Kamfanin Startimes da ke yada tashoshin talabijin na tauraron dan Adam, ya sanar da sanya fitacciyar tashar nan ta harshen Hausa wato AREWA24 cikin jerin tashoshin da ke kan
dikodarsu, a wani yunkuri da tashar ke yi na ganin ta biya bukatun dinbun mutanen da ke kallonta. A ta bakin Daraktan kasuwanci na tashar, Qasim Elegbede ya bayyana cewa “bukatar samar da karin tashoshin talabijin na harshen Hausa ta ci gaba da hauhawa a tsakanin masu kallo musamman ma a arewacin Najeriya a shekarar da ta gabata. Kasancewar mu na sauraron bukatun al’umma, mu na kokari ne mu ga mun bawa masu kallonmu hakikanin abin da su ke bukata, da karin shirye-shirye masu nishadantarwa.”
Shi ma da ya ke bayani game da wannan ci gaba da aka samu, shugaban sashen gudanar da tallace tallace na tashar AREWA24, Celestine Umeibe, ya yi nuni da cewa “hakika hadin guiwa tsakanin AREWA24 da kamfanin Startimes wani ci gaba ne da ake bukata. A yanzu mutane da dama masu magana da harshen hausa a Arewacin Najeriya da ma sauran sassan kasar zasu samu damar kallon shirye-shiryen tsarin rayuwa da nishadantarwa dake nuni da al’adu daban-daban da ake alfahari da su a Arewacin Najeriya akan wannan tasha da ke kan tsarin biya.”
Ya kuma kara da cewa “A halin yanzu masu tallace-tallace da kamfanoninsu zasu iya kaiwa ga dukkanin mutanen da suke so su tallata musu hajarsu ta hanyar amfani da tashar AREWA24 wadda a yanzu take cikin dukkanin tsarikan da ke kan dikodar Startimes.”
Tashar Arewa 24 na nuna shirye-shiryen na nishadi da al’adu da kuma addinai cikin harshen hausa wadanda take yadawa akan tasha ta 138 akan Dikodar Startimes. Idan za a iya tunawa a wataan Disanmbar shekarar 2017 ne, Kamfanin Startimes ya sanar da fara nuna tashoshinsa a Maiduguri babban birnin Jahar Borno a wani gagarumin yunkuri da yake yi domin cika alkawarin da ya dauka na samar da shirye-shirye masu nishadantarwa cikin sauki a kowanne gida a Najeriya..
You Might also like
-
Tashar AREWA24 za ta nuna shirin “77 Percent” na DW da Harshen Hausa
Shirin “The 77 Percent” – Shirin Talabijin ne da DW ta shirya domin matasa – wanda tashar AREWA24 da ke Najeriya ta fassarashi zuwa harshen Hausa. Kamar yadda masu daukar nauyin shirin suka bayyana a ganawar su da manema labarai, tashar AREWA24 za ta nuna wannan shirin da harshen Hausa a lokutan da aka fi kallon tashar.
Shirin “The 77 Percent” ya samo sunansa ne daga kason matasan Afirka ‘yan kasa da shekaru 35, sannan aka tsara shi domin nuna rayuwarsu tare da “labarun mahimman abubuwan da suka fuskanta a rayuwarsu”. Shirin na tsawon mintuna 30, an taba nuna shi ne a baya da harsunan turanci da Portuguguese.
Shugaban tashar AREWA24 Jacob Arback, yayin da yake bayani game da karbar shirin, ya bayyana cewa,”Kara shirin “The 77 Percent” a cikin tsarin jadawalin shirye-shiryenmu wata babbar dama ce ga tashar AREWA24 wajen nuna batutuwa na zahiri, da kalubale da labarum nasarori daga matasa a kowanne bangare na fadin wannan nahiya. Muna alfahari da farin ciki da hadin guiwa tare da DW da kuma sadar da wannan shiri mai inganci ga matansamu masu magana da harshen Hausa da kuma iyalansu.”
Daraktan shirye-shiryen Afirka na DW, Claus Stacher, yayin da yake bayani game da kaiwar shirin kashi na 50 a wannan, ya bayyana cewa: “Mun tsara shirinmy ta yadda rukunin matasan da muka yi wannan shiri domin su za su fahimci shirin a matsayin shiri mai kayatarwa, da tsari sannan kuma an yi shi don ‘yan asalin nahiyar Afirka. Tsarin ‘yan Afirka, da tattaunawa da kuma samo mafita yana kara daraja ga abokan hadin guiwarmu na kafafen yada labarai na zamani, da radiyo da talabijin a wannan yanki. Muna da da tabbacin cewa wannan hadin guiwa da tashar talabijin kamar tashar AREWA24 zai kara budede kofofin samun hadin guiwa a nan gaba.
Tushi: DW.COM
Post Views: 17,501 -
Al Jazeera da AREWA24 sun yi hadin guiwa don fassara shirye-shirye na musamman da masu dogon zango zuwa harshen Hausa domin masu kallo sama da milyan 40 dake arewacin Nijeriya da kuma yankin Sahel
23 ga watan Nuwamba, 2021. Doha/Lagos. Nan ba da jimawa ba masu kallon tashar AREWA24 sama da milyan 40 da ke Arewacin Najeriya, da kasashen Nijar, da Chad da kuma Cameroon za su fara kallon shirye-shirye Al Jazeera na musamman da masu dogon zango na turanci, da aka fassarasu zuwa harshen Hausa, bisa wata sabuwar yarjejeniya da aka cimma kwanannan tsakanin Al Jazeera da kuma AREWA24.
Wannan yarjejeniya za ta bada damar kallon shirye-shiryen Al Jazeera na harshen Turanci a kan tashar tauraron ta AREWA24 dake kan tsarin kallo kyauta da kuma sauran kafafen tauraron dan adam na yankin da ke kan tsarin biyan kudi na: DStv, da StarTimes, da CANAL+ da kuma TSTV sannan kuma da tsarin kallo kai tsaye ta yanar gizo daga ko ina a duniya ta manhajar AREWA24 wato “AREWA24 On Demand.”
“Mun ji dadi sosai da wannan yarjejeniya, kasancewar shirye-shiryen Al Jazeera na harshen turanci za su dinga zuwa ga sabbin masu kallo dake yanki mafi girma a nahiyar Afirka da harshensu,” a ta bakin Mai rike da mukamin Babban Darakta mai kula da Sashen Sadarwa da Al’amuran Kamfanin a Duniya, Ramzan Alnoimi. Ya kara da cewa “Muna kokari muga mun fadada hanyoyi yada shirye-shiryen Al Jazeera da aka fassarasu da sauran harsuna a nan gaba.”
Shugaban tashar AREWA24, Jacob Arback, ya bayyana cewa: Tashar Al Jazeera da kuma kayatattun shirye-shiryenta za su samu karbuwa sosai a wajen masu kallon tashar AREWA24 na Arewacin Najeriya da kuma yammacin Afirka.”
Ya kuma kara da cewa “Mun yi matukar jin dadi game da wannan hadin guiwa, da kuma kasancewarmu tashar talabijin ta farko da za ta yada shirye-shiryen Al Jazeera masu inganci da harshen Hausa, harshen da sama da mutane milyan 90 ke magana da shi a Najeriya da kuma Yammacin Afirka.
Tahsar AREWA24 da sashen shirye-shiryenta, an kafa Tashar AREWA24 a shekarar 2014 domin cike wawakeken gibin da ake da shi a fagen shirye-shiryen nishadi da tsarin rayuwa da ake shiryawa da harshen hausa. Tashar AREWA24 taNA kaiwa ga mutane sama da milyan 40 masu magana da harshen Hausa a Najeriya da kuma yammacin nahiyar Afirka, sannan kuma kamfanin da ke da ofisoshinsa a Kano da kuma Lagos yana daga cikin kamfanonin ‘yan Afirka da ke kan gaba ta fuskar yada labarai, samar da shirye-shirye, da kuma yada shirye-shirye na talabijin.
Najeriya na daya daga cikin kasashen da aka fi kallon tashar Al Jazeera. Kai tsaye wannan yarjejeniya za ta bada damar fassara shirye-shiryen Al Jazeera zuwa harshen Hausa da kuma yada su ga daukacin masu kallo daga sassa daban-daban na yankin.
GAME DA TASHAR ALJAZEERA ENGLISH: Tashar harshen Turanci ta Al Jazeera tana gabatar da shirin labarun duniya da al’amuran yau da kullum da kuma sa mutane su san halin da ake ciki, wanda ya samo asali ta yin imani da cewa kowa yana da labarin da ya dace a saurara. Ta aikin jaridar da take yi na rashin nuna tsoro da kuma shirye-shiryenta da suka lashe labar yabo, tashar tana bada ingantattun labarai game da mutane a ko’ina, ba tare da la’akari da yankin da suka fito ko kuma al’adunsu ba. Tun daga lokacin da aka kaddamar da tashar a shekarar 2006, tashar Al Jazeera ta harshen Turanci ta samu yabo a fadin duniya bisa nuna rashin nuna son rai da kuma rahotanni na gaskiya, inda ta samu nasarar samun lambobin yabo daga bangarorin aikin jarida da aka fi girmamawa a duniya. Tashar da ke da babban ofishinta a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma wakilai a ofisoshinmu 69 da ke fadin duniya, ta kuma dauki wani sabon salo ta fuskar labaran duniya. Daga kasuwannin da suka ci gaba zuwa kasuwannin da ke tasowa, tashar tana kara gundarin abin da ya shafi mutane ta hanyar kasancewa a wajen da abu ke faruwa a gurare da dama. A yau, tashar AlJazeera ta harshen Turanci tana kaiwa ga gidaje sama da milyan 350 a kasashe 150 (Daga watan Fabrairun 2020), inda take yada ingantattun rahotanni da ke fadakarwa, karfafa guiwa da kuma kalubalantar yadda ake kallon abubuwa.
Domin karin bayani, sai ku danna wannan https://www.aljazeera.com/
GAME DA TASHAR AREWA24: Tahsar AREWA24 da shirye-shiryenta, an kafa Tashar AREWA24 a shekarar 2014 domin cike wawakeken gibin da ake da shi a fagen shirye-shiryen nishadi da tsarin rayuwa da ake shiryawa da harshen hausa, wadanda ke nuni da abubuwan da ake alfahari da su a rayuwar Arewacin Najeriya, da al’adu, da kade-kade, da fina-finai, da fasaha, da girke-girke da kuma wasanni. A yau, tashar AREWA24 tana kaiwa ga mutane sama da milyan 40 masu magana da harshen Hausa a Najeriya da kuma yammacin nahiyar Afirka a kan tauraron dan dan’adam na Eutelsat da ke kan tsarin kallo kyauta, da kuma kan tauraron dan adam na StarTimes da ke kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba 138), da kafafen tauraron dan’adam na kamfanin Multichoice guda biyu da ke kan tsarin biya kudi, wato DSTV (tasha mai lamba 261) da kuma Gotv (tasha mai lamba 101), da kuma tauraron dan adam na Canal+ a kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba #285) a Jamhuriyar Nijar, da Chadi da kuma Kamaru. AREWA24 na amfana da masu kallo da ke kasancewa da dukkanin shafukanta na yanar gizo a kan AREWA24.com, facebook.com/AREWA24, Instagram.com/AREWA24channel, and twitter.com/AREWA24channel.
Domin karin bayani game da AREWA24 sai ku ziyarci https://arewa24.com/company-overview/ ko kuma ku tuntubemu ta wannan adireshi: info@arewa24.com
Post Views: 27,403 -
Sabuwar manhajar AREWA24 za ta kai ga Hausawa mazauna kasar waje fiye da mutum miliyan 8 kan kudi Dalar Amurka 4.99 a tsawon wata guda
Tashar Arewa24, tasha ta Hausa ta Arewacin Najriya ta na kaddamar da Arewa24 on Demand, wata sabuwar manhaja ta nuna shirye-shiryenta da ake kira subscription video-on-demand da “Over-the-Top” (OTT) a Turance. Russell Southwood ya gana da shugaban Arewa24, Jacob Arback kan dalilan kaddamar da wannan manhaja da kuma abunda su ka shirya.
Tashar Arewa24 ta dade tana shirya kirkirar manhaja mai share fage kamar wannan.
Manufarmu ita ce hada kan masu magana da harshen Hausa da ke Arewacin Najeriya, da wadanda ke Najeriya baki daya, da kuma Hausawa mazauna kasashen waje a kan wata kafa domin kallon shirye-shiryen talabijin. Muna tsammanin samun muhimmiyar taskar adana shirye-shirye da suke da ingancin da ake bukata domin yin kafada-da-kafada da sauran shirye-shiryen kashashen duniya.
Arback ya kwatanta manhajar da manhajar “Netflix dan kallon shirye-shiyen Hausa”, wannan yana nufin manhajar ta kunshi shirye-shirye daban-daban wadanda su ka hada da wasannin kwaikwayo da kade-kade da motsa jiki da sauransu. Babu tallace-tallace a ciki haka zalika masu kallo zasu kalli duk abinda suke so kan kudi Dalar Amurka 4.99 tsawon wata guda da kuma kudi Dalar Amurka 48 tsawon shekara.
An kaddamar da manhajar ne a karshen watan Oktoba, za a iya sauke manhajar daga shafin Arewa24 inda za ku samu manhajar da zata dace da wayoyinku masu amfani da tsarin iOS da kuma na Android. Kafar Google Play ta bayyana cewa kawo yanzu, fiye da mutum 500,000 suka sauke manhajar. Haka kuma za a iya samun manhajar a kan kafafen Roku da Amazon Prime haka kuma nan gaba kadan za a iya samun manhajar a kan wasu kafofin.
“Yadda muka tsara shi ne, mukan dora shirye-shirye kyauta kan shafin YouTube tare da sako mai zayyanawa masu kallo cewa zasu koma kallo a kan wannan sabuwar manhajar daga 21 ga watan Nuwamba. Muna so mu fara da masu kallonmu da ke kasashen Saudi Arabia da Sudan da Amurka da kuma na nahiyar Turai” Shugaban ya nuna cewa wannan tsarin ya fi sauki ga masu magana da harshen Hausa da ke ko ina a duniya fiye da tsarin tauraron dan dan’adam.
Arewa24 tana aiki tare da masu shirya fina-finai masu zaman kansu na Arewacin Najeriya wadanda Arback ya kira da ”Hazikan marubuta da suka kware wajen iya bada labari, Arback din ya kara da cewa, babu abun da suke bukata sai jari dan su habbaka su zamo kamar masana’antar Nollywood dake Kudancin Kasar. Muna aiki tare da wasu masu shirya fina-finai wadanda suke shirya fina-finai na musamman.”
Shirye-shiryen da aka fi maida hankali akai su ne rubutattun wasannin kwaikwaiyo da tashar ta shirya. Wasannin sun hada da shararrun wasannin kwaikwayonmu masu dogon zango wato “Kwana 90” da kuma “Dadin Kowa” wanda shi ne shirin wasan kwaikwayo na farko da tasha mai zaman kanta ta shirya. “Za mu samar da wani shirin wasan kwaikwayo a shekara mai zuwa. Masu Magana da harshen Hausa su na son wasannin kwaikwayo. Wasanni ne masu nuni da al’adu da rayuwar yau da kullum amma cikin kyakyyawan tsari.”
Dadin dadawa, sabuwar manhajar za ta kunshi dukkannin shirye-shirye da ke kan tashar wadanda suka hada da shirye-shiryen Hip Hop da na girke-girke da shirye-shiryen yara da na motsa jiki (wanda ya kunshi sharhin Gasar Premier League ta Nahiyayar Turai da manya-manyan gasar kwallon kafa da ake gudanarwa a birnin London wadanda aka juya zuwa harshen Hausa). Haka kuma akwai bangaren takaitattun shirye-shirye wadanda suka kunshi shirye-shiryen yara da wasannin barkwanci da kananun shirye-shirye da kuma gajerun fina-finai. ”Muna da wani shiri da mai’akatanmu na shashen sada zumunta suka tsara wanda suke fita su na tambayar mutane tambayoyi ma su ban dariya.”
Yaya matsalar yanar gizo da ake fuskanta za ta yi tasiri ga wannan manhajar? “Da farko dai manufar wannan manhajar ita ce nishadantar da masu magana da harshen Hausa mazauna kasashen waje. Tasharmu tasha ce da take kai wa kai tsaye ga wasu kebantattun mutane mazauna kasashen waje: Hasashe ya nuna cewa da akwai Hausawa mazauna kasashen waje kimanin miliyan 8 zuwa 10 wadanda ke zama a Saudi Arabia da kuma Sudan. Mazauna Arewacin Najeriya za su iya sauke manhajar kuma za ta zo musu da wani yanayi wanda zai daidaita matsalar yanar gizo da ake fuskanta.”
Ma su kallo mutum nawa ya ke hasashen samu nan da shekara 2-3?. “Ba na ce ba. Yanzu haka muna da masu kallon shirye-shiryenmu a shafin YouTube mutum miliyan 50 amma mun zuba hannun jari kuma muna da kyakkyawan zato game da manhajar. Za mu rika kawo sababbin shirye-shirye a kullum kuma a kowanne mako. Mu na san mu samar da shiri 11-12 a kowacce rana, dan haka zai yi kyau a samar da wata kafar yada shirye-shirye dan wasu ma su samu damar kallo.”
Wanne irin matakin hannun jari aka zuba cikin wannan manhajar? “Duba ga yanayin tasharmu dai babban hannun jari ne, amma ga matakin duniya an yi abu na azo a gani. Muna so mu zama mu ne na farko wajen kirkirar irin wannan manhajar. Tara shirye-shiryen shi ne abu na farko. Yanzu muna da kimanin sa’o’i Dubu 45. Rabin wadannan shirye-shiryen kadai na aka samu damar dorawa a kan manhajar kasancewar sauran aikin da ya rage ya yi nauyi saboda ingancinsa.”
Post Views: 8,534