Shirye-shiryen Kasashen Ketare

Shirye-shiryen Kasashen Ketare 2018-02-08T15:13:03+01:00

Project Description

AREWA24 ta kawo muku sababbin fina-finai masu kayatarwa daga manyan gidajen talabijin na duniya da suka hada da Aljazeera, Zuku TV, da Endemol. Shirye-shiryen yara kamar su 99 da Malaman Musulunci wadanda suke cike da nishadantarwa da kuma koyarwa ga dukkan iyali. Shirin sharhin kwallon kafa, yana nuna tattaunawa, labarai da kuma cin kwalakwalai daga gasar kwallon kafa ta turai domin kashe kishirwar ma’abota wasanni. Haka kuma masu kallonmu zasu iya tsunduma dajin Afirka idan suka kalli jerin shrinmu na Africa Odessey, ko suka yi ninkaya zuwa dajukan Afirka ta Gabas domin nemo abubuwan girke-girke ta shirinmu na Tales of The Bush Larder. Masu kallonmu ma’abota wasan kwaikwayo zasu iya kamo sabon jerin wasan kwaikwayonmu na kasar Turkiyya, Kyautata Rayuwa, kuma su kalli daya daga cikin tarin fina-finanmu na Bollywood da Kannywood. Ko wace irin nishadantarwa kuke bukata, zaku iya samu a daya daga cikin shirye-shiryenmu da ake gabatar da su a harshen Hausa.

AREWA24 na nuna ingantattun fina’-finan kasashen waje da harshen Hausa a farko, da suka hada da:

HARSHE-4Shirin Sharhin Kwallon Kafa, shiri ne da Masana’antar DIS ta shirya shi a HD, Tashar Arewa24 kuma ta dauke shi da Harshen Hausa. Wannan shahararran shirin wasanni dake zuwa muku a kowanne mako, na cike da sabbabin labarun wasannin kwallon Kafa da aka samo su daga wasannin cin kofin Nahiyar Turai wato Champion League da na ‘Premier League da na ‘La Liga’ da na ‘Serie A’ da na Bundesliga da kuma na ‘Ligue One, da ma wasun su. Inda masoya suka bukaci sharhi da bayanai na musamman. Wannan shiri na Sharhin Kwallon kafa gagarumi ne kuma mai muhimmanci dake dadada rai. Shirin Sharhin Kwallon Kafa yafi gaban rahotanni irin na yau da kullum, wanda ke gabatar da gagarumar muhawara da kuma tattaunawa.
arewa-video-youth-role-models2Wannan wani sabon shiri ne dake kunshe da wasu jerin wasanni da zai rika zuwa muku a kowanne mako dauke da kayatattun labarai dangane da yadda harkokin wasanni daban-daban suka canja rayukan wasu ‘yan wasa a cikin Kasa Najeriya ta fuskoki da dama. Wanda jajircewa na kaiwa ga kololuwa ya zama wata kafa tattare da darusan da zasu kara kaimi ga kafatanin al’aumma baki daya. Kowanne shiri, yana mayar da hankali ne da wata siga ta daban, wanda farkonsa zai somo da kalubale mafi wuya, sa’annan ya sauya da samun nasara da kaiwa ga gaci. Daga karshe kuma, su kai ga kololuwa a rayuwa.
statehouseShirin ‘LEGENDS’ da zai kewaya da masu kallo fadin Duniya ya kuma yi duba ga rayuwar Shararrun ‘Yan wasa a kowanne irin wasannin motsa jiki da abinda ya ja hankulansu da yadda suka sauya tunanin al’umma da kuma abinda ke kunshe da sauyuwarsu har ta kai su ga samun nasara. Wannan kayataccen shirin, yana koyar da mu dangane da irin daraja da dabi’a da tashe da kuma kudirin da ke sanya ‘yan wasa su zama gawurtattu a kowanne lokaci.
vlcsnap-2014-08-19-18h12m00s149Wannan shirin harkokin kwallon kafa ne da yake zakulo muhimman bayanai daga manyan kungiyoyin Kwallon Kafa dake Nahiyar Turai da wadansu kasashen daban, domin masoya harkokin Wasannin dake Arewacin Najeriya. Shirin Clubland, ya zaiyano nasarori da kalubale da kuma manyan batuttuwa na kungiyoyin ‘Yan wasa Gasar Wasanni ta Firimiya da Gasar La Liga haka kuma da wasu manyan kungiyoyin ‘yan-wasa da muka sani muke kuma kauna.
baban-zaure-3Hawk Speed shiri ne da yake dauke da fitattun wasannin tsere da na Matuka Babura, wanda ya hada da Nasarorin su da kalubalen su da illolin da suke gamuwa da su da dukkanin abubuwan da ya kunshi Babur da kuma gyaran sa. Inda tsofaffin mahaya Baburan ke nuna bajintar su akan Baburan da suka fi kauna da kuma yadda suka kai ga kololuwar su.
Wannan kirkirarran shiri ne da aka shirya shi domin Yara, don wayar musu da kai game da littafin tsatsuniyoyi a kuma dada jaddada wayar musu da kai a kan akidar nan ta shiga duniyar karance-karance da kuma karfafa tunaninsu. Ana gabatar da wannan shiri domin Iyaye su kalla tare da ‘Ya’yansu. A kowanne kashi, an gayyaci fitattun ‘yan wasa don su karanto labarin wanda kowanne ke koyar da darussa da kuma dab’iu irin ta Nahiyar Afirika. An sanya fitattun daidaikun shahararrun ‘yan wasa da ya karanta labarin ta hanyar da ya ga ta dace, domin su sanya halayyarsu da dabi’unsu na musamman don karawa labarin nasu armashi.
Google ChromeScreenSnapz005Wannan wani shahararren jerin shirin katun ne da Kamfanin ‘Big Bad Boo’ ke gabatarwa inda suke kawo muku tsatsuniyoyin yankin Larabawa na Dare Dubu Daya’. Tashar Arewa24 na alfahari da kawo wannan shiri da harshen Hausa da aka haska shi a Kasashe sama da Dubu Tamanin don kawo muku kayatattun Tsatsuniyoyi na ‘Aladin da ‘Sinbad’ da kuma ‘Ali Baba saboda masu kallo a yankin Afrika, wadan nan shirye-shirye, an shirya su ne cikin harshen hausa.
Wannan shahararran shiri domin yara, an shirya shi cikin zane domin ‘Yara, labari ne game da wani Yaro a cikin aji da yake yaruka iri tattare da yaruka iri daban-daban da suka samar da ‘Nut’
arewa-video-h-hip-hop4Wannan shiri na ‘Manoma’ zai kawo muku Noma da aikace-aikacen noma iri daban-daban a fadin kasar nan, inda shirin zai maida hankali wajen ire-iren Noma da kiwon Dabbobi, wannan shirin yana karfafawa wajen aikace-aikace da sana’ar Noma da kuma hukomumin aikin Gona da kuma samar da bayanai da horo a kan dabarun noman zamani.
Breakfast ShowWadan nan shirye-shirye, za su kawo muku mutane na musamman wadanda suka magance kalubale iri daban-daban na zahiri, da shawo kansu da kuma gabatarwa masu kallo labarai masu ban sha’awa na maida hankali da samun nasarori a rayuwa.Wadan nan shirye-shirye, za su kawo muku mutane na musamman wadanda suka magance kalubale iri daban-daban na zahiri, da shawo kansu da kuma gabatarwa masu kallo labarai masu ban sha’awa na maida hankali da samun nasarori a rayuwa.
arewa-video-kannywood-movie2 alt=AREWA24 zata kawo muku gungun fina-finan Kannywood daga mashahuran masu bada umarni da masu daukar nauyi a masana’antar. Masu kallo zasu ga taurarinsu irinsu Jamila Nagudu, Ali Nuhu, da Adam A. Zango wadanda suke wasan kwaikwayon da yake cike da kalubale da ake nunawa kullum a AREWA24.