AREWA24 Na Cigaba Da Bunkasa Zuwa Ga Masu Magana Da Harshen Hausa Da Ke Ko Ina A Fadin Duniya

Tashar AREWA24, tasha ta Hausa da ke kan gaba a fagen nishadi da tsarin rayuwa a Najeriya da kuma yanmacin Afirka na sanar da kaddamar da “AREWA24 ON DEMAND,” wata sabuwar manhaja ta nuna shirye-shiryenta da ake kira subscription video-on-demand (“SVOD”) da “Over-the-Top” (OTT) a turance. A yanzu dukkanin masu magana da harshen Hausa da Iyalansu dake zaune a ko ina a fadin duniya, za su samu damar more kallon shirye-shiryen daban-daban da suka lashe lambar yabo, wadanda al’ummar Najeriya da na yammacin nahiyar afirka ke jin dadin kallonsu yau da kullum a kan tashar AREWA24 da ke nuna shirye-shiryenta a tsawon sa’o’i 24 a ranakun mako.

Shugaban tashar AREWA24, Jacob Arback, ya bayyana wannan sabuwar manhaja da cewa, wata hanya ce ta fadada hanyoyin yada shirye-shiryensu domin kaiwa ga dukkannin masu magana da harshen Hausa da ke fadin duniya. Ya ce “Sanya masu kallo su ji kamar suna gida da kuma jin suna alfahari da al’adunsu na gargajiya shi ne babban makasudin samar da wannan sabuwar manhaja ta AREWA24 ON DEMAND da ma tashar AREWA24 baki daya. A yanzu, masu kallonmu za su iya more kallon shirye-shieryen da suka yi fice, wadanda ke da alaka da garuruwansu, suke kuma nishadantar da iyali da masu magana da harshen Hausa a ko ina su, ta amfani da wannan sabuwar manhaja. Musamman ma yadda muke nuna al’adu na alfahari da kuma sanya Iyalan Hausawa da suke kasasen waje su ji kamar suna gida Najeriya ko kasashen Yammacin nahiyar Afirka.”

Arback ya kara da cewa, “za a kaddamar da manhajar AREWA24 ON DEMAND da dinbun shirye-shirye na musamman. “Muna shirya shirye-shirye da dama da suka shafi abubuwa daban-daban da salo daban-daban a kowacce rana a dakunan shirye-shiryenmu da ke garin Kano a Najeriya, wadanda suka hada da shararrun wasannin kwaikwayonmu masu dogon zango, wato “Kwana 90” da kuma “Dadin Kowa.” Haka kuma, muna fassara shirye-shiryen sassan fadin duniya da na yankin nahiyar Afirka da dama zuwa harshen Hausa dakunan daukar shirye-shiryenmu guda uku da muke da su, wadanda dukkaninsu za su kasance a kan wannan sabuwar manhaja.”

Sabuwar manhajar AREWA24 ON DEMAND SVOD za ta bada damar samun dukkanin shirye-shiryen tashar AREWA24 da kuma taskar ajiye shirye-shirye na harshen Hausa, wadda ita ce taskar shirye-shirye na harshen Hausa mafi girma a duniya. Baya ga wasannin kwaikwayo masu dogon zango da tashar ke shiryawa, sabuwar manhajar ta AREWA24 ON DEMAND za ta dinga kunsar sabbin shirye-shirye a kowacce rana, da suka hada da sabbin wasannin kwaikwayo na masana’antar Kannywood, da kuma shirye-shiryen Hausa Hip Hop, da na girke-girke, da shirye-shiryen da tashar ke kawo a kullum wato Gari ya waye, da shirye-shiryen wasanni, da na al’adu da shirin Bayan fagen fina-finan Kannywood, da shirye-shiryen mata da matasa da kuma yara, da ma wasu da dama. Manhajar AREWA24 ON DEMAND tana karkashin gudanarwar gudanar fasahar kanfanonin Vimeo’s state-of-the-art SVOD da kuma OTT technologies. Kamfanin Vimeo ne ke samar da dabaru masu inganci domin masu gudanar da ayyukansu ta yanar gizo su bawa abokan huldarsu damar kulla alaka da su a dukkanin manyan manhajoji da kuma na’urorin amfani da yanar gizo.

“Muna alfahari da damar da kamfanin fasahar Vimeo’s best-in-class OTT technology ya bamu, na kaiwa ga abokan hulda ba tare da wata sarkakiya ba, da kuma bada ingantacen yanayi ga tashar AREWA24 da kuma masoyanta,“a ta bakin Kathleen Barrett, SVP, Enterprise, na kamfanin fasahar Vimeo. “A yanzu masu kallo za su iya amfani da kuma morewa kallon sabuwar manhajar kallon shirye-shiryen harshen Hausa ta farko a manhajar da ake kira SVOD service a turance.”

Domin amfani da sabuwar manhajar AREWA24 ON DEMAND wato SVOD service, sai ku ziyarci adreshin yanar gizo http://tv.arewa24.com ko kuma ku sauke manhajar a kan wayoyinku daga kafofin IOS App Store, da Google Play, da Apple TV, da Roku Channel Store da kuma Amazon Fire TV.

GAME DA MANHAJAR AREWA24 ON DEMAND: Manhajar AREWA24 ON DEMAND, wani bangare ne na kamfanin Network AREWA24, Ltd, manhaja ce kallon dukkanin shirye-shiryen harshen Hausa da ake kira all-Hausa language global streaming da kuma OTT service a turance, da nufin yada al’adu na alfahari ga masu magana da harshen Hausa a fadin duniya. An kaddamar da wannan manhaja da kimanin sama da shirye-shirye 2,000 da suka shafi abubuwa daban-daban da salo daban-daban da suke da farin jini a Najeriya da kuma Yammacin nahiyar Afirka, wadanda suka hada da wasannin kwaikwayo masu dogon zango da tashar ke shiryawa, da sabbin wasannin kwaikwayo na masana’antar Kannywood, da hirarraki da shirye-shiryen mata da na Hip Hop da na matasa da kuma yara da shirin girke-girke, da na al’adu da ma wasu da dama.

GAME DA TASHAR AREWA24: Tahsar AREWA24 da shirye-shiryenta, An kafa Tashar AREWA24 a shekarar 2014 domin cike wawakeken gibin da ake da shi a fagen shirye-shiryen nishadi da tsarin rayuwa da ake shiryawa da harshen hausa, wadanda ke nuni da abubuwan da ake alfahari da su a rayuwar Arewacin Najeriya, da al’adu, da kade-kade, da fina-finai, da fasaha, da girke-girke da kuma

wasanni. A yau, tashar AREWA24 ta kai ga mutane milyan 38 masu magana da harshen Hausa a Najeriya da kuma yammacin nahiyar Afirka a kan tauraron dan dan’adam na Eutelsat da ake kallo kyauta, da kuma kan tauraron dan adam na StarTimes da ake biya (tasha mai lamba 138), da kafafen tauraron dan’adam na kamfanin Multichoice guda biyu da ake biya, wato DSTV (tasha mai lamba 261) da kuma Gotv (tasha mai lamba 101), da kuma tauraron dan adam na Canal+ payTV service (tasha mai lamba #285) a Jamhuriyar Niger, da Chad da kuma Cameroun. AREWA24 na amfana da masu kallo da ke kasancewa da dukkanin shafukanta na AREWA24.com, facebook.com/AREWA24, Instagram.com/AREWA24channel, and twitter.com/AREWA24channel.

Domin karin bayani sai ku tuntubi: info@arewa24.com

About the Author
A Website Developer and Digital Content Creator, CloudOps Engineer, Web Developer & Tech Community Lead
Scroll to top