Taka Leda

Taka Leda 2017-12-02T00:15:47+01:00

Project Description

Bayanai

Lokacin wannan shirin:
Talata

Shirin:
AREWA24

Bayani kan shirye-shiryen mu

Wannan shiri ne mai kayatarwa da ke zuwa muku a kowanne mako, wanda ya kunshi sakamakon wasannin da suka fi shahara da Sharhin Wasanni da kuma hasashen magoya baya a duniyar kwallon kafa da ke Nahiyar Turai da kuma wasannin Gida Najeriya. Shirin zai rika kawo muku tattaunawa da ‘Yan-wasa da Masu horaswa don baku damar sanin abinda ake toyawa a fagen kwallo kafa tsakanin kungiyoyin kwallon kafa dake nan gida, da kuma tattaunawa akan wasannin da suka gabata, wanda ya hada da wasanni da yadda wasan zai kaya tun kafin farawa da dabarun horaswa da kuma burukan ‘yan wasa da ake son cimmawa a nan gaba. Wannan shiri, zai gayyato magoya bayan manyan abokan karawa daban-daban cikin dakin watsa shirye-shiyen mu don tattaunawa da tafka muhawara game da wasannin su da kuma hasashe ga wasannin masu zuwa a gaba.