Tashar AREWA24 Tana Sanar Da Kaddamar Da Sabon Sashen Wasannin Kwaikwayo Da Fina-Finai Da take Shiryawa

AREWA24, tashar talabijin da ke kan gaba wajen yada shirye-shiryen nishadantar da iyali da tsarin rayuwa, wadda ke da ofishin daukar shirye-shiryenta a Najeriya a Yammacin Afirka, tana sanar da kaddamar da sabon sashen wasannin kwaikwayo da fina-finan da take shiryawa. Sabon sashen shirye-shiryen kamfanin zai samar da rubutun labaru da kuma shirya sabon jadawalin […]
Kwana Casa’in
Wasan kwaikwayo ne da aka gina shi a kan tarka-tirkar siyasa da cin hanci da rashawa. Labarin yana faruwa ne a wani kirkirarren gari mai suna Alfawa.
Tauraron Kwallon kafa

Shirine domin fitattun jaruman wasannin kwallon kaf ana duniya, irin rawan da suka taka da kuma gudun mawar da suke badawa.
Against The Odds

Shiri ne da yake nuna masu was an motsa jiki na bangare daban daban kama daga kwallon kafa, kwallon Kwando , hockey.
Dan Birni

Shrin Dan Birni an dora alhakin wata annoba a kan mai maganin gargajiya, sannan aka yiwa matarsa barazana
Kaddarar Rayuwa

Kaddarar Rayuwa wani shirin wasan kwaikwayo ne a kan yadda kaddara ta yi tasiri a rayuwar wasu ‘yanmata biyu ‘yan’uwan juna.
The 77 Percent

Shirine da ya kunshi labaru da fashin baki daga wannan nahiya game da batutuwan da a ka fi damuwa dasu.
Goge Africa

Shirin Goge Africa shiri ne da yake duba a kan mahimman al’adu nahiyar Afirka ta hanyar yin tafiye-tafiye,
Akili and Me

Akili and Me – Shirin ilimi na matakin farko da ke koyar da yara ilimi lissafi matakin farko da turanci a matsayin harshe na biyu
Yusuf – Nabiyillah

Yusuf – Nabiyillah Shirin tarihin Annabi Yusuf domin yara wanda tashar AREWA24 ta fassarashi cikin harshen Hausa