CANAL+ INTERNATIONAL sun sanya tashar AREWA24 a jerin tashohinsu.

CANAL+ INTERNATIONAL ya cimma yarjejeniyarta da tashar nishadantarwa da tsarin rayuwa a Najeriya, wato AREWA24.
Tashar wadda aka bude a shekarar 2014 don haskakawa tare da fito da al’adun Hausawa, AREWA24 na isa ga masu kallo da ke magana da harshen Hausa sama da milyan 80 a yammacin Afirka.
Tashar AREWA24 na gabatar da shirye-shirye masu nishadantarwa da tsarin rayuwa da dama, iri daban-daban, Kama daga shirye-shiryen Gari Ya Waye da na Mata da Matasa da shiryeshiryen Hip Hop, da Fina-finan Kannywood da shirin “Kundin Kannywood” da Girke-Girke da kuma Shirn al’adu da shirye-shirye na musamman.

Haka kuma shirye-shiryen talabijin na tashar AREWA24 sun hada da shirye-shiryen kiwon lafiya, da shirin yara da kada-kaden gargajiya da kuma wasannin kwaikwayo daban-daban na kasashen Indiya da Turkiyya masu dogon zango, wadanda duk aka fassarasu cikin harshen Hausa. Tashar nishadantarwa a Najeriya, AREWA24 na nan a kan na’urar tauraron dan adam ta Canal+ kan tasha mai lamba 285, wadda zata fara daga yau. Don haka ne, wannan sanarwa ke kaddamar da bude sabon rukunin tashohin talabijin a kasar Nijar.

Kamfanin CANAL+INTERNATIONAL yana kokarin ganin ya kara matsowa kusa da abokan huldarsa na Najeriya, domin fitar da hanyar biya musu bukatunsu. “Muna farin ciki da muka samun damar fadada shirye-shirye masu inganci da muke samarwa. Tashar AREWA24 tasha ce da ta ke samar da shirye shirye masu inganci tun daga shekarar 2014.

A halin yanzu CANAL+INTERNATIONAL ta iso kasar Nijar kuma muna fata mu bawa masu basira a kasar damar kaiwa ga dukkanin kasashen dake magana da harshen Faransanci a nahiyar Afirka. Manufarmu ita ce tallata nasarorin da Najeriya ta samu da kuma kulla wata alaka tsakanin bangarori daban-daban na nahiyar Afirka.” A cewar Cheikh Sarr, Babban Jami’in Canal + ta kasar Niger. “Mun yi farin cikin samun hadin guiwa da CANAL + INTERNATIONAL wajen nuna shirye-shirye masu inganci da harshen Hausa ga abokan huldarsu. Muna da tabbacin cewa shirye-sjiryenmu za su zaburar tare da nishadantar da sabbin masu kallonmu a kan CANAL + a kasar Nijar kamar yadda suke yi a tsawon shekaru biyar da suka wuce a Najeriya.” A cewar Celestine Umeibe, Shugaban sashen tallace-tallace na tashar AREWA24.

Game da AREWA24 : Za a iya sauke shirye-shiryen tashar AREWA24 a kowanne mako a kan youtube.com/AREWA24channel. Ku kasance da masu kallon tashar AREWA24 da ke k kafafen sada zumunta a kan: AREWA24.com, da https://facebook.com/AREWA24, da Instagram.com/AREWA24channel, da kuma twitter.com/AREWA24channel.

About the Author
A Website Developer and Digital Content Creator, CloudOps Engineer, Web Developer & Tech Community Lead
Scroll to top