LABARU 2018-01-17T10:53:38+01:00

Sakon Jawabin AREWA 24

AREWA24 Ta Bayyana A Dikodar StarTimes   

16 ga Janairu, 2018  -Kamfanin Startimes da ke yada tashoshin talabijin na tauraron dan Adam, ya sanar da sanya fitacciyar tashar nan ta harshen Hausa wato Arewa24 cikin jerin tashoshin da ke kan dikodarsu, a wani yunkuri da tashar ke yi na ganin ta biya bukatun dinbun mutanen da ke kallonta. A ta bakin Daraktan kasuwanci na tashar, Qasim Elegbede ya bayyana cewa “bukatar samar da karin tashoshin talabijin na harshen Hausa ta ci gaba da hauhawa a tsakanin masu kallo . …..

AREWA24 Ta Bijiro Da Jerin Shirye-Shiryenta A Watan Azumin Ramadan Na Shekarar 2017  

Afrilu 18, 2017  – AREWA24 ta sanar jerin shirye-shiryenta a watan Ramadan na shekarar 2017. Tashar Arewa24 ita ce tashar tauraron dan adam ta yan arewa ta farko dake yada shirye-shiryenta cikin harshen hausa na tsawon sa‟o‟i 24 a dukkanin ranakun mako, wadanda „yan Arewa ke shiryawa domin „yan Arewacin Najeriya da kuma masu magana da harshen Hausa dake Nageriya da kasahen dake Makotaka da ita. …..

‘Girl Rising’ da tashar AREWA24 na sanar da fara nuna shirinsu na Da Bazar mu…, 

Fabarairu,  13, 2017  – Wani sabon shiri da yake da kasha shida wanda zai zagaya da masu kallo sassanduni sannan ya sake dawo wa zuwa yankin arewacin Najeriya don shaida irin jajircewar da dan adam ke da ita da kuma tasirin da ilimi ke da shi wajen kawo sauyi duniya. …..

AREWA24 Ta Kaddamar Da Sabon Sashen Wasanni Mai Taken “A24 Sports”

February 7, 2017:  – Daga ranar 7 ga watan Fabrairu, 2017 kamfanin yada labarai na tashar gidan talabijin na AREWA24, mai yada shirye-shiryenta a harshen Hausa a kan tauraron Dan-Adam awa 24 na sanar da kaddamar da sabon sashen shiryeshirye, “A24 Sports.”…

AREWA24 Za Ta Hau DStv Da GOtv A Oktoba

Lagos, Nigeria; 17 October 2016:  – MultiChoice Nigeria zata dora AREWA24, a rukunin tashoshinta domin fadada samar da tashoshi na kyauta (FTA) akan DStv da GOtv. Muna gabatar da tashar farko ta tauraron Dan-Adam mai yada shirye-shiryenta awa 24 a harshen Hausa kyauta ranar 20 October akan DStv channel 261 da kuma GOtv channel 101…

AREWA24 TARE DA CHOCOLATE CITY NA YIN SHIRI NA MUSAMMAN KAN FITATTUN MAWAKAN AREWACIN NAJERIYA

Agusta 23, 2016  – Chocolate City Group, mafi girman kamfanin da ke yada nishadantarwa a Afirka, tare dagidan talabijin na AREWA24, mai yada shirye-shiryensa24/7a harshen Hausa da ke Arewacin Najeriya, na sanar da gagarumar hadin gwiwar talabijin ta “Nunin Mawaka.” Nunin Mawaka, wani sabon shiri ne da zai gabatar da wani sabon yanayi na taba ka lashe da zai yi nuni akan fasihai, kuma fitattun mawaka daga Arewacin Najeriya.Kowane gajeren taba ka lashe zai bibiyi harkar wake-waken daya daga cikin mawakan Chocolate City daga kuruciya zuwa matsayin da yake a yanzu kallonmu…

AREWA24  Na Murnar Cikarta Shekaru Biyu Tana Watsa Shirye-Shirye A Arewacin Najeriya

Yuni,  28, 2016  – AREWA24, Kamfanin Tashar da ke yada kayatattun shirye-shirye masu nishadantarwa a ko da yaushe, na murnar cika shekara biyu ranar 28 ga watan Yuni. Tun da aka kaddamar da ita a ranar farko ta watan Ramadan, 2014, AREWA24 ta tsaya da kafarta wajen zama tasha ta farko da ke samar da shirye-shiryen Hausa don Arewacin Najeriya. AREWA24 na shiryawa da kuma yada shirye-shirye daban-daban da suka dace da Hausawa a ko wane fanni ga masu amfani da harshen Hausa a duk fadin Arewacin Najeriya da kuma kasashen da suka makwabce ta…..

AREWA24 Ta Kaddamar Da Sabon App Na Hausa A Androud Da iOS

March 17, 2016  – AREWA24, gidan talabijin da ke kan tauraron Dan-Adam na farko a Hausa mai yada shirye-shirye awa ashirin da hudu kyauta da ‘yan Arewacin Najeriya su ke yi don Arewacin Najeriya, ta samu nasanar kaddamar da App dinta na wayar hannu da za a iya samu a Google Play Store da kuma Apple App Store. ….

NTA Tare Da AREWA24 Za Su Fara Hadin Gwiwa Kan Shirye-Shiryensu

April 12, 2016  –  Hukumar Talabijin ta Najeriya (NTA) da AREWA24, tashar tauraron Dan-Adam da take yada shirye-shiryenta  masu nishadantaarwa da kayatarwa a harshen Hausa, na sanar da hadin gwiwar yada shirye-shirye da ya hada da daukacin tashoshin NTA 17 da suke watsa shirye-shiryensu a Arewacin Najeriya…..

Shirin Dadin Kowa Ya Ci Kyauta

March 5, 2016  – Shirin wasan kwakwaiyo na Dadin Kowa shi ya lashe gasar fina-finai da wasannin kwaikwayo na talbijin da aka yi da Hausa na shekarar 2016. Dadin Kowa wasan kwakwayo na talbijin ya doke fim din Sarki Jatau da Sakaina da Baya da kura da kuma In ji ‘yan caca….

screen africaTashar Arewa24 Za Ta Fitar Da Jerin Sababbin Shirye-Shiryenta Masu Kayatarwa Na Shekarar 2016

January 19, 2016  – Domin samun ci gaba a kan bunkasa da kuma farin jinin ga tashar, tashar za ta kaddamar da jerin sababbin shirye-shirye masu nishadantarwa a shekarar 2016. Tun farkon kafa tashar Arewa24 a watan Yunin shekarar 2014, shirye-shiryen harshen Hausa masu kayatarwa wadanda suke haska al’adun gargajiya, sun kasance ginshikinta. Tashar ta samu nasara wajen kaddamar da wasan kwaikwayonta na farko wato “Dadin Kowa” a watan Fabrairu na shekarar 2015…

AREWA24 TANA BIKIN CIKAR SHEKARA GUDA DON SAMUN NASARARTA WAJEN YADA SHIYE-SHIRYE A HARSHEN HAUSA

July 7, 2015Wannan watanne ake bikin cikar shekara guda na AREWA 24, tashar talabijin ta farko da ke yada shirye-shiryenta a harshen Hausa ta Tauraron Dan-Adam don masu magana cikin yaren Hausa a Najeriya da makwabtan kasashe. Tun farkon kaddamar da ita, AREWA 24 ta zama gagarabadau a matsayin tashar da tafi kowacce yada nagartattun shirye-shiryen talabijin a cikin harshen Hausa, yaren Afirka ta Yamma da fiye da mutane miliyan hamsin suke magana da shi a duniya. AREWA 24 zata yi wannan biki ne ta hanyar amfani da shirye-shiryenta da suka fi farin jini, wadanda za su hada da shiri na musamman ta kafofin dandalin sada zumunta da kuma tattaunawa da masu kallonmu…


AREWA24 a labarai

July 8, 2015. NexTV: “ACTV adds AREWA24 to its Channel Bouquet” by Malini Nagaraj (Screen Capture)

leadership-logo320x75July 8, 2015. Leadership: “Arewa 24; Tashar Hausa Ta Farko A Nigeria Mai Yada Shirye-shiryenta 24 Ta Sauka Cikin Rukunin ACTV” by Samuel Abulude. (Screen Capture)

Tashar talabijin ta farko kuma tilo ta tauraron Dan-Adam, ta ‘yan kasa mai yada shirye-shiryenta a harshen Hausa, Arewa 24 ta shiga rukunin tashoshin African Cable Television.Tashar talabijin ta Arewa 24 me nuna tsarin rayuwa da nishadantarwa ta karkata wajen samarwa da nuna tsantsar shirye-shirye masu nagarta cikin harshen Hausa da kuma tallata kyawawan abubuwa, bada gudunmawa da fikirorin Arewacin Najeriya ta watsa su zuwa kasashen Afirka, Gabas ta Tsakiya da ma duniya baki daya. An tsara Arewa 24 don ta maida hankali ga al’adun matasa, Arewacin Najeriya, cinikayya, al’ada, fasahohi da nishadantarwar iyali da za’a iya bayyana su ta hanyar tattaunawa, shirin hira a duk mako, hatsin bara, wasan kwaikwayo da kade-kade.

February 2015. screen africaScreen Africa: “First ever homegrown Hausa-language channel now on air” by Warren Holden


Taskar Labaru


TUNTUBE MU a info@arewa24.com