AREWA24, tashar talabijin da ke kan gaba wajen yada shirye-shiryen nishadantar da iyali da tsarin rayuwa, wadda ke da ofishin daukar shirye-shiryenta a Najeriya a Yammacin Afirka, tana sanar da kaddamar da sabon sashen wasannin kwaikwayo da fina-finan da take shiryawa. Sabon sashen shirye-shiryen kamfanin zai samar da rubutun labaru da kuma shirya sabon jadawalin sabbin wasannin kwaikwayo masu dogon zango da kuma daidaikun fina-finai, don bada labarun Afirka na asali daga Arewacin Najeriya da kuma Yammacin Nahiyar Afirka da harshen Hausa da kuma na harshen Turanci zalla.
Ofishin samar da shirye-shiryen tashar AREWA24, ya kasance yana shiryawa da kuma yada kayatattu kuma shahararrun wasannin kwaikwayo masu dogon zango na Hausa a Arewacin Najeriya da Yammacin Afirka, wato “Dadin Kowa” wanda a halin yanzu ya kai zango na 25, da kuma wasan kwaikwayon tashar da ya kunshi siyasa, wato “Kwana Casa’in” (“90 Days”), wanda aka kammala daukar zango na 7 a kwanannan. Ana kan shirya wasu wasannin kwaikwayon masu dogon zango da dama, kuma wannan kamfani zai fara nuna shirin fim mai gajeren zango da ya shirya na farko a zango na hudu a shekarar 2022.
“AREWA24” ta kasance tana daga darajar wasu daga cikin kwararrun marubutan Najeriya, da masu shirya fina-finai, da daraktoci, da masu tace hotuna da kuma jarumai tun bayan kafuwar tashar shekaru takwas da suka gabata. Shugaban tashar AREWA24 Jacob Arback, ya bayyana cewa, “A halin yanzu muna matsayin babban kamfanin samar da shirye-shirye na ‘yan Afirka, mai samar da tsararrun shirye-shirye masu inganci na Afirka – domin ‘yan Najeriya, da ‘yan Afirka da kuma masu kallo da ke yammacin duniya, wadanda ke kara jin dadin kallon irin wadannan labaru masu kayatarwa da aka tsara su da inganci cikin wasannin kwaikwayo da fina-finai daga wannan nahiya”.
Shugaban sabon sashen wasannin kwaikwayon da fina-finai shi ne Evans Ejioju, wani gogagge kuma kwararre, da ya kasance a matsayin babban mai shirya shirin wasan kwaikwayon nan mai dogon zango na Kwana Casa’in tun daga zango na farko. Salisu Balabare, wanda ke bada umarni a shirin na Kwana Casa’in kuma wanda ya dade yana bada umarni a shirin wasan kwaikwayo nan mai dogon zango na Dadin Kowa, shi ne zai jagoranci bangaren kirkira na wannan sabon sashe. Bob Reid, sanannan da ya lashe lambar yabo ta Emmy-award a matsayin babban mashiryin shirin nan na kamfanin Discovery Networks, kuma tsohon mai kula da kimar ma’aikata (EVP), kuma babban shugaban sashen shirye-shirye a tashar The Africa Channel da ke kasar Amurka, shi ne zai kasance a matsayin mashawarci kuma babban mashiryin shiri na wasannin kwaikwayo da fina-finan da tashar AREWA24 ke shiryawa.
Samar da wannan sabon sashen na wasannin kwaikwayo da fina-finai, zai sa tashar AREWA24 ta amfani kwarewa da kuma kayan aikin shirye-shirye da ta tattara, sannan kuma ta nemi abokan hulda masu kaifin basira daga dukkanin fadin duniya, da kuma manyan kamfanonin da ke aikin yada shirye-shirye kai tsaye ta yanar gizo (streaming services) a duniya, domin bunkasawa da shirya rubutattun shirye-shirye.
“Manufarmu ita ce, shirya karin fitattu kuma kayatattun wasannin kwaikwayo domin masu kallonmu da ke magana da harshen Hausa”. Arback ya ce, “Wasu daga cikin shirye-shiryen da za mu samar, ba lallai a fara nuna su a tashar AREWA24 ba. A nan gaba, mun shirya samar da jadawalin shirye-shirye da suka dace da masu kallo a fadin nahiyar Afirka da kuma sauran sassa na duniya. Sabon sashen shirye-shiryen zai bamu dama mu tsara shirye-shiryenmu domin su dace da dukkanin masu kallo. Don yin hakan, mun tsara shirya shirye-shirye na ‘yan Afirka masu inganci da harshen Turanci da kuma harshen Hausa kuma mu tabo karin batutuwan da ke ciwa mutane tuwo a kwarya a cikin nau’ikan shirye-shirye da dama.”
GAME DA TASHAR AREWA24: Tahsar AREWA24 da bangaren shirye-shiryenta, an kafa Tashar AREWA24 a shekarar 2014 domin cike wawakeken gibin da ake da shi a fagen shirye-shiryen nishadi da tsarin rayuwa da ake shiryawa da harshen Hausa, wadanda ke nuni da abubuwan da ake alfahari da su a rayuwar Arewacin Najeriya, da al’adu, da kade-kade, da fina-finai, da fasaha, da girke-girke da kuma wasanni. A yau, tashar AREWA24 tana kaiwa ga mutane sama da milyan 40 masu magana da harshen Hausa a Najeriya da kuma yammacin nahiyar Afirka a kan tauraron dan dan’adam na Eutelsat da ke kan tsarin kallo kyauta, da kuma kan tauraron dan adam na StarTimes da ke kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba 138), da kafafen tauraron dan’adam na kamfanin Multichoice guda biyu da ke kan tsarin biya kudi, wato DSTV (tasha mai lamba 261) da kuma Gotv (tasha mai lamba 101), da kuma tauraron dan adam na Canal+ a kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba #285) a Jamhuriyar Nijar, da Chadi da kuma Kamaru. AREWA24 na amfana da masu kallo da ke kasancewa da dukkanin shafukanta na yanar gizo a kan AREWA24.com, facebook.com/AREWA24, Instagram.com/AREWA24channel. AREWA24 tana kuma yada shirye-shirye kai tsaye ta yanar gizo a duniya a kan manhajar nan ta, AREWA24 On Demand tare da hadin guiwar kamfanin Vimeo.
Domin yin rijista da manhajar kallon shirye-shirye kai tsaye ta yanar gizo a kan manhajar AREWA24 ON DEMAND, sai ku ziyarci http://tv.arewa24.com ko kuma ku sauke manhajar daga IOS App Store, Google Play, Apple TV, Roku Channel Store da kuma Amazon Fire TV.
Domin karin bayani, sai ku tuntubi: info@arewa24.com