Daga Masu Kallon Mu

Daga Masu Kallon Mu 2017-12-02T00:16:52+01:00

Project Description

Bayanai

Lokacin wannan shirin:
Juma’a

Shirin:
Arewa 24

Bayani kan shirye-shiryen mu

Wannan kayataccen shirin zai bawa masu kallo damar samun amsoshin tambayoyin da suke aikowa game kayatattun shirye-shirye da Tashar Arewa24 ke gabatarwa, har ila yau, su ga yadda Tashar ke gabatar da shirye-shiryen ta, za’a tattaro tambayoyin da masu kallo suka aiko ta e-mel din Arewa24 da sashin sada zumunta na ‘Facebook’ da na ‘Twitter’ da kuma na ‘YouTube’ a mika su kai tsaye ga Ma’aikaci ko sashen da tambayar ta shafa. Wannan shiri, zai zama wata dama da masu kallo za su ga shiri na bayan fage na yadda Tashar Arewa24 ke gabatar da kayatattun shirye-shiryenta su kuma sadu da masu shiryawa da masu gabatarwa don ganin yadda ake gabatar da wadannan shirye-shirye.

Kuna da tambaya ko bayani akan AREWA24? Ku turo ta Facebook ko Twitter domin ganin ma’aikata da taurarin AREWA24 sun amsa tambayarku!

Shirye-Shiryen mu na yanzu

A danna nan domin kallon Shirye-Shiryen mu da dama a ATASHAR YOUTUBE!