{"id":5606,"date":"2025-04-15T16:16:44","date_gmt":"2025-04-15T15:16:44","guid":{"rendered":"https:\/\/arewa24.com\/?p=5606"},"modified":"2025-04-15T17:13:17","modified_gmt":"2025-04-15T16:13:17","slug":"arewa24-ta-samu-sabon-shugaba-da-zai-jagoranci-tashar-wasu-shekaru-goma-da-za-su-zo-da-cigaba-da-kuma-sabbin-abubuwa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/arewa24-ta-samu-sabon-shugaba-da-zai-jagoranci-tashar-wasu-shekaru-goma-da-za-su-zo-da-cigaba-da-kuma-sabbin-abubuwa\/","title":{"rendered":"AREWA24 ta samu sabon Shugaba da zai jagoranci tashar wasu Shekaru Goma da za su zo da cigaba da kuma sabbin abubuwa"},"content":{"rendered":"<p><img fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" class=\"alignnone wp-image-5613 size-large\" src=\"https:\/\/arewa24.com\/wp-content\/uploads\/2025\/04\/PRESS-RELEASE-1024x576.jpg\" alt=\"\" width=\"1024\" height=\"576\" srcset=\"https:\/\/arewa24.com\/wp-content\/uploads\/2025\/04\/PRESS-RELEASE-1024x576.jpg 1024w, https:\/\/arewa24.com\/wp-content\/uploads\/2025\/04\/PRESS-RELEASE-300x169.jpg 300w, https:\/\/arewa24.com\/wp-content\/uploads\/2025\/04\/PRESS-RELEASE-768x432.jpg 768w, https:\/\/arewa24.com\/wp-content\/uploads\/2025\/04\/PRESS-RELEASE-1536x864.jpg 1536w, https:\/\/arewa24.com\/wp-content\/uploads\/2025\/04\/PRESS-RELEASE-800x450.jpg 800w, https:\/\/arewa24.com\/wp-content\/uploads\/2025\/04\/PRESS-RELEASE.jpg 1920w\" sizes=\"(max-width: 1024px) 100vw, 1024px\" \/><\/p>\n<p><strong>15 ga Afrilu 2025.<\/strong>\u00a0 <strong>FOR IMMEDIATE RELEASE\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0 <\/strong><\/p>\n<p>AREWA24, tashar talabijin da ke kan gaba wajen ya\u0257a shirye-shirye masu nisha\u0257antar da iyali da da tsarin rayuwa cikin Harshen Hausa tsawon sa\u2019o\u2019i 24 a dukkanin ranakun mako, tana sanar da gagarumin sauyin shugabanci da ta samu a karon farko tsawon shekaru goma. Celestine Umeibe, wanda a halin yanzu yake matsayin mataimakin Shugaban AREWA24 (AREWA24\u2019s Deputy CEO and Chief Commercial Officer), shi ne zai kar\u0253i mu\u0199amin Babban Shugaba wato Chief Executive Officer, inda zai gaji Jacob Arback, wanda shi kuma zai koma sabon mu\u0199amin Executive Vice Chairman, wato Babban Mataimakin Shugaban Gudanarwa. Mr. Umeibe zai ci gaba da kula da dukkanin harkokin tallace-tallace da kasuwanci na kamfanin.<\/p>\n<p>A cewar Celestine Umeibe: \u201cJacob Arback ya taka mahimmiyar rawa a gagarumar nasarar da AREWA24 ta samu tsawon shekaru goma da suka wuce. Salon shugabancinsa na musamman da bawa kowa dama domin bada gudunmawarsa ya bawa AREWA24 dama wajen tsallake duk wasu matsaloli na kasuwance da kuma \u0199alubalen da kan addabi sabbin harkokin kasuwanci, musamman a wannan yanki. Karin matsayi da Mr. Arback ya samu zuwa Babban Mataimakin Shugaban Gudanarwa abu ne da ya cancanta, kuma babu ko shakka zai ci gaba da kawo cigaba a cikin kasuwancin wannan kamfani.<\/p>\n<p>Shugaban mai barin gado, Jacob Arback, ya yi aiki tare da Mr. Umeibe a AREWA24 tun daga lokacin da aka kafa tashar a shekarar 2014. \u201cBabu wani wanda ya fi cancanta da dacewa ya jagoranci AREWA24 cikin shekaru goma masu zuwa da za su zo da cigaba da kuma alfanu sama da Celestine,\u201d a cewar Arback. \u201cBaiwar da yake da ita ta shugabanci, kasuwanci da gogewa kan abubuwan da aka san kamfani a kai, da kuma zurfin ilimi game da bangaren kafafen ya\u0257a labarar da samar da shirye-shirye masu nisha\u0257antarwa sun sa Celestine ya zamo wani za\u0253i mai sau\u0199i ga Daraktocin Gudanarwarmu. Ina matu\u0199ar \u0257okin ganin yadda shekaru goma masu zuwa cike da \u0199ir\u0199ira, da sabbin abubuwa da kuma bun\u0199asa da ci gaba za su kasance \u0199ar\u0199ashin jagorancinsa. Tun daga farkon kafa AREWA24, Celestine ya nuna jajircewa bisa \u201cDalilin\u201d kafa tashar AREWA24 &#8211; &#8211; \u2018don nunawa da kuma alfahari da al\u2019adun gargajiya kuma cikin Harshen Hausa.\u2019<\/p>\n<p>Aiki da Mr. Umeibe sama da shekaru 10+ a \u00a0AREWA24, gami da matsayinsa na baya na shugaban sashen tallace-tallace, da kasuwanci, da matsayinsa na kasuwanci da ya ri\u0199e a StarTimes da kuma TVC, ya kawo gagarumar gogewa ta kawo sauyin da AREWA24 ta kawo a tsakanin tashoshin talabijin da kafafen ya\u0257a labarai, tare da hangen nesa game da makomar kamfanin. Mr. Umeibe zai yi aiki wajen yin amfani da basira wajen yanke hukunci kan shirye-shirye, da amfani da cigaban fasahohin zamani da kuma samar da sabbin hanyoyin samun ku\u0257a\u0257en shiga domin ciyar da manufar AREWA24 gaba ta zamowa \u0257aya daga cikin manyan tashoshin talabijin na Afirka, da samar da shirye-shirye, da kuma kamfanonin ya\u0257a labarai na nahiyar.<\/p>\n<p><a href=\"http:\/\/(https\/arewa24.com\/company-overview\/\"><strong>GAME DA AREWA24<\/strong><\/a>:\u00a0 AREWA24 da Bangarenta na samar da shirye-shirye, An fara gabatar da shiryen shiryen AREWA24 a shekarar 2014 domin cike wawakeken gibin da ake da shi a fagen shirye-shiryen nishadi da tsarin rayuwa da ake shiryawa da harshen Hausa masu inganci, wadanda ke nuni da abubuwan da ake alfahari da su a rayuwar Arewacin Najeriya, da al\u2019adu, da kade-kade, da fina-finai, da fasaha, da girke-girke da kuma wasanni. A yau, tashar AREWA24 tana kaiwa ga mutane sama da milyan 40 masu magana da harshen Hausa a Najeriya da kuma Yammacin Afirka a kan tauraron dan dan\u2019adam na Eutelsat da ke kan tsarin kallo kyauta, da kuma kan tauraron dan adam na StarTimes da ke kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba 138), da kafafen tauraron dan\u2019adam na kamfanin Multichoice guda biyu da ke kan tsarin biya kudi, wato DSTV (tasha mai lamba 261) da kuma Gotv (tasha mai lamba 136), da kuma tauraron dan adam na Canal+ a kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba #297) a Jamhuriyar Benin, da Burkina Faso, da Cameroon, da Chad, da Mali, da Nijar, da kuma\u00a0 Togo Nijar, AREWA24 na amfana da masu kallo da ke kasancewa da dukkanin shafukanta na yanar gizo a kan <a href=\"http:\/\/www.arewa24.com\/\">www.AREWA24.COM<\/a>,\u00a0<a href=\"https:\/\/www.facebook.com\/AREWA24\">www.facebook.com\/AREWA24<\/a>,da\u00a0<a href=\"https:\/\/www.instagram.com\/AREWA24channel\">Instagram.com\/AREWA24channel<\/a>.\u00a0 Haka kuma AREWA24 tana yada shirye-shiryenta a tsarin kallo kai tsaye a ko ina a duniya a kan AREWA24 On Demand tare da hadin guiwar Vimeo. <em>Domin samun damar kallo kai tsaye a ko ina a duniya a kan AREWA24 ON DEMAND, ku shiga <\/em><a href=\"http:\/\/tv.arewa24.com\/\">http:\/\/tv.arewa24.com<\/a><em> ko ku sauke manhajar daga kan IOS App Store, ko Google Play, ko Apple TV, ko Roku Channel Store da kuma Amazon Fire TV.<\/em><\/p>\n<p>Domin karin bayani, sai ku tuntubi: <a href=\"mailto:info@arewa24.com\">info@arewa24.com<\/a><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>15 ga Afrilu 2025.\u00a0 FOR IMMEDIATE RELEASE\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0 AREWA24, tashar talabijin da ke kan gaba wajen ya\u0257a shirye-shirye masu nisha\u0257antar da iyali da da tsarin rayuwa cikin Harshen Hausa tsawon sa\u2019o\u2019i 24 a dukkanin ranakun mako, tana sanar da gagarumin sauyin shugabanci da ta samu a karon farko tsawon shekaru goma. Celestine Umeibe, wanda a halin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":5613,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":"","_links_to":"","_links_to_target":""},"categories":[69],"tags":[132],"class_list":["post-5606","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","tag-news-2"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5606","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5606"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5606\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5618,"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5606\/revisions\/5618"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5613"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5606"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5606"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/arewa24.com\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5606"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}