Shirin Matasa’@360 zai maida hankali ne ga al’adar matasa, wannan shirin na matasa@360 yana baiwa masu kallo damar ganin yadda matasa masu magana da harshen Hausa suke a Nahiyar Afirka ta yamma a wannan zamani.
Shirin yana maida hankali ne akan abubuwan da suka shafi matsaloli irin na sana’o’in hannu da kayan sakawa na zamani da abubuwan da ake yayi, inda Sashin Matasa masu gabatar da shirye-shirye na Tashar Arewa24.
Ke baiwa matasa dama ta hanyar da zasu amayar da abubuwan dake da muhimmanci a rayuwar su, Shirin Matasa@360 yana karfafawa matasa gwiwa su zama masu tsarawa kansu ci-gaba da sanin tudun dafawa a rayuwar su.