Gari ya Waye

Gari ya Waye 2017-12-01T23:17:15+01:00

Project Description

Bayanai

Lokacin wannan shirin:
Litinin zuwa jumma’a da kuma shiri na musamman ranar asabar da lahadi

Shirin:
Arewa 24

Bayani kan shirye-shiryen mu

Shirin GARI YA WAYE, shiri ne na musamman na Gidan AREWA24 ke kawo muku a kowacce safiya, shirin yana duba ne ga dukkanin rayuwar Arewacin Najeriya; Al’adu da Wasanni da Matasa da al’amuran dake faruwa yau da gobe na Fasaha da Wasannin Kwaikwayo da Kiwon Lafiya da Motsa Jiki, Zamantakewa, Harkokin Kasuwanci, Nishadantarwa da Jaruman ‘Yanwasa da ma wasun su, Shirye-shiryen Gari ya waye sun hada da Tattaunawa akan muhimman batutuwa da Rahotanni da suka saba zuwa a cikin shirin.

wannan shirin na tsawon awa daya ya tabo bangarori da dama:

TEAWannan bbin yana duba ne akan abubuwan da suka shafi mata da kananan yara a Arewacin Nigeria. Wannan babi an shirya shi ne musamman don iyaye matasan mata, amma zai amfanar da mata ko wadanne iri. Ya kunshi ilmi, sana’a, rainon yaro, shiga huldodin yau da kullum al’ada’ addini da sauransu.
arewa-video-kannywood-movie2A’umma kamar ko wace rayuwa, an gina ta ne akan dangantaka, ko tsarin iyali, abota,soyayya, tattalin arziki, abokan karatu ko makotaka. Yadda muka yi amfani da wan-nan damar shine ma’aunin da zai sa muci nasara ko muyi farin ciki. Wannan babi zai duba yadda dangantaka take a tsakanin mu da kuma yadda kowa zai bada gudunmowa wajen gina al’umma mai inganci ta hanyar aikin mu, dabi’un mu da hukuncin mu.
DIRECTOR Saira-aminu-1561273454Wannan babi zai mayar da hankali ne a kan fitattun ‘yan wasan Hausa,ba don nishadantarwa ba kawai, don kuma yayi nuni sannan ya ilmantar da masu kallon mu. Shirin kuma zai kawo muku bayanai akan sababbin fina-finai da kuma rayuwar jarumai da ma’aikatan bayan fage da kuma irin dangantakar da take tsakanin su da rawar da kowa yake takawa.
HARSHE-4Wannan sashi zai yi nuni akan asalin harshen Hausa, yayi nuni akan kyawun harshen da kuma yadda ake furta shi a bangarori daban daban na kasar Hausa. Za’a tattauna da masana, shehun nan malamai wadanda suka san tarihi su yi bayanin yadda bambance bambancen ya karawa harshen fadi da armashi.
arewa-video-youth-role-models2Wannan bangaren yana zaburar da matasa akan dogaro da kai da shiga makaranta. A kullum wannan babin zai tattauna da mutanen da suka yi fice a sana’o’i daban daban da yadda akay isuka yi fice akan su da nufin matasa su yi koyi da abinda aka yi bayani akai.
Breakfast ShowMutane da yawa basu san muhimmancin kiwon lafiya ba, wasannin motsa jini, ziyartar asibiti, da cin abincin da ya dace. Mutane da dama basa gane alamomin ciwukan da suke damun su,don haka sai su sha maganin da bashi ya dace ba. Wannan bangaren yana nuni ne akan yadda mutane zasu zauna cikin koshin lafiya.
ADO DA KWALIYA 3Wannan bangaren yana Magana ne akan yadda kayan sakawa na gargajiya yake. Yana nuna wa masu kallo cewa sitirar mu aba ce muhimmiya a rayuwar mu da al’adar mu.
baban-zaure-3Wannan bangaren yana tattaunawa ne da manyan mutane, su yi bayanin yadda suka sha wahala kafin su zama abinda suka zama.
arewa-video-morning-show2Nigeria, kasa ce mai yawan jama’a da kabilu daban daban don haka zai yi wahala a dauki abinci guda daya a matsayin abincin ta. Ko wane bangare yana da irin nasa abincin, amma shigowar ciye ciyen zamani yana neman ya batar da wadannan abinci. Ilmin sanin makamar yadda ake yin irin wadannan abinci yana gushewa, haka ma al’adunsu. Wannan sashi zai farfadowa da masu kallon mu wadannan abinci don tabbatar da cewa ba’a manta da su ba.
Google ChromeScreenSnapz005Yawancin matasa yanzu sun jefar da al’adunsu,sun dauki al’adun da ba nasu ba. Wannan sashin zai wayar musu da kai akan su san muhimmancin al’adun su don su rungume su.
arewa-video-youth-magazine2Wannan shiri ne dayake kawo rahotanni na al’amuran yau da kullum ga al’umma.
arewa-video-h-hip-hop4Wannan shiri ne da yake nuna wakoki kuma ya tattauna da fitattun mawaka daga Arewacin Nigeria.
vlcsnap-2014-08-19-18h12m00s149Wannan babi ne da yake tsokaci akan bukukuwan mu na yau da kullum, na al’ada da kuma addini daga duk fadin Arewacin Nigeria.

Shirye-Shiryen mu na yanzu

A danna nan domin kallon Shirye-Shiryen mu da dama a ATASHAR YOUTUBE.