Author

About the Author
A Website Developer and Digital Content Creator, CloudOps Engineer, Web Developer & Tech Community Lead

Farm and fortune

Helen Paul da Frank Donga ne za su ke gabatar da shiri mai nuna manyan masana noma na kasar Najeriya.

N*Gen

Shirin kimiyya ga yara masu koyo. Zane-zane na kimiyya masu nishadantarwa, da shawarwari na  rayuwa.

Rayuwata

Wata yarinya dake karatun zama kwararriyar kuku. Ta hadu da wani matashi a cikin jirgin, inda ta dauki  jakarsa maimakon tata.

Matar Aure

Labari ne akan kaunar dake tsakanin wata mata da mijinta, da jarrabawar da suka shiga a sanadin dansu suka rasa duk abin da ya mallaka.

Ajeeb

Shiri ne na soyayya a kan rayuwar Vikram da Shobha, da iyalensu, da kuma yadda suke barin rayuwarsu ta baya domin kyautatuwar ta gaba.

StartUp Africa

StartUp Africa Gagarumin shirin talabijin ne da ke nuna yunkuri na cike gibin harkokin fasaha cikin nahiyar Afrika.

Zabin Raina

Shirine na Labari na ban al’ajabi game da wani likita da ya tsinci kansa tsakanin soyayya da kuma sadaukarwa.

AREWA24 ta Kaddamar da shirinta na “Watan Gangamin Mayar da Hankali Kan Lafiyar Kwakwalwa” A Daukacin Watan Yuli

AREWA24, tashar talabijin da ke kan gaba wajen gabatar da shirye-shirye masu nishadantar da iyali da tsari rayuwa cikin harshen Hausa, wadda ke da ofishinta na samar da shirye-shirye a Najeriya da kuma yammacin Afirka, tana sanar da kaddamar da wani shirin wayar da kai na watan mayar da hankali kan kula da lafiyar kwakwalwa.

A cikin daukacin watan yuni, tashar AREWA24 za ta sadaukar da manyan bangarorin shirin nan nata da ke zuwa a kullum, watao “Gari ya Waye”, da kuma shirin mata, watao “Mata a Yau” domin gabatar da jerin tattaunawa, da hira da wasu manyan likitoci, masu bada shawarwari da kuma sauran kwararru a bangaren lafiya, game da matsalolin da suka danganci lafiyar kwakwalwa a Arewacin Najeriya. Duk da cewa kwararu sun tabbatar da cewa lafiyar kwakwalwa wani mahimmin bangare ce ga lafiyar jiki da kasancewa cikin koshin ladiya, said ai an yi watsi da ita a Arewacin Najeriya da ma Najeriya baki daya.

Kamar yadda Kungiyar Likitocin Kwakwalwa ta Najeriya (APN) suka bayyana, cewa sama da ‘yan Najeriya milyan 60 ne ke fama da matsalolin lafiyar kwakwalwa, amma kaso 10 cikin dari ne kacal suke iya samun kulawar da ta kamata. Shugaban kungiyar likitocin ta APN, Taiwo Obindo ya bayyana cewa gibin da ake da shi wajen samun magani shi ne ya haifar da matsaloli da dama, da suka hada da rashin ilimin abin, wanda kuma hakan ya bar mutane da karancin bayanai game da abubuwan da ke haddasa matsalolin lafiyar kwakwalwa, da kasa gane su da kuma neman kulawar da ta dace.

Duk da tsananin da matsalolin lafiyar kwakwalwa suka yi a kasar nan, kamar yadda kungiyar likitoci ta Najriya ta bayyana, likitoci 350 ne kadai ke aiki a halin yanzu a Najeriya, wadda ke da adadin mutane milyan 220. A kiyasta cewa a kalla daya daga cikin kowanne mutum hudu a Najeriya yana rayuwa ne da wani nauyi na larurar kwakwalwa.

“Mutane basu fahimci abin da ya shafi lafiyar kwakwalwa ba,” kamar yadda wata kwararriya a fannin lafiyar kwakwalwa a Najeria, Aisha Bubah ta bayyana. Ta ce, “Don haka ne ake danganta lafiyar kwakwalwa da abubuwa da suka danganci al’adu, chamfe-chamfe da kuma tsafi. Sannan yadda ake tunanin mutanen da ke da lafiyar kwakwalwa a koda yaushe shi ne tunanin sai wadanda yanayin su ya ta’azzara.”

AREWA24 tana aiki domin cike wawakeken gibin ilimi ta hanyar bayar da mahimman bayanai da wayar da kai game da kula da lafiyar kwakwalwa, da larurorin kwakwalwa da kuma cikakkiyar lafiyar kwakwalwa. Manufar wannan shiri na gangamin lafiyar kwakwalwa da AREWA24 ta shirya shi ne ta cike gibin bayanan da ba a samu, ta hanyar samar da ingantattun bayanai da kuma kawar da nuna kyama da ke tattare da matsalolin lafiyar kwakwalwa. AREWA24 ta tattaro gamayyar rukunin masana lafiyar kwakwalwa, masu bada shawarwari da kwararru kana bin da ake Magana a kai, wadanda za su tattauna yadda za mu samar da wasu hanyoyi domin kula da lafiyar kwakwalwa, a daidaikunmu da kuma tare iyalanmu. Wannan ya hada da aiyuka, kama daga duba mara lafiya, gano cutar da ke damunsa, bashi magani da kuma shawarwari – duk domin kula da kuma dawo da koshin lafiyar kwakwalwar al’ummar Arewacin Najeriya.

“A AREWA24, mun mayar da hankali don yin amfani da sananniya, amintacciya kuma shararriyar tasharmu mai nishadantarwa domin hidimtawa al’ummar Arewacin Najeriya da gamgami masu alfani kamar wannan gangami namu da ke tafe “Watan Mayar da Hankali Kan Lafiyar Kwakwalwa”, ta bakin Aisha Lawal, babbar shugaba mai kula da Shirye-shiryen AREWA24 na dakunan shirye-shirye. Ta ce “Mun yi Imani wannan wani nauyi ne na al’umma a kanmu mu samar da musu da abin da ya fi nishadantar da masu kallo kawai. Shi yasa mu ke so mu wayar da kai a kan mahimman batutuwa a cikin al’ummarmu kamar abin da ya shafi lafiyar kwakwalwa. Muna so mu taimaka wajen ilimantarwa da fadakar da ‘ya’yanmu maza da mata, don taimaka musu su yi kyakkyawar rayuwa a nan gaba, da kuma kokarin magance abubuwan da ke jawo talauci, wanda tabarbarewar bangaren kula da lafiyar kwakwalwa ke bada gagarumar gudunmawa.”

GAME DA TASHAR AREWA24: Tahsar AREWA24 da shirye-shiryenta, an kafa Tashar AREWA24 a shekarar 2014 domin cike wawakeken gibin da ake da shi a fagen shirye-shiryen nishadi da tsarin rayuwa da ake shiryawa da harshen hausa, wadanda ke nuni da abubuwan da ake alfahari da su a rayuwar Arewacin Najeriya, da al’adu, da kade-kade, da fina-finai, da fasaha, da girke-girke da kuma wasanni. A yau, tashar AREWA24 tana kaiwa ga mutane sama da milyan 40 masu magana da harshen Hausa a Najeriya da kuma yammacin nahiyar Afirka a kan tauraron dan dan’adam na Eutelsat da ke kan tsarin kallo kyauta, da kuma kan tauraron dan adam na StarTimes da ke kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba 138), da kafafen tauraron dan’adam na kamfanin Multichoice guda biyu da ke kan tsarin biya kudi, wato DSTV (tasha mai lamba 261) da kuma Gotv (tasha mai lamba 101), da kuma tauraron dan adam na Canal+ a kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba #285) a Jamhuriyar Nijar, da Chadi da kuma Kamaru. AREWA24 na amfana da masu kallo da ke kasancewa da dukkanin shafukanta na yanar gizo a kan AREWA24.com, facebook.com/AREWA24, da Instagram.com/AREWA24channel. Haka kuma AREWA24 tana yada shirye-shiryenta a tsarin kallo kai tsaye a ko ina a duniya a kan AREWA24 On Demand tare da hadin guiwar Vimeo.

Domin samun damar kallo kai tsaye a ko ina a duniya a kan AREWA24 ON DEMAND, ku shiga http://tv.arewa24.com ko ku sauke manhajar daga kan IOS App Store, ko Google Play, ko Apple TV, ko Roku Channel Store da kuma Amazon Fire TV.

Domin karin bayani, sai ku tuntubi: info@arewa24.com

Aljazeera Presents

Shiri ne da zai ke kawo muku labarai daban-daban daga kowanne sako na duniya domin tattaunawa, da ilimantarwa, sannan kuma da zaburarwa.

Scroll to top