AREWA24 na sanar da sabon jadawalin shirye-shirye na wasannin kwaikwayo da take shiryawa, da fina-finai, da shirye-shiryenta na cikin gida a yayin da kamfanin ke cika shekaru 10 da kafuwa

AREWA24, tashar talabijin da ke kan gaba wajen yaɗa shirye-shirye masu nishaɗantar da iyali da tsarin rayuwa cikin harshen Hausa, wadda ke da ofishin samar da shirye-shirye a Najeriya da yammacin Afirka, tana sanar da wani gagarumin sabon jadawali na shirye-shirye, da fina-finai da wasannin kwaikwayo da take shiryawa da kuma karɓar wasannin kwaikwayo na Hausa masu dogon zango domin nuna su a mahajarta ta kallo kai tsaye, wato AREWA24 On Demand.

Domin bukin murnar cikar AREWA24 shekaru 10, tashar ta kaddamar da sabon shirinta na matasa, wato, “Arewa Gen-Z,” wanda aka shirya domin matasan Arewacin Najeriya masu ɗinbin yawa. Matasa ne ke shirya wa, kuma gabatar da shirin “Arewa Gen-Z”, wanda ke mayar da hamkali a kan irin ƙalubalen da a yanzu matasa ke fama da shi kowacce rana. Shirin na mintuna 30 da ake gabatarwa a kowanne mako, zai dinga kawo labarun nasarori, da fasaha, da waƙe-waƙe, da kuma al’adun matasa. Shirin zai kasance wata farfajiya domin abubuwan da aka san matasa da shi domin jawo hankalin matasa a faɗin Arewacin Najeriya.

Haka kuma nan ba da daɗewa ba AREWA24 za ta fito da fim ɗinta na farko mai gajeren zango, mai sunan, “The Jaru Road,” wani labari mai ƙayatarwa kuma na asalin Arewacin Najeriya, wanda aka shirya da harshen Turanci, kuma domin masu kallo dake fadin Afirka da ma sauran sassa na duniya. Kamfanin ya tsara shirya ƙarin wasu fina-finai huɗu a 2024 – 2025, wasu da harshen Hausa domin masu kallo a Najeriya da kuma Yammacin Afirka, wasu kuma da harshen Turanci domin masu kallo a dukkanin faɗin Afirka da duniya baki ɗaya. Bugu da ƙari, AREWA24 za ta ƙaddamar da shirin “Climate Change Africa,” wani shiri da zai yi duba kan tasirin da sauyin yanayi yake yi a Najeriya, da faɗin Afirka, da sauran sassan duniya baki ɗaya.

“Waɗannan sabbin shirye-shirye suna nuna irin yadda AREWA24 ta mayar da hankali wajen samar da shirye-shiryenta na cikin gida da suke da alaƙa da halin da al’umma ke ciki, da wasannin kwaikwayo, da kuma fina-finai, sannan bisa matakin ingancin shirye-shirye a duniya.” A ta bakin Shugaban Sashen Kasuwanci da Tallace-tallace kuma Mataimakon Shugaban AREWA24, Celestine Umeibe, ya bayyana cewa “waɗannan sabbin shirye-shirye suna nuna yadda muke iya samar da shirye-shirye masu ƙayatarwa domin masu kallonmu na cikin gida, da kuma shirye-shiryen da za su kai har zuwa kasahen duniya, da kuma nunawa sauran masu kallo na nahiyar Afirka da faɗin duniya yadda asalin rayuwar Arewacin Najeriya da Yammacin Afirka take.”

Tashar AREWA24 za ta cigaba da samar da sabbin zango na fitattun wasannin kwaikwayonta da take shiryawa, wato “Kwana Casa’in da kuma “Dadin Kowa,” sannan tana kan aikin samar da wasu sabbin wasannin kwaikwayo masu dogon zango guda uku da za fito a ƙarshen shekarar 2024 da kuma cikin shekarar 2025. Na farko a cikin sabbin wasannin kwaikwayon masu dogon zango shi ne, “Jos Chronicles,” wanda aka tsara a yankin jahohin tsakiyar kasarnan a Birnin Jos, kuma za a shi ne da Harsunan Turanci da kuma Hausar Jos. Shirin wasan kwaikwayo ne da ya ƙunshi barkwanci – wanda zai mayar da hankali a kan alaƙa mai sarƙaƙiya da ke tsakanin wasu abokai biyar, kuma ana sa rai zai jawo hankalin masu kallo daga yankin jahohin tsakiyar Najeriya. Haka kuma AREWA24 za ta dora wannan wasan kwaikwayo na “Jos Chronicles” a kan mahajarta ta kallo kai tsaye domin masu kallo talabijin a faɗin Afirka da kuma duniya baki ɗaya.
Haka kuma, AREWA24 tana aikin haɗin guiwa da manyan masu shirya fina-finan Hausa na Kannywood da dama domin ɗora wasannin kwaikwayonsu masu dogon zango a kan manhajar AREWA24 ON Demand da kuma tashar AREWA24 television network.

GAME DA AREWA24 (https://arewa24.com/company-overview/): AREWA24 da Bangarenta na samar da shirye-shirye, An fara gabatar da shiryen shiryen AREWA24 a shekarar 2014 domin cike wawakeken gibin da ake da shi a fagen shirye-shiryen nishadi da tsarin rayuwa da ake shiryawa da harshen Hausa masu inganci, wadanda ke nuni da abubuwan da ake alfahari da su a rayuwar Arewacin Najeriya, da al’adu, da kade-kade, da fina-finai, da fasaha, da girke-girke da kuma wasanni. A yau, tashar AREWA24 tana kaiwa ga mutane sama da milyan 40 masu magana da harshen Hausa a Najeriya da kuma Yammacin Afirka a kan tauraron dan dan’adam na Eutelsat da ke kan tsarin kallo kyauta, da kuma kan tauraron dan adam na StarTimes da ke kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba 138), da kafafen tauraron dan’adam na kamfanin Multichoice guda biyu da ke kan tsarin biya kudi, wato DSTV (tasha mai lamba 261) da kuma Gotv (tasha mai lamba 136), da kuma tauraron dan adam na Canal+ a kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba #297) a Jamhuriyar Nijar, da Chadi da kuma Kamaru, AREWA24 na amfana da masu kallo da ke kasancewa da dukkanin shafukanta na yanar gizo a kan AREWA24.com, facebook.com/AREWA24, da Instagram.com/AREWA24channel. Haka kuma AREWA24 tana yada shirye-shiryenta a tsarin kallo kai tsaye a ko ina a duniya a kan AREWA24 On Demand tare da hadin guiwar Vimeo.

Domin samun damar kallo kai tsaye a ko ina a duniya a kan AREWA24 ON DEMAND, ku shiga http://tv.arewa24.com ko ku sauke manhajar daga kan IOS App Store, ko Google Play, ko Apple TV, ko Roku Channel Store da kuma Amazon Fire TV.
Domin karin bayani, sai ku tuntubi: info@arewa24.com

Scroll to top