30 ga watan Yuni, 2020 – Tashar AREWA24, Tashar talabijin ta Hausa dake kan gaba wajen samar shirye-shirye masu nishadntarwa da nuna tsarin iyali, wadda ke da dakin daukar shirye-shirye a Najeriya dake Yammacin Nahiyar Afirka, tana sanar da wani sabon jadawalin shirye-shirye da kuma kayatattun shirye-shirye domin su dace da bukin cika shekaru shida da kafuwar wannan tasha. Tun baya kafa ta a shekarar 2014, Tashar AREWA24 tana samar da shirye-shirye masu inganci da muryar Arewacin Najeriya domin masu kallon tashar da kuma nuna abubuwan da yankin ke alfahari da su ta fuskar al’adu, da fasaha da kuma tsarin rayuwa domin iyalai masu magana da harshen Hausa a ko’ina.
Tashar AREWA24 za ta fara nuwa wani sabon shirin wasan kwaikwayo mai dogon zango a farkon watan Yuli, mai suna “Labarina”, wanda ya zo daga sanannaen mai bada umarni a fina-finan Hausa wato, Aminu Saira. Dadin-dadawa, masu kallo za su samu tagomashin sabon zangon shahararren shirin wasan kwaikwayon ban dariyar nan wato, “Gidan Badamasi”. Sannan Tashar za ta ci gaba da nuna cigaban shirin wasan kwaikwayonta mafi dadewa ana nunawa a Arewacin Najeriya wato, “Dadin Kowa” da kuma Gagara-badan Shirin wasan kwaikwayo mai dogon zango na tashar AREWA24 wato “KWANA CASA’IN”. Tashar AREWA24 za ta ci gaba da nuna sabbi kuma shahararrun fina-finan Kannywood, haka kuma ta tantance sunayen sabbin fina-finai da za su a zo a makonni da kuma watanni masu zuwa.
A mahimmin fagen shirye-shiryen yara da matasa, Tashar AREWA24 ta hada kai da shararren shirin nan na yaran wato, Sesame Street, domin gabatar da shirin da wani salo na Najeriya mai suna “Dandalin Sesame,” wanda ya kunshi dukkanin ‘yan wasan shirin, amma cikin tsarin al’adu na Najeriya da kuma Harshen Hausa. Haka kuma Tashar AREWA24 za ta fara nuna wani sabon shiri na ilimantar da yara da ya samu kyakkyawan yabo wato, “Akili and Me,” wanda ya zo daga wadanda suka shirya sanannen shirin nan na matasa wato, Ubongo Kids, wanda tashar AREWA24 ke nunawa a halin yanzu. Jadawalin sabbbin shirye-shiryen matasa zai karkare da “My Better World,”(Duniya mafi Inganci), wani shiri na yara da yake bibiyar labarin wasu matasan Afirka shida a yayin da suke kokarin shawo kan kalubale masu tsauri a makarantarsu, da Iyalansu, da kuma abokansu, sannan da shirin “The 77%”, wani shiri ne na matasa game da kaso 77 cikin dari na ‘yan Afirka wadanda suke kasa da shekaru 35 kuma wadanda za su zamo makomar nahiyar a nan gaba.
Mataimakin shugaban Sesame Workshop, Danny Labin, ya bayyana cewa “Sesame Workshop yana alfahari da hadin guiwa da Tashar Arewa24 wajen nuna Shirin Sesame Street wanda aka fassara shi domin dacewa da bukatar samar da ilimi na musamman ga yara a Najeriya. Muna fatan samun kyakkyawar nasara a wannan hadin guiwa da Tashar Arewa24 da kuma fatan Dandalin Sesame zai ci gaba da kawo farin ciki da kuma ilimantarwa da harshen Hausa tsawon shekaru da dama da za su zo a nan gaba,” .
A bangaren shirye-shiryen tsarin rayuwa, Tashar AREWA24 za ta fara nuna shirin “Jakadan Arewa.” Shirin Jakadan Arewa shiri ne na tafiye-tafiye, da tsarin rayuwa, da kuma sanannun mutane wanda ya kunshi sannannun Hausawa, Makada da kuma al’ummu da ke sauran kasashen Nahiyar Afirka da ma duniya baki daya.
Janar Manaja na tashar AREWA24 John Ekainu, ya bayyana cewa “Babu wata hanya da za mu yi bukin cika shekaru shida da kafuwar wannan tasha wadda ta fi mu kawowa masu kallonmu sabbin wasannin kwakwayo na Hausa, da shirye-shiryn yara da matasa da kuma sauran shirye-shiryen nishadantar da iyali da suke cikin jadawalinmu”. Ekainu ya kara da cewa “za a iya samun dukkanin wadannan sabbin shirye-shirye a shafin kallon shirye-shiryen tashar ta yanar gizo wato, “AREWA24 On Demand,” dake kaiwa ga dukkanin masu magana da harshen Hausa a fadin duniya.”
Shugaban sashen tallace-tallace na Tashar AREWA24 Celestine Umeibe, ya kara da cewa: “Dukka wadannan sabbin shirye-shirye suna kara nuna yadda tashar AREWA24 ke nuna damuwa ga mutane milyan 40 dake kallonmu da kuma abokan huldarmu da ke kawo mana tallace-tallace, wadanda ke samun yakinini dari bisa dari na sanya tallukansu, kuma suke samun cikakkun bayanai da kyakkyawan duba ga masu sayen kayayyaki dake Arewacin Najeriya, sannan kuma suke more gwaggwabar riba a kasuwancinsu sakamakon sanya tallukansu a tashar AREWA24.”
GAME DA TASHAR AREWA24: Tahsar AREWA24 da shirye-shiryenta, An kafa Tashar AREWA24 a shekarar 2014 domin cike wawakeken gibin da ake da shi a fagen shirye-shiryen nishadi da tsarin rayuwa da ake shiryawa da harshen hausa, wadanda ke nuni da abubuwan da ake alfahari da su a rayuwar Arewacin Najeriya, da al’adu, da kade-kade, da fina-finai, da fasaha, da girke-girke da kuma wasanni. A yau, tashar AREWA24 ta kai ga mutane milyan 38 masu magana da harshen Hausa a Najeriya da kuma yammacin nahiyar Afirka a kan tauraron dan dan’adam na Eutelsat da ake kallo kyauta, da kuma kan tauraron dan adam na StarTimes da ake biya (tasha mai lamba 138), da kafafen tauraron dan’adam na kamfanin Multichoice guda biyu da ake biya, wato DSTV (tasha mai lamba 261) da kuma Gotv (tasha mai lamba 101), da kuma tauraron dan adam na Canal+ payTV service (tasha mai lamba #285) a Jamhuriyar Nijar, da Chadi da kuma Kamaru. AREWA24 na amfana da masu kallo da ke kasancewa da dukkanin shafukanta na yanar gizo a kan AREWA24.com, facebook.com/AREWA24, Instagram.com/AREWA24channel, and twitter.com/AREWA24channel.
GAME DA MANHAJAR AREWA24 On Demand: Manhajar AREWA24 ON DEMAND, wani bangare ne na kamfanin Network AREWA24, Ltd, manhaja ce ta kallon dukkanin shirye-shiryen harshen Hausa da ake kira all-Hausa language global streaming da kuma OTT service a turance, da nufin yada al’adun hausawa da ake alfahari da su ga masu magana da harshen Hausa a fadin duniya. An kaddamar da wannan manhaja da kimanin sama da shirye-shirye 2,000 da suka shafi abubuwa daban-daban da salo daban-daban da suke da farin jini a Najeriya da kuma Yammacin nahiyar Afirka, wadanda suka hada da wasannin kwaikwayo masu dogon zango da tashar ke shiryawa, da wasannin kwaikwayo na masana’antar Kannywood, da tattaunawa daban-daban, da shirye-shiryen mata da na Hip Hop da na matasa da kuma yara da shirin girke-girke, da na al’adu da ma wasu da dama. Domin shiga tsarin kallon shirye-shirye ta kafar AREWA24 On Demand streaming service, sai ku ziyarci wannan adreshi http://tv.arewa24.com ko kuma ku sauke manhajar daga shafukan sauke manhajojin wayoyi na IOS App Store, ko Google Play, ko Apple TV, ko Roku Channel Store ko kuma Amazon Fire TV.
Domin karin bayani sai ku tuntubi: info@arewa24.com