Show Description

Bayanai

Lokacin wannan shirin:
Talata

Shirin:
Arewa 24

Bayani kan shirye-shiryen mu

Shirin Kundin Kannywood, shiri ne dake duba ciki da wajen Masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood a Arewacin Nijeriya na tsawon sa’a guda; wanda daya daga cikin fitattun jaruman da ake so na Masana’antar Kannywood, kuma Ma’aikacin Arewa24 wato Aminu Shariff yake gabatarwa. Shirin zai yi duba ne ga sababbin fina-finai dake tashe, sannan ya baiwa masu kallon Tashar Arewa24 damar yin tambayoyi akan fitattun Jarumai da rawar da suke takawa da sana’ar su da kuma ra’ayoyin su, sannan ya zabi fitattun Fina-finai goma da suka yi fice a kowanne mako, shirin zai bi masu shirya shirya fina-finai fagen fama don ya kawo muku yadda ake gudanar da shirin fim a Kannywood, sannan kuma, ya tattauna da Jarumai da Masu bada Umarni da kuma Masu shiryawa.

Shirye-Shiryen mu na yanzu


A danna nan domin kallon Shirye-Shiryen mu da dama a ATASHAR YOUTUBE.