Matasa@360

Matasa@360 2017-12-02T00:09:47+01:00

Project Description

Bayanai

Lokacin wannan shirin:
Litinin

Shirin:
Arewa 24

Bayani Kan Shirye-shiryenmu

Shirin Matasa’@360 zai maida hankali ne ga al’adar matasa, wannan shirin na matasa@360 yana baiwa masu kallo damar ganin yadda matasa masu magana da harshen Hausa suke a Nahiyar Afirka ta yamma a wannan zamani. Shirin yana maida hankali ne akan abubuwan da suka shafi matsaloli irin na sana’o’in hannu da kayan sakawa na zamani da abubuwan da ake yayi, inda Sashin Matasa masu gabatar da shirye-shirye na Tashar Arewa24. Ke baiwa matasa dama ta hanyar da zasu amayar da abubuwan dake da muhimmanci a rayuwar su, Shirin Matasa@360 yana karfafawa matasa gwiwa su zama masu tsarawa kansu ci-gaba da sanin tudun dafawa a rayuwar su.

Matasa@360 yana da kashe-kashe da dama:

vibesMajibatan al’amuran matasa suna daukar amsakuwa su nuna ra’ayinsu kuma su bada shawara akan muhimman abubuwan da suka shafi matasa a yau, kama daga shan kwayoyi da rashin aikin yi zuwa zaman Lafiya da mutunta juna. Bakinmu suna amayar da abinda yake zuciyarsu don samar da hanyoyin da matasa masu kallo zasu iya yin kokari wajen maganta matsalolinsu kuma su dauki matakin da ya dace.
pulseWannan jerin nune nune na gabatar da bidiyon da matasa suka bayyana ra’ayoyinsu akan abubuwan da suka shafe su, kuma suka aiko da su ta hanyar wayoyinsu na hannu daga duk fadin Arewacin Najeriya. Wannan shirin da yake bada damar tsoma baki daga waje, ya bawa masu kallo damar tsoma baki a cikin shirin kuma hakan ya tabbatar da kududirin shirin Matasa@360 na matasa, don matasa, kuma wanda matasa ke yi.
Musicology A wannan zamanin Kashe-kashen kade-kade da wake-wake na Hausa ya gaji asali daga al’adu daban daban da kuma abinda ya bijiro da kade-kaden da wake-waken; wannan kashi yana tsefe matasan mawaka a kokarinsu na farfado da kade-kaden gargajiya.
trendsWannan kashin yana yin nuni ne ga suturar da ake yayi, gayu da kuma sababbin kirkire-kirkire daga zuciyoyin matasa. Ko wane sati mai gabatar da shirin Fa’iza Shehu takan yi duba akan sababbin yayi na dinke-dinke da kawata jiki, zuwa fasaha da kuma abinda ya yada gari a kafafen sada zumunci da yanar gizo a wannan lokacin.
Talent ProfileKowane kashi na wannan bangare ya tsefe rayuwar wani matashi da yayi fice a wani bangare na fasaha, kirkira da sana’a. Bakin mu da muka gayyata suna zunguro fannonin da suka hada da zamani da gargajiya, wadanda suka hada da masu fenti, marubuta, masu zane, mawaka, da ‘Yan kasuwa. Wannan tattaunawa tana bayyana gwagwarmayar da bakin mu suka sha kafin su kai matsayin da suka kai da kuma tasirin da sana’arsu take da shi a kansu da al’umarsu a yanzu.

Shirye-Shiryen mu na yanzu

A danna nan domin kallon Shirye-Shiryen mu da dama a ATASHAR YOUTUBE.