15 ga Afrilu 2025.  FOR IMMEDIATE RELEASE                                                           

AREWA24, tashar talabijin da ke kan gaba wajen yaɗa shirye-shirye masu nishaɗantar da iyali da da tsarin rayuwa cikin Harshen Hausa tsawon sa’o’i 24 a dukkanin ranakun mako, tana sanar da gagarumin sauyin shugabanci da ta samu a karon farko tsawon shekaru goma. Celestine Umeibe, wanda a halin yanzu yake matsayin mataimakin Shugaban AREWA24 (AREWA24’s Deputy CEO and Chief Commercial Officer), shi ne zai karɓi muƙamin Babban Shugaba wato Chief Executive Officer, inda zai gaji Jacob Arback, wanda shi kuma zai koma sabon muƙamin Executive Vice Chairman, wato Babban Mataimakin Shugaban Gudanarwa. Mr. Umeibe zai ci gaba da kula da dukkanin harkokin tallace-tallace da kasuwanci na kamfanin.

A cewar Celestine Umeibe: “Jacob Arback ya taka mahimmiyar rawa a gagarumar nasarar da AREWA24 ta samu tsawon shekaru goma da suka wuce. Salon shugabancinsa na musamman da bawa kowa dama domin bada gudunmawarsa ya bawa AREWA24 dama wajen tsallake duk wasu matsaloli na kasuwance da kuma ƙalubalen da kan addabi sabbin harkokin kasuwanci, musamman a wannan yanki. Karin matsayi da Mr. Arback ya samu zuwa Babban Mataimakin Shugaban Gudanarwa abu ne da ya cancanta, kuma babu ko shakka zai ci gaba da kawo cigaba a cikin kasuwancin wannan kamfani.

Shugaban mai barin gado, Jacob Arback, ya yi aiki tare da Mr. Umeibe a AREWA24 tun daga lokacin da aka kafa tashar a shekarar 2014. “Babu wani wanda ya fi cancanta da dacewa ya jagoranci AREWA24 cikin shekaru goma masu zuwa da za su zo da cigaba da kuma alfanu sama da Celestine,” a cewar Arback. “Baiwar da yake da ita ta shugabanci, kasuwanci da gogewa kan abubuwan da aka san kamfani a kai, da kuma zurfin ilimi game da bangaren kafafen yaɗa labarar da samar da shirye-shirye masu nishaɗantarwa sun sa Celestine ya zamo wani zaɓi mai sauƙi ga Daraktocin Gudanarwarmu. Ina matuƙar ɗokin ganin yadda shekaru goma masu zuwa cike da ƙirƙira, da sabbin abubuwa da kuma bunƙasa da ci gaba za su kasance ƙarƙashin jagorancinsa. Tun daga farkon kafa AREWA24, Celestine ya nuna jajircewa bisa “Dalilin” kafa tashar AREWA24 – – ‘don nunawa da kuma alfahari da al’adun gargajiya kuma cikin Harshen Hausa.’

Aiki da Mr. Umeibe sama da shekaru 10+ a  AREWA24, gami da matsayinsa na baya na shugaban sashen tallace-tallace, da kasuwanci, da matsayinsa na kasuwanci da ya riƙe a StarTimes da kuma TVC, ya kawo gagarumar gogewa ta kawo sauyin da AREWA24 ta kawo a tsakanin tashoshin talabijin da kafafen yaɗa labarai, tare da hangen nesa game da makomar kamfanin. Mr. Umeibe zai yi aiki wajen yin amfani da basira wajen yanke hukunci kan shirye-shirye, da amfani da cigaban fasahohin zamani da kuma samar da sabbin hanyoyin samun kuɗaɗen shiga domin ciyar da manufar AREWA24 gaba ta zamowa ɗaya daga cikin manyan tashoshin talabijin na Afirka, da samar da shirye-shirye, da kuma kamfanonin yaɗa labarai na nahiyar.

GAME DA AREWA24:  AREWA24 da Bangarenta na samar da shirye-shirye, An fara gabatar da shiryen shiryen AREWA24 a shekarar 2014 domin cike wawakeken gibin da ake da shi a fagen shirye-shiryen nishadi da tsarin rayuwa da ake shiryawa da harshen Hausa masu inganci, wadanda ke nuni da abubuwan da ake alfahari da su a rayuwar Arewacin Najeriya, da al’adu, da kade-kade, da fina-finai, da fasaha, da girke-girke da kuma wasanni. A yau, tashar AREWA24 tana kaiwa ga mutane sama da milyan 40 masu magana da harshen Hausa a Najeriya da kuma Yammacin Afirka a kan tauraron dan dan’adam na Eutelsat da ke kan tsarin kallo kyauta, da kuma kan tauraron dan adam na StarTimes da ke kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba 138), da kafafen tauraron dan’adam na kamfanin Multichoice guda biyu da ke kan tsarin biya kudi, wato DSTV (tasha mai lamba 261) da kuma Gotv (tasha mai lamba 136), da kuma tauraron dan adam na Canal+ a kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba #297) a Jamhuriyar Benin, da Burkina Faso, da Cameroon, da Chad, da Mali, da Nijar, da kuma  Togo Nijar, AREWA24 na amfana da masu kallo da ke kasancewa da dukkanin shafukanta na yanar gizo a kan www.AREWA24.COMwww.facebook.com/AREWA24,da Instagram.com/AREWA24channel.  Haka kuma AREWA24 tana yada shirye-shiryenta a tsarin kallo kai tsaye a ko ina a duniya a kan AREWA24 On Demand tare da hadin guiwar Vimeo. Domin samun damar kallo kai tsaye a ko ina a duniya a kan AREWA24 ON DEMAND, ku shiga http://tv.arewa24.com ko ku sauke manhajar daga kan IOS App Store, ko Google Play, ko Apple TV, ko Roku Channel Store da kuma Amazon Fire TV.

Domin karin bayani, sai ku tuntubi: info@arewa24.com