayar da kai, duk za mu iya bayar da gudunmawa wajen ceto rayuka da kuma gina al\u2019umma mai cike da \u0199oshin lafiya.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>By Musa Abdullahi Sufi Cutar sikila, matsala ce da ta addabi duniya, da miliyoyin mutane ke fama da ita a fa\u0257in duniya. Kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta bayyana, kimanin yara dubu 300 ake haihuwa da cutar sikila a kowacce shekara, kuma mafi yawa an fi samun masu cutar a yankin Sahara na Afirka. [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":5565,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":"","_links_to":"","_links_to_target":""},"categories":[69],"tags":[132],"class_list":["post-5571","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","tag-news-2"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5571","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5571"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5571\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5573,"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5571\/revisions\/5573"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5565"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5571"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5571"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5571"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}