CANAL+ INTERNATIONAL ya cimma yarjejeniyarta da tashar nishadantarwa da tsarin rayuwa a Najeriya, wato AREWA24.
Tashar wadda aka bude a shekarar 2014 don haskakawa tare da fito da al’adun Hausawa, AREWA24 na isa ga masu kallo da ke magana da harshen Hausa sama da milyan 80 a yammacin Afirka.
Tashar AREWA24 na gabatar da shirye-shirye masu nishadantarwa da tsarin rayuwa da dama, iri daban-daban, Kama daga shirye-shiryen Gari Ya Waye da na Mata da Matasa da shiryeshiryen Hip Hop, da Fina-finan Kannywood da shirin “Kundin Kannywood” da Girke-Girke da kuma Shirn al’adu da shirye-shirye na musamman.
Haka kuma shirye-shiryen talabijin na tashar AREWA24 sun hada da shirye-shiryen kiwon lafiya, da shirin yara da kada-kaden gargajiya da kuma wasannin kwaikwayo daban-daban na kasashen Indiya da Turkiyya masu dogon zango, wadanda duk aka fassarasu cikin harshen Hausa. Tashar nishadantarwa a Najeriya, AREWA24 na nan a kan na’urar tauraron dan adam ta Canal+ kan tasha mai lamba 285, wadda zata fara daga yau. Don haka ne, wannan sanarwa ke kaddamar da bude sabon rukunin tashohin talabijin a kasar Nijar.
Kamfanin CANAL+INTERNATIONAL yana kokarin ganin ya kara matsowa kusa da abokan huldarsa na Najeriya, domin fitar da hanyar biya musu bukatunsu. “Muna farin ciki da muka samun damar fadada shirye-shirye masu inganci da muke samarwa. Tashar AREWA24 tasha ce da ta ke samar da shirye shirye masu inganci tun daga shekarar 2014.
A halin yanzu CANAL+INTERNATIONAL ta iso kasar Nijar kuma muna fata mu bawa masu basira a kasar damar kaiwa ga dukkanin kasashen dake magana da harshen Faransanci a nahiyar Afirka. Manufarmu ita ce tallata nasarorin da Najeriya ta samu da kuma kulla wata alaka tsakanin bangarori daban-daban na nahiyar Afirka.” A cewar Cheikh Sarr, Babban Jami’in Canal + ta kasar Niger. “Mun yi farin cikin samun hadin guiwa da CANAL + INTERNATIONAL wajen nuna shirye-shirye masu inganci da harshen Hausa ga abokan huldarsu. Muna da tabbacin cewa shirye-sjiryenmu za su zaburar tare da nishadantar da sabbin masu kallonmu a kan CANAL + a kasar Nijar kamar yadda suke yi a tsawon shekaru biyar da suka wuce a Najeriya.” A cewar Celestine Umeibe, Shugaban sashen tallace-tallace na tashar AREWA24.
Game da AREWA24 : Za a iya sauke shirye-shiryen tashar AREWA24 a kowanne mako a kan youtube.com/AREWA24channel. Ku kasance da masu kallon tashar AREWA24 da ke k kafafen sada zumunta a kan: AREWA24.com, da https://facebook.com/AREWA24, da Instagram.com/AREWA24channel, da kuma twitter.com/AREWA24channel.
You Might also like
-
AREWA24 na bikin cikarta shekaru shida tare da gabatar da sababbin shirye-shirye
Tashar AREWA24, Tashar talabijin ta Hausa dake kan gaba wajen samar shirye-shirye masu nishadntarwa da nuna tsarin iyali, wadda ke da dakin daukar shirye-shirye a Najeriya dake Yammacin Nahiyar Afirka, tana sanar da wani sabon jadawalin shirye-shirye da kuma kayatattun shirye-shirye domin su dace da bukin cika shekaru shida da kafuwar wannan tasha.
-
AREWA24 ta kaddamar da sabon jadawalin shirye-shiryenta na zango
Tashar AREWA24, tashar Hausa da ke kan gaba wajen nishadantarwa da tsarin rayuwa a Najeriya, tana sanar da fitowar jadawalin sabbin shirye-shiryenta na zango na hudu a wannan shekara da kuma zangon farko na shekarar 2019, wanda ya kunshi sabon wasan kwaikwayon tashar da aka dade ana jira, wanda zai zo a watan Janairu, kari a kan wasan kwaikwayon “Dadin Kowa” da tashar ke nunawa a halin yanzu wanda ta dade tana nunawa wanda kuma ya samu lambar yabo. A halin yanzu ana nan ana shirya wannan sabon wasan kwaikwayo mai kayatarwa, kuma ana tsammanin zai kawo wani sabon sauyi da inganci a bangaren shirye-shiryen talabijin da harshen Hausa.
Sabon jadawalin shirye-shiryen tashar AREWA24 da zai fara a watan Oktoba, ya kunshi shirin “Amo daga Arewa”. Wannan shiri na kade-kade ya kunshi gabatar da wakoki kai tsaye da tattaunawa da fasihan mawaka daga fadin Arewacin Najeriya, da suka hada da mawakan gargajiya da na R&B da masu wakokin sanyaya ruhi da kuma mawakan addinai. Shirin “Amo Daga Arewa” ya tattara kada-kaden gargajiya na al’ada da dama da yankin Arewacin Najeriya ke da su, kari a kan shahararrun shirye-shiryen AREWA24 na
Hip Hop.
A zangon na hudu , shirin nan na “Matasa@360” zai sake dawowa da wani sabon salo da kuma sabbin masu gabatarwa. Shirin na “Matasa@360” shiri ne na matasa da yayi daidai da zamani kuma yake bi lungu da sako, tare da mayar da hankali a kan basira da kirkira da kuma fasahar matasan Arewacin Najeriya.
Haka kuma shirin zai dinga tattauna kalubale na zahiri da matasan yankin ke fuskanta da kuma wahalhalun da suke fama da su a yau da kullum. Bangarorin da shirin ya kunsa za su nuna yadda matasan Arewacin Najeriya ke rayuwarsu ta yau da kullum, da alakarsu da sauran mutane, da kafafen yada labarai, da sana’o’i, da wasanni, da al’amuran yau da kullum, da rayuwar makaranta, da fasaha da sauran bangarorin da matasa daga dukkan fadin duniya ke da alaka da su.Haka kuma tashar AREWA24 za ta fara gabatar da shirin “Haske: Matan Arewa” kashi na hudu, wanda jajirtattun mata daga Arewacin Najeriya ke bayyana labarinsu cike da kwarin guiwa. Suke kuma bijirewa wasu dabi’u na zamantakewa da al’adu don su zamo shugabanni, ko yan kasuwa, ko masu sana’o’i, ko masu wayar da kai a yankunan karkara, ko masu shirya fina-finai da sauransu, Wadannan hazikan mata kan bayyana ci gabansu, da fadi-tashinsu, da matsalolin da suke fuskanta, da kuma nasarorinsu.
Cikon sabbin shirye-shiryen da tashar AREWA24 za ta gabatar a zango na hudu a wannan shekarar su ne sabbin fitattun fina-finan Kannywood daga kwararrun daraktocin masana’antar. A yanzu tashar AREWA24 ta yi fintinkau ga kowacce tasha dake yankin Arewa, idan ana magana a kan nuna fitattun fina-finan Kannywood.Sannan kuma tashar ta samar da shirye-shirye don manyan gobe da ke kallon shahararrun shirye-shiryen yara a tashar safe da yamma.
Haka kuma tashar tana sanar da daukar manyan kuma kwararrun ma’aikatan shirye-shirye da ta yi a dakin shirye-shiryenta da ke Kano: wato Kadiri Yusef da Evans Ejiogu, wadanda kowannensu ya zo da irin kwarewar da ya dade yana samu da irin shuhurar da ya yi a fagen shirin talabijin da kafafen yada labarai a Lagas, zuwa kano.
Kadiri Yusef dai wani babban ma’aikacin shirye-shirye ne a gidan talabijin na Silverbird Television, inda ya yi aiki tun daga shekarar 2004 zuwa 2017. Kadiri ya zamo shugaban sashen shirye-shirye na tashar Silverbird Television a shekarar 2006 inda ya bada umarni a manyan shirye-shiryen Silverbird da suka ciri tuta, da kuma dukkanin shirye-shiryenta na kai-tsaye. A tashar AREWA24, shi ne mai kula da bangaren bada umarni da tsara dukkanin shirye-shirye daban-daban da ake gabatarwa a dakin shirye-shirye.
Evans Ejiogu ya kasance kwararren mai samar da shirye-shiryen talabijin, mai shiryawa, mai bada umarni, marubuci sannan kuma mai tace hotunan bidiyo. Baya ga wannan gogewa da kwarewa a fagen daukacin nau’ikan shirye-shirye da yake da su, Evans ya kawowa tashar AREWA24 dabarun kasuwanci da ya samu a tsawon shekarun da ya shafe a fagen sadarwa da tallace-tallace. Evans yayi aiki a babban dakin gabatar da shirye-shirye , da wasan kwaikwayo na talabijin, da gajerun fina-finai, da tallace-tallace, da gidan radiyo da kuma shafukan yanar gizo, inda yake taimakawa wajen kawo babban matakin kwarewa da inganta shirye-shirye a tashar AREWA24.Babban Shugaban tashar AREWA24 Jacob Arback ya bayyana cewa, “Mun yi gagarumar sa’ar samun manyan ma’aikata da ke da irin wannan kwarewa da gogewar aiki don yin aiki a tashar AREWA24. Evans da Kadiri ba su tsaya iya bada gudunmawa ga jajirtattun ma’aikatanmu na shirye-shirye da suka tarar da kuma daga darajar shirye-shiryen tashar ba, suna kuma taimakawa wajen bunkasa bangaren aiyukan talabijin da kafafen yada labarai na Arewaci Najeriya.”
GAME DA TASHAR AREWA24: An kafa Tashar AREWA24 a shekarar 2014 domin cike wawakeken gibin da ake da shi a fagen shirye-shiryen nishadi da tsarin rayuwa da ake shiryawa da harshen hausa, wadanda ke nuni da abubuwan da ake alfahari da su a rayuwar Arewacin Najeriya, da al’adu, da kadekade, da fina-finai, da fasaha, da girke-girke da kuma wasanni. A yau, mutane masu Magana da harshen hausa sama da milyan 80 a Najeriya da kuma yammacin Afirka ne ke lallon tashar AREWA24 ta tauraron dan dan’adam na Eutelsat kyauta, haka kuma, a Najeriya ana kallon tashar akan StarTimes da ake biya (tasha mai lamba 138), da kuma kafar tauraron dan’adam ta StarTimes DTH (tasha mai lamba 538) sannan da kafafen tauraron dan’adam na kamfanin Multichoice guda biyu da ake biya, wato DSTV (tasha mai lamba 261) da kuma Gotv (tasha mai lamba 101).
Haka kuma ana dora ingantattun shirye-shiryen tashar AREWA24 kowanne mako a shafin youtube.com/AREWA24channel, sannan tashar na amfana da masu kasancewa da ita a shafukanta na AREWA24.com, da facebook.com/AREWA24, da Instagram.com/AREWA24channel, da kuma na twitter.com/AREWA24channel. Domin karin bayani sai ku tuntubi: info@arewa24.com
Post Views: 10,713 -
Gangamin Wayar da kai na AREWA24 a watan October: Sauya rayuwa da tattauna ƙalubale game da cutar Sikila.
By Musa Abdullahi Sufi
Cutar sikila, matsala ce da ta addabi duniya, da miliyoyin mutane ke fama da ita a faɗin duniya. Kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta bayyana, kimanin yara dubu 300 ake haihuwa da cutar sikila a kowacce shekara, kuma mafi yawa an fi samun masu cutar a yankin Sahara na Afirka.
A Najeriya kaɗai, kimanin yara dubu 150 ake haihuwa da wannan cuta a kowacce shekara, wadda hakan ya sa ta zamo kasar da wannan cuta ta fi addaba a faɗin duniya. Yankin Arewacin Najeriya shi ne ya fi ɗaukar kaso mafi yawa, da kimanin kaso 20-30 cikin ɗari na yawan al’ummar da ke ɗauke da gadon cutar a jininsu.
Sikila na ci gaba da kasancewa wata matsananciyar matsala a Najeriya, wadda miliyoyin mutane ke fama da ita, musamman a cikin al’ummar da ke magana da Harshen Hausa. Domin daƙile wannan matsala, AREWA24, tashar talabijin ta Hausa da ke kan tauraron ɗan’adam mafi girma, ta ɗauki wani gagarumin shirin wayar da kai da kuma ilimantar da ɗaukacin masu kallonta, ta yin wani gangamin wayar da kai na tsawon wata guda da ta ware domin tattauna batun da ya shafi cutar ta sikila.
A tsawon watan Oktoba, AREWA24 ta mayar da hankali wajen nuna jerin shirye-shirye domin wayar da kai game da cutar sikila. Baƙi na musamman sun haɗa da likitoci, ma’aikatan jinya, masu larurar sikila, iyaye, shugabannin addinai, wakilan gwamnati, da kuma kwararru a harkar lafiya da sauransu, waɗanda za su kasance a cikin sanannun shirye-shirye daban-daban domin tattauna haƙiƙanin yadda rayuwa da cutar sikita take, da kuma mahimmancin gano cutar da wuri da kulawar da ta dace.
Wannan gangamin wayar da kai, yunƙuri ne na kawo sauyi a rayuwa, kasancewar miliyoyin masu magana da harshen Hausa a fadin duniya za su samu ilimi mai mahimmanci bisa yadda za a kaucewa cutar da kuma yadda za a kula da wannan larura da ake gado a cikin jini. Yawan masu fama da cutar a wannan yanki yana da alaƙa ne da ƙarancin kayan aikin kula da lafiya, da ƙarancin wayar da kai, da kuma ƙalubalen al’adu, waɗanda suka sa yake da mahimmaci a yaƙi wannan cuta ta hanyar wayar da kai, kamar irin wannan Gangamin wayar da kai na AREWA24 a watan Oktoba.
Wannan gangamin wayar da kai, za a yi shi ne domin wayar da kan al’umma, da samar musu bayanai na ceton rai, da fito da yadda za a yi gawaje-gwaje da kuma dabarun da za yi amfani da su da wuri wajen rage tasirin cutar ta sikila a Arewacin Najeriya.
Ilimantar da Miliyoyin al’umma: Gangamin wayar da kai na AREWA24 domin ceton rai, wani aiki ne da zai kawo sauyi a yaƙin da ake yi da larurar ta sikila. Yawan al’ummar da wannan tasha ke kaiwa garesu, yana tabbatar da cewa miliyoyin mutane, a Najeriya da ma fadin duniya, za su ilimantu game da mahimmancin da ke akwai game da buƙatar yin gwaji kafin aure. Iyalai da dama da suke fama da larurar sikila ba su da wayewar kai game da mahimmancin gwaji kafin aure domin kaucewa yaɗuwar cutar.
Wannan gangamin wayar da kai, zai cike wannan giɓin, ya kuma bawa masu kallo ilimin da zai taimaka musu wajen yanke hukuncin da zai iya ceto ‘ya’yan da za a haifa a nan gaba daga ƙalubalen da ke da alaƙa da cutar.
Bugu da ƙari, shirye-shiryen AREWA24 za su samar da mahimman bayanai a kan yadda za a kula da waɗanda ke fama da cutar ta sikila. Kasancewar kwararru a harkar lafiya cikin shirye-shirye, kamar Gari Ya waye, da Mata A Yau, zai tabbatar da cewa masu kallo sun ilimantu dangane da tallafin da ake buƙata ta fuskar kiwon lafiya da damuwar masu cutar, domin kyautatwar ingancin rayuwar masu ɗauke da cutar ta sikila.
Kama daga raɗadin da suke fuskanta lokaci bayan lokaci, zuwa fahimtar mahimmancin duba lafiyarsu akai-akai, waɗannan shirye-shirye za su gabatar da shawarwari a aikace waɗanda za su iya kawo tabbataccen sauyi a rayuwar mutane.
Faɗakar da al’ummu ta hanyar shawarar ƙwararru: Abin da ya sa wannan gangamin wayar da kai ya zamo na musamman shi ne, shigo da baƙi daban-daban cikin wannan shiri. Kama daga likitoci da ma’aikatan jinya da za su dinga bada shawarwari na kiwon lafiya ga masu ɗauke da cutar ta sikila da kuma iyalansu, suna masu bayyana abubuwan da suka fuskanta.Gangamin zai yi duba a kowanne ɓangare na haƙiƙanin yadda rayuwa da cutar sikila take.
Shugabannin addinai suma suna taka wata mahimmiyar rawa wajen wayar da kai, ta hanyar ƙarfafa mahimmancin kula da lafiya da kuma alhakin da ke kan al’umma wajen tabbatar da lafiya da kuma jin dadin yaran da za a haifa a nan gaba ta hanyar yin gwaji kafin aure.
Kwararru a harkar lafiya da kuma wakilan gwamnati za su ƙarawa shirin armashi ta hanyar bayar da ƙarin haske a kan irin ƙalubalen da ake da shi wajen shawo kan cutar sikila da kuma haska dokoki da shirye-shiryen da aka yi domin inganta hanyoyin samun kiwon lafiya.
Wannan gangami na wayar da kai bai tsaya iya wayar da kai ba kawai, zai kuma yi wkira domin a samar da tsarin kula da lafiya kyauta ga wadanda cutar ta sikila ta shafa, wanda wani babban mataki ne na magance matsalar tattalin arziki da zamantakewa da wasu majinyatan da dama ke fama da ita wajen neman magani.
Wannan wani mahimmin mataki ne na kawo ƙarshen yaɗuwar cutar sikila: Mahimmancin wayar da kai game da cutar sikila ba zai misaltu ba. A sassan Najeriya, musamman Arewa, har yanzu akwai ƙarancin fahimtar wannan cuta, wanda ke kaiwa ga yaɗuwar bayanai na ƙarya da nuna ƙyama.
Iyali da dama ba su san wajabcin neman shawarwari dangane da gadon kwayoyin halitta da kuma gwaji kafin aure ba, wanda hakan zai yi matuƙar rage yaɗuwar wannan cuta.
Gangamin wayar da kai na AREWA24 wani mahimmin taimako ne, kasancewar kai tsaye yana cike gibi ta fuskar ilimi da kuma samar da wata farfajiya don tattaunawa ta gaskiya kuma a bayyane game da cutar sikila.
Ta hanyar aiwatar da wannan gangamin ilimantarwa kyauta, AREWA24 tana yiwa al’umma hidima ne. Ƙoƙarin tashar game da harkokin kiwon lafiya, musamman a bangarorin da ba a fiya basu mahimmanci ba, yana nuna irin sadaukarwarta wajen sauke nauyin al’umma da kuma kyautata rayuwarsu. Yayin da Jaruman majinyatan da ke fama da cutar sikila da iyalansu ke amfana da wannan gangami, abu ne a zahiri cewa wannan gangami zai yi tasiri sosai a rayuwar milyoyin mutane.
Labarun jaruman da ke fama da cutar sikila, da shawarwarin kwararru daga likitoci, da kuma samun kwarin guiwa daga shugabannin addninai, duk za su hadu su samar da wani gagarumin saƙo da zai ceto rayuka.
Ƙari a kan wayar da kai, wannan gangami zai kuma zaburar da al’umma domin ɗaukar mataki. Baƙin, za su tattauna game da shirye-shiryen da suke gudana a yanzu haka, waɗanda aka tsara su domin samar da tsarin kula da lafiya kyauta ga majinyata masu larurar sikila, wanda zai ci gaba da ƙarfafar rawar da AREWA24 ta taka a matsayin wadda ta kawo sauyi mai amfani. Wannan shiri yana nufin ceto rayuka, da kyautata rayuwa ga jaruman da ke fama da cutar ta sikila, da kuma kare yaran da za a haifa a nan gaba daga fukantar irin wannan ƙalubale.
Rufewa: Wani shiri gangami wayar da kai a watan Oktoba na AREWA24 domin Jarumai masu larurar sikila, wani gagarumin aiki ne a yaƙin da ake yi da cutar sikila. Ta hanyar hada kwararru a harkar lafiya, da shugabannin al’umma, da kuma iyalan da abin da ya shafa, ba iya wayar da kai kaɗai tashar ke yi ba, bar ma da sauya rayuwar al’umma.
Jaruman da ke fama da cutar ta sikila da kuma iyalansu suna matuƙar godiya da wannan shiri, wanda zai basu fata, ya kuma ƙarfafesu ta inda aka fi buƙatar hakan.
Wannan gangamin wayar da kai na tsawon wata guda, wata shaida ce da ke nuna jajircewar da AREWA24 ke yi wajen amfani da tashar don yin abin alkhairi. Kada masu kallo su bari wannan dama ta musamman ta koyon ilimi, da tattaunawa, da kuma ɗaukar mataki a kan yaƙi da cutar sikila ta wuce su. Ta hanyar ilimantarwa da wayar da kai, duk za mu iya bayar da gudunmawa wajen ceto rayuka da kuma gina al’umma mai cike da ƙoshin lafiya.
Post Views: 582