AREWA24 ta bayyana a dikodar StarTimes

Kamfanin Startimes da ke yada tashoshin talabijin na tauraron dan Adam, ya sanar da sanya fitacciyar tashar nan ta harshen Hausa wato AREWA24 cikin jerin tashoshin da ke kan
dikodarsu, a wani yunkuri da tashar ke yi na ganin ta biya bukatun dinbun mutanen da ke kallonta. A ta bakin Daraktan kasuwanci na tashar, Qasim Elegbede ya bayyana cewa “bukatar samar da karin tashoshin talabijin na harshen Hausa ta ci gaba da hauhawa a tsakanin masu kallo musamman ma a arewacin Najeriya a shekarar da ta gabata. Kasancewar mu na sauraron bukatun al’umma, mu na kokari ne mu ga mun bawa masu kallonmu hakikanin abin da su ke bukata, da karin shirye-shirye masu nishadantarwa.”

Shi ma da ya ke bayani game da wannan ci gaba da aka samu, shugaban sashen gudanar da tallace tallace na tashar AREWA24, Celestine Umeibe, ya yi nuni da cewa “hakika hadin guiwa tsakanin AREWA24 da kamfanin Startimes wani ci gaba ne da ake bukata. A yanzu mutane da dama masu magana da harshen hausa a Arewacin Najeriya da ma sauran sassan kasar zasu samu damar kallon shirye-shiryen tsarin rayuwa da nishadantarwa dake nuni da al’adu daban-daban da ake alfahari da su a Arewacin Najeriya akan wannan tasha da ke kan tsarin biya.”

Ya kuma kara da cewa “A halin yanzu masu tallace-tallace da kamfanoninsu zasu iya kaiwa ga dukkanin mutanen da suke so su tallata musu hajarsu ta hanyar amfani da tashar AREWA24 wadda a yanzu take cikin dukkanin tsarikan da ke kan dikodar Startimes.”

Tashar Arewa 24 na nuna shirye-shiryen na nishadi da al’adu da kuma addinai cikin harshen hausa wadanda take yadawa akan tasha ta 138 akan Dikodar Startimes. Idan za a iya tunawa a wataan Disanmbar shekarar 2017 ne, Kamfanin Startimes ya sanar da fara nuna tashoshinsa a Maiduguri babban birnin Jahar Borno a wani gagarumin yunkuri da yake yi domin cika alkawarin da ya dauka na samar da shirye-shirye masu nishadantarwa cikin sauki a kowanne gida a Najeriya..

About the Author
A Website Developer and Digital Content Creator, CloudOps Engineer, Web Developer & Tech Community Lead
Scroll to top