{"id":5583,"date":"2024-10-15T09:09:26","date_gmt":"2024-10-15T08:09:26","guid":{"rendered":"https:\/\/arewa24.com\/?p=5583"},"modified":"2024-10-15T14:27:23","modified_gmt":"2024-10-15T13:27:23","slug":"arewa24-za-ta-fa%c9%97a%c9%97a-adadin-%c6%99asashen-da-take-ya%c9%97a-shirye-shiryenta-tare-da-canal-za-ta-fa%c9%97a%c9%97a-zuwa-%c6%99arin-%c6%99asashen-yammacin-afirka-hu%c9%97u-benin-republic-bur","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/arewa24-za-ta-fa%c9%97a%c9%97a-adadin-%c6%99asashen-da-take-ya%c9%97a-shirye-shiryenta-tare-da-canal-za-ta-fa%c9%97a%c9%97a-zuwa-%c6%99arin-%c6%99asashen-yammacin-afirka-hu%c9%97u-benin-republic-bur\/","title":{"rendered":"AREWA24 ZA TA FA\u018aA\u018aA ADADIN \u0198ASASHEN DA TAKE YA\u018aA SHIRYE-SHIRYENTA TARE DA CANAL+, ZA TA FA\u018aA\u018aA ZUWA \u0198ARIN \u0198ASASHEN YAMMACIN AFIRKA HU\u018aU: BENIN REPUBLIC, BURKINA FASO, MALI AND TOGO"},"content":{"rendered":"<p><strong>15 ga Oktoba, 2024<\/strong> \u2013 AREWA24, tashar talabijin da ke kan gaba wajen yada shirye-shirye da harshen Hausa, masu nishadantar da iyali da nuna tsarin rayuwa, wadda ke da ofishin daukar shirye-shiryenta a Yammacin Afirka, tare da hadin guiwar CANAL+ International, tana mai farin cikin sanar da gagarumin aikin fa\u0257a\u0257a ya\u0257a shirye-shiryenta zuwa \u0199arin kasashe hu\u0257u: <strong>Benin Republic, Burkina Faso, Mali da Togo,<\/strong> a kan <strong>CANAL+ tasha mai lamba CH 297<\/strong>, wanda hakan zai \u0199aru zuwa kasashen ta\u0199was (8) a Yammacin Afirka da ake kallon AREWA24, wa\u0257anda suka ha\u0257ar da Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi.<\/p>\n<p>Wannan mahimmin aikin fa\u0257a\u0257awa, yana nuna mahimmanci da tasirin ala\u0199ar da ke tsakanin CANAL+ International da AREWA24 ke da shi, bisa \u2018yancin samun bayanai da shirye-shiryen nisha\u0257i masu inganci a fa\u0257in nahiyar Afirka. Wannan cigaba zai bawa AREWA24 wata dama ta musamman wajen samar da ingantattun shirye-shirye ga sabbin miliyoyin masu kallonta a fa\u0257in Jamhuriyar Benin, Burkina Faso, Mali da Togo. Da wannan aiki na fa\u0257a\u0257awa domin kaiwa ga \u0199arin masu kallon Talabijin, AREWA24 za ta ci gaba da \u0199o\u0199arinta wajen nuna al\u2019adu na alfahari, na masu magana da Harshen Hausa a fadin duniya, ta hanyar nuna shirye-shirye masu inganci da ke fa\u0257akarwa, nisha\u0257antarwa da kuma zaburarwa.<\/p>\n<p>\u201cMuna farin cikin ganin shirye-shiryenmu sun kai ga sabbin miliyoyin masu kallo a Jamhuriyar Benin, Burkina Faso, Mali da Togo, tare da ha\u0257in guiwar CANAL+ International\u201d a ta bakin Celestine Umeibe, Mataimakin Shugaban AREWA24 kuma Babban Shugaban Sashen tallace-tallace da kasuwanci. Wannan wata gagarumar nasara ce ga \u0199o\u0199arin da AREWA24 ke yi na kasancewa kafar ya\u0257a shirye-shirye da ke kan gaba a Nahiyar Afirka. Wannan zai sa mu ci gaba da yin \u0199arfi a mataki na duniya, da ha\u0257a kan harsuna da al\u2019adu a fa\u0257in Yammacin Afirka, a lokaci guda kuma muna bu\u0257e mahimman damarmaki ga masu tallace-tallace da kamfanoni domin kaiwa ga masu kallo a gagarumar kasuwar Yammacin Afirka.\u201d<\/p>\n<p>Jadawalin AREWA24 da ya \u0199unshi shirye-shirye daban-daban, kamar wasannin kwaikwayo masu dogon zango; wato Dadin Kowa, Kwana Casa\u2019in da Gidan Badamasi, da sannanen shirin na matasa, wato Arewa Gen-Z, da shirin mata, wato Mata A Yau, da shirinta da ke zuwa kowacce rana wato shirin Gari Ya Waye, da \u0199o\u0199arin da take na ci gaba da samar da shirye-shirye masu inganci a mataki na duniya, da kuma samar da shirye-shirye na cikin gida da ke abubuwan al\u2019ada na alfahari, sun sa ta zamo amintacciyar hanyar nisha\u0257antar da iyali da harshen Hausa.<\/p>\n<p><strong>GAME DA AREWA24 (<\/strong><a href=\"https:\/\/arewa24.com\/company-overview\/\">https:\/\/arewa24.com\/company-overview\/<\/a>)<strong>:<\/strong>\u00a0 AREWA24 da Bangarenta na samar da shirye-shirye, An fara gabatar da shiryen shiryen AREWA24 a shekarar 2014 domin cike wawakeken gibin da ake da shi a fagen shirye-shiryen nishadi da tsarin rayuwa da ake shiryawa da harshen Hausa masu inganci, wadanda ke nuni da abubuwan da ake alfahari da su a rayuwar Arewacin Najeriya, da al\u2019adu, da kade-kade, da fina-finai, da fasaha, da girke-girke da kuma wasanni. A yau, tashar AREWA24 tana kaiwa ga mutane sama da milyan 40 masu magana da harshen Hausa a Najeriya da kuma Yammacin Afirka a kan tauraron dan dan\u2019adam na Eutelsat da ke kan tsarin kallo kyauta, da kuma kan tauraron dan adam na StarTimes da ke kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba 138), da kafafen tauraron dan\u2019adam na kamfanin Multichoice guda biyu da ke kan tsarin biya kudi, wato DSTV (tasha mai lamba 261) da kuma Gotv (tasha mai lamba 136), da kuma tauraron dan adam na Canal+ a kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba #297) a Jamhuriyar Nijar, da Chadi da kuma Kamaru, AREWA24 na amfana da masu kallo da ke kasancewa da dukkanin shafukanta na yanar gizo a kan <a href=\"http:\/\/arewa24.com\/\">AREWA24.com<\/a>, <a href=\"http:\/\/facebook.com\/arewa24\">facebook.com\/AREWA24<\/a>, da <a href=\"http:\/\/www.Instagram.com\/AREWA24channel\">Instagram.com\/AREWA24channel<\/a>. Haka kuma AREWA24 tana yada shirye-shiryenta a tsarin kallo kai tsaye a ko ina a duniya a kan AREWA24 On Demand tare da hadin guiwar Vimeo.<\/p>\n<p><em>Domin samun damar kallo kai tsaye a ko ina a duniya a kan AREWA24 ON DEMAND, ku shiga <\/em><a href=\"http:\/\/tv.arewa24.com\/\">http:\/\/tv.arewa24.com<\/a><em> ko ku sauke manhajar daga kan IOS App Store, ko Google Play, ko Apple TV, ko Roku Channel Store da kuma Amazon Fire TV.<\/em><\/p>\n<p>Domin karin bayani, sai ku tuntubi: <a href=\"mailto:info@arewa24.com\">info@arewa24.com<\/a><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>15 ga Oktoba, 2024 \u2013 AREWA24, tashar talabijin da ke kan gaba wajen yada shirye-shirye da harshen Hausa, masu nishadantar da iyali da nuna tsarin rayuwa, wadda ke da ofishin daukar shirye-shiryenta a Yammacin Afirka, tare da hadin guiwar CANAL+ International, tana mai farin cikin sanar da gagarumin aikin fa\u0257a\u0257a ya\u0257a shirye-shiryenta zuwa \u0199arin kasashe [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":5589,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":"","_links_to":"","_links_to_target":""},"categories":[69],"tags":[132],"class_list":["post-5583","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","tag-news-2"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5583","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5583"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5583\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5588,"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5583\/revisions\/5588"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5589"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5583"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5583"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5583"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}