Dadin Kowa

Dadin Kowa 2017-12-01T22:43:58+01:00

Project Description

Bayanai

Lokacin wannan shirin:
Asabar

Shirin:
Arewa 24

DADIN KOWA

Wasan kwaikwayo na asali mai farin jini da Arewa24 ta shirya, wanda ya lashe lambar yabo, inda ya kawo labarin Dadin Kowa, wani kirkirarren gari wanda jaruman cikinsa suke nuni da irin rayuwar al’ummar dake arewacin Najeriya ta zahiri. Da irin wannan labaran ne masu kallo suke ganin kansu a wannan matsayi da irin burikansu da kalubalensu da kuma kwatanta irin dabi’un su wajen fadi tashinsu wajen yanke shawara game da sana’arsu da iyalansu da kudadensu ko kuma rikici. Dadin Kowa shine ya cinye gasar Afirka Magic na 2016.

Ku sadu da ‘Yan wasan Dadin Kowa:

Nazir2Mawaki. Mai burin zama mawakin zamani, wanda himmarsa take birge abokansa amma kuma iyayensa suke kyamatar wannan himmar. Duk da ya tashi a cikin yayunsa mata guda biyar, Nazir yana zama a firgice idan ya tsinci kansa a tsakanin mata – musamman wacce yake da shauki a kanta Zainab.
Badaru2Yaron banza. Dan ta’adda kuma dan daba, babu wani abu da yake iya girgiza shi, sai kyawawan mata! Ya taso a hannun mafadacin ubansa da kuma kishiyar uwa da ta tsane shi, Badaru ya samu mafaka a miyagun kwayoyi da ta’addanci, sannan akwai cikakkiyar fahimtar juna tsakanisa da abokansa ‘yan daba.
Alawiyya2Mai yawan buri. ‘Yar aikin gida wacce bata gama makarantar firamare ba, Alawiyya tana da kaunar littattafai da kuma burin taimakawa iyalinta don tabbatar da cewa ‘yar uwarta tayi karatun da ita bata samu ba…amma matsolanci irin na mahaifinta yana taka mata birki.
Zuby‘Yar duniya. Zuby wacce take da matukar sha’awar kyale-kyale, tasan dabarun samun kudi ta ko wane hali. Kuma mutuniyar kirki ce abar kauna, amma kishiyoyin uwarta basu amince da yanayin dabi’unta ba, sannan suna ganin saurayinta Goje a Dan-ta’adda kuma suna tsoron watakila Zuby tana aikata wani abin kunya a boye.
Sallau2Shasha ne. Bakauye, Sallau mutumin gargajiya ne kazami wanda yake sana’ar duk wani kayan marmari da ake yayi. Sallau mai faran-faran ne kuma mai kaunar jama’a, duk da dai wani lokacin taimakonsa yana komawa matsala! Amma shashashan ne shi kamar yadda ake gani?
DantaniMakoci nagari. Mai shayi, Dantani masani ne akan dukkan abubuwan da suke faruwa a Dadin Kowa, amma wace irin soyayya wadanda suke tare da shi suke yi masa? Duk da yana ikirarin cewa yazo ne daga wani kauye na kusa da na su Sallau, yakensa na nuni da wata mummunar rayuwa da yayi a wata kasar a baya.
Mal KabiruMatsolon makaho. Mahaifin Alawiyya, Kande da Aminu, Makaho ne kuma almajiri, babbar matsalarsa ita ce yayi asarar kudi – mafi muni kuma ita ce ya kashe kudi! Babban burinsa kuma shine yaje aikin haji. Ko zai iya ware wasu daga cikin kudinsa ya taimaki iyalinsa ko kuma matarsa da bata da lafiya?
GojeDan-daba. Maraya wanda ya girma a titi mai yawan son caca, Goje ba abinda ya amincewa sai burin da yasa a gaba. Aiki tare da dan siyasa mara imani yasa ya dandana giyar mulki, Makiyansa suna masa kallon mara imani, kuma abokansa suna sha’awar yanayinsa, amma dai kowa ya aminta da cewa sabo da shi jari ne.
TimoWanzami. Mai kirki kuma mai hakuri, Timo yana da farin jini a wajen kowa amma kullum a tsorace yake don kada abokansa su gano shi kuma su tsangwame shi a matsayinsa na kirista, da kuma kyamatar da zai fuskanta daga iyayensa saboda son musulma da kuma tsangwama daga al’uma saboda wani abu da ya faru a baya.
Aminu AKDan tawaye. Ana yaba masa wajen iya sarrafa kayan wuta, Aminu shine mafi kankanta a yaran Badaru kuma yana biye da shi ko ina koda kuwa cikin matsala ne! Ya tsani yawan mitar yayarsa Alawiyya, amma yana son bawa kanwarsa Kande kariya, duk da dai cewa wani lokacin yana tunanin komawa Libya ya rabu da su gaba daya…
ZainabMarubuciya. Mahaifinata ma’aikacin gwamnati ne, mahaifiyarta kuma malamar jinya, Zainab lokuta da dama ita kadai ake bari a gida tare da Dan-haya kirista, wanda suke abota tare- amma abin a iya abota ya tsaya kuwa?
KamalDan rawa. Dan gudun makarantar allo wanda bashi da ilimin boko, Kamal kullum a cikin matsala yake da babansa kuma malaminsa saboda yawan son kade-kade da raye-raye a maimakon karatun kur’ani. Mahaifin Kamal ya hana shi cudanya da wadanda ba musulmi ba, amma Kamal zai iya watsar da ra’ayinsa yabi abinda mahaifinsa yake so?
stella2Muguwar Uwargida: Kirista ce mai rufin asiri, Stella bata yarda da musulmai ba – musamman ma ‘yar aikinta Alawiyya, wacce take samun kulawa ta musamman daga mijinta Olabode. Amma irin kallon juna dake tsakanin Stella da Patrick yana nuna cewa ba Olabode ne kadai yake da jinkai ba.
OlabodeMai kaunar zaman lafiya. Duk da cewa shi kirista ne kullum yana cikin raha da makotansa musulmi, koda yake matarsa Stella ta damu da yawan sakin fuskar da yake yiwa ‘yar aikinsa Alawiyya.

Ku Kalli Dadin Kowa a AREWA24.com KAFIN a saka a AREWA24!

A danna nan domin kallon Shirye-Shiryen mu da dama a ATASHAR YOUTUBE.