Wasan Kwaikwayo

Gidan Badamasi

Gidan Badamasi sabon fim din wasan barkwanci ne da ake dauki-ba-dadi a tsakanin wasu irin ‘ya’ya masu kunnen kashi da mahaifinsu Alhaji Badamasi.

Ubongo Kids

Ubongo Kids Shiri ne na zane na koyan ilimi wanda aka shirya a kasar Tanzania. Shiri ne da zai taimakawa yara wajen koyo cikin nishadi.

Kyautata Rayuwa

Wasan Kwaikwayo ne mai dogon zango wanda ke bayyana matsaltsalun da iyalai ke fuskanta, da kuma yawan sake-saken aure

Khalimullah

Shirin kissar Annabi Musa (Amincin Allah su Tabbata a gare shi) wanda zai nuna al’amuran da suka wakana kafin haihuwarsa da rayuwarsa.

Khalilullah

Shirin Kissar Annabi Ibrahim, tare da Annabawan na wannan zamani wanda ya hada da Annabi Isma’il da Annabi Is’haq da Annabi Ya’akub.

Habibullah

Shiri ne domin yara, wanda ke nuni da tarihin Rayuwar Annabi Muhammad, Amincin Allah da Albarka da Salama su kara tabbata a gare shi.

Agent Raghav

Agent Raghav, Jami’in Bincike ne na ban mamaki da ke aiki a Fittacciyar Hukumar Bincike ta CBI dake Kasar India.

Dadin Kowa

Wasan kwaikwayo na asali mai farin jini da AREWA24 ta shirya, inda ya kawo labarin Dadin Kowa, wani kirkirarren gari.

Tarkon Kauna

Wannan fitaccen wasan Kwaikwayo na tsawon sa’a guda, shiri ne da ya maida da hankali a kan labarin Omer da Zehra.

Sapne Suhane

Wannan labarin gwagwarmayar wasu matasan masoya ne dake kaunar juna duk da matsin lambar da suke fuskanta daga wurin Iyayensu.

Scroll to top