Aljazeera Presents

Shiri ne da zai ke kawo muku labarai daban-daban daga kowanne sako na duniya domin tattaunawa, da ilimantarwa, sannan kuma da zaburarwa.

My Better World

Labari ne na wasu matasa ‘yan Afrika yayın da suke gaggwarmaya da kalubale daban-daban irin na makaranta, da na iyali, da kuma na abota.

Bino & Fino

Fino & Bino shirin yara mai ilimantarwa akan labarin Fino da Bino da kuma malam bude mana littafi mai ban al’ajabi yayın da suke koyun tarihi da al’adun nahiyar Afrika.

Buka Africana

Wata jajirtacciyar uwa, da ‘yarta da ba ta da gogayyar rayuwa da kuma ma’aikatanta masu juriyar da ajizanci, yayın da suke fuskantar kalubale tare.

Sirrin Boye

Shirine na wata yarinya mai suna Amira ‘yar shekaru 12 da ke da baiwar sani da fahimtar idan kwanan mutum ya zo karshe in ta hadu dashi.

Al Jazeera da AREWA24 sun yi hadin guiwa don fassara shirye-shirye na musamman da masu dogon zango zuwa harshen Hausa domin masu kallo sama da milyan 40 dake arewacin Nijeriya da kuma yankin Sahel

23 ga watan Nuwamba, 2021.  Doha/Lagos. Nan ba da jimawa ba masu kallon tashar AREWA24 sama da milyan 40 da ke Arewacin Najeriya, da kasashen  Nijar, da Chad da kuma Cameroon za su fara kallon shirye-shirye Al Jazeera na musamman da masu dogon zango na turanci, da aka fassarasu zuwa harshen Hausa, bisa wata sabuwar […]