Zango na 2 na Shararren Wasan Kwaikwayon nan na AREWA24 Mai Dogon Zango da aka dade ana jira wato “Zabi Biyu” ya dawo
24 ga watan Maris 2026 – AREWA24, tashar talabijin da ke kan gaba wajen yaɗa shirye-shirye masu nishaɗantar da iyali da tsarin rayuwa cikin harshen Hausa, wadda ke da ofishin samar da shirye-shirye a Najeriya da yammacin Afirka, ta dawo da shararren shirin wasan kwaikwayon nan nata “Zabi Biyu” a zango na biyu da aka dade ana dakon jira bayan kammala shirye-shiryen Ramadan.
Biyo bayan nasarar fitowar zango na farko, shirin wasan kwaikwayo na Zabi Biyi ya samu karbuwa da jan hankalin masu kallo a fadin Arewacin Najeriya da sauran bangarori, da labari mai kayatarwa, da mahimman abubuwa na al’adu, da kuma jarumai da masu shiga ran masu kallo. Shirin mai dogon zango ya zamo abin so ga masu kallonsa cikin sauri, wanda ake yabonsa saboda yadda ya nuna hakikanin soyayya, zabi, da kuma rudanin da ke cikin alaka ta zamani a tsakanin al’umma ‘yan gargajiya.
Babu shakka zango na biyu zai gina a kan wannan nasara da aka samu a baya da karin rigingimu, da cigaban labarin jaruman, da kuma wasu sauye-saye da ba a zata ba. Masu kallo za su ci gaba da bin labarin yayin da jaruman ke fuskantar sakamakon zabukan da suka yi a baya, yayin da suke fuskantar sabbin kalubale da za su gwada dabi’unsu, dangantakarsu, da burikansu.
Da yake magana game da sabon zagon, Babban Shugaban AREWA24, ya bayyana cewa:
“Shirin wasan kwaikwayo na Zabi Biyu yana wakiltar shirin wasan kwaikwayo ne mai ma’ana da ya dace da al’adu wanda muka kuduri aniyar gabatarwa ga masu kallonmu, musamman matasa da matsakaitan mutane. Martanin da aka samu a kan zango na 1 ya kasance abin mamaki matuƙa, kuma muna matuƙar farin ciki da kawo zango na 2, wanda zai fi jan hankali da kayatarwa ga masu kallo. Ga masu talla kuwa, za su samu damar haduwa da masu kallo ta hanya mai ma’ana, ta hanyar bibiyar dinbin masu kallon talabijin a cikin al’ummomin masu magana da harshen Hausa.”
Shirin wanda ma’aikatan AREWA24 suka samar, yana ci gaba da cika manufar tashar na samar da ingantattun shirye-shirye da harshen Hausa wadanda ke nuna hakikanin rayuwa da burikan da masu kallonta suke da shi.
A cewar Salisu Balarabe, Daraktan ‘Zabi Biyu “A tsakiyar shirin ‘Zabi Biyu’ akwai wani labari da ke nuna rayuwar yau da kullum ta masu kallonmu, shirin kuma yana ci gaba da bunƙasa cikin yanayi mai tsananin jan hankali da taba zuciya mataki mataki, yayin da a lokaci guda yake ci gaba da kiyaye al’adu, harshe, da dukkanin abubuwan yau da kullum na zahiri da ke jan hankalin al’ummomi masu magana da Hausa.”
An fara nuna zango na 2 na shirin ‘Zabi Biyu’ a ranar Lahadi 22 ga Maris, 2026, kuma za a rika haskawa a kowane mako a ranakun Lahadi daga karfe 8:00 na dare zuwa 9:00 na dare (20:00H WAT), tare da ƙarin damar kallo a manhajar kallo kai tsaye ta AREWA24 (AREWA24 on DEMAND).
GAME DA AREWA24 (https://arewa24.com/company-overview/): AREWA24 da Bangarenta na samar da shirye-shirye, An fara gabatar da shiryen shiryen AREWA24 a shekarar 2014 domin cike wawakeken gibin da ake da shi a fagen shirye-shiryen nishadi da tsarin rayuwa da ake shiryawa da harshen Hausa masu inganci, wadanda ke nuni da abubuwan da ake alfahari da su a rayuwar Arewacin Najeriya, da al’adu, da kade-kade, da fina-finai, da fasaha, da girke-girke da kuma wasanni. A yau, tashar AREWA24 tana kaiwa ga mutane sama da milyan 50 masu magana da harshen Hausa a Najeriya da kuma Yammacin Afirka a kan tauraron dan dan’adam na Eutelsat da ke kan tsarin kallo kyauta, da kuma kan tauraron dan adam na StarTimes da ke kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba 138), da kafafen tauraron dan’adam na kamfanin Multichoice guda biyu da ke kan tsarin biya kudi, wato DSTV (tasha mai lamba 261) da kuma Gotv (tasha mai lamba 136), da kuma tauraron dan adam na Canal+ a kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba #297) a Jamhuriyar Nijar, da Chadi da kuma Kamaru, AREWA24 na amfana da masu kallo da ke kasancewa da dukkanin shafukanta na yanar gizo a kanAREWA24.com, facebook.com/AREWA24, da Instagram.com/AREWA24channel. Haka kuma AREWA24 tana yada shirye-shiryenta a tsarin kallo kai tsaye a ko ina a duniya a kan AREWA24 On Demand tare da hadin guiwar Vimeo.
Domin samun damar kallo kai tsaye a ko ina a duniya a kan AREWA24 ON DEMAND, ku shigahttp://tv.arewa24.com ko ku sauke manhajar daga kan IOS App Store, ko Google Play, ko Apple TV, ko Roku Channel Store da kuma Amazon Fire TV.
Domin karin bayani, sai ku tuntubi: info@arewa24.com
AREAW24 is the leading Hausa language entertainment and lifestyle network in Nigeria and West Africa, reaching over 50+M viewers via
Free-to-Air Satellite and major PayTV services.