AREWA24 Ta Kaddamar Da Sabon Dakin Shirye-Shirye

Tashar AREWA24tashar da ta yi fice wajen nishadantarwa da tsarin rayuwa da harshen Hausa a Kasar Nijeriya, na sanar da ku cewa, ta bude sabon Dakin Yada Shirye-shiryenta mai dauke da tsarika irin daban-daban da wasu sababbin shirye-shirye da za a fara a zango yada shirye-shiryenta karo na biyu. Sabon Dakin Yada shirye-shiryen zai taimakawa sabon salon shirin GARI YA WAYE da sabon salon shirin Sharhin Wasanni wato (Sport Central) da kuma sabon Salon Kayataccen shirin KUNDIN KANNYWOOD har ila yau, da SHARHIN FINA-FINAN KANNYWOOD. haka kuma, Tashar zata sake kawo muku shirin dake tattaunawa a kan lafiya da Cututtuka da Magani a cikin wani sabon salo da mai gabatar da shirin Lafiya Jari wanda za a rika gabatar da shi a Garin Abuja. wanda zamu karkare wannan sabon zango na uku na shirye-shiryen Nishadantarwa da kuma tsarin rayuwa da shirin ‘Haske; Matan Arewa’ wanda zai sada ku da shaharrrun matan Arewacin Nijeriyu. haka kuma, Tashar AREWA24 zata gabatar muku da sababbin Fina-finan Kannywood har karshen wannan shekara.

Bugu da kari, dan gane da sababbin shirye-shirye da Tashar AREWA24 ke kawo wa masu kallo, Tashar AREWA24 za ta kawo wa masu kallon sabbabin Fina-finan daga tashar ‘Zee World Series’ ‘Bhagya Lakshmi’ da wani fitaccen sabon Wasan Kwaikwawo daga Kasar ‘Turkish’ “Prisoner of love’ wato ‘Tarkon Kwana’ da wasu sabbabbin Fina-finan Kasar Indiya. kamar dukkaninn shirye-shiryen kasashen ketare masu lasisi na Tashar AREWA24. duk wadannan guntattakin Fina-finan na Series da na Fina-finan Indiya ana daukarsu ne da shiryasu da Harshen Hausa a Daikin daukar Sauti na Tashar AREWA24.

Babbar Mai Gabatar da Shirye-shiryen ‘GARI YA WAYE’ Aisha Lawal ta ce, ‘Masu Kallon Tashar AREWA24 sun cancanci a gabatar musu da kyawawan shiri da zai birge su, kuma ba dare ba rana mun kwashe wata da watanni muna ta aiki tukuru don ganin mun kawata sabon Dakin Yada shirye-shiryenmu mai fasali daban-daban. Sabon shirinmu na ‘Gari ya Waye’ ba zai tsaya ga sakawa masu kallo da sabon salon gabatar da shirin ka dai bane, Amma, har da saka musu da sabbabin masu gabatar da shirin wato Nana Musa da kuma Muhammad Abubakar Suleiman.’ An kafa tashar AREWA24 a Shekara ta 2014 domin cike gagarumin gibin samar da shirye-shirye masu nishadantarwa da tsarin rayuwa a Harshen Hausa, wadanda su ke nuna hakikanin rayuwa a Arewacin Najeriya, da Al’adu da Kade-Kade da Fina-Finai da Fasahar zane da Girke-Girke da kuma Wasanni. A yau, sama da mutane miliyan 80 masu magana da Harshen Hausa a fadin Najeriya da makwabtansu na Yammacin Afirika na kallon Tashar AREWA24 da ake haskawa a kan Tauraron Dan Adam ta Eutelsat a kyauta, a Kasa Najeriya kuma, ana iya kama ta a kan Dikodar Tsarin biya ta StarTimes Tasha ta 138 da kuma Dikododin Kamfanin Multichice masu guda biyu masu Tsarin Biya wato DSTV Tasha ta 261 da kuma GOtv Tasha ta 101.

GAME DA AREWA24: Tashar AREWA24 ( arewa24.com) tasha ce ta farko a kasar nan kuma tashar daya tilo dake shiryawa da kuma yada shirye-shiryenta a kan Tauraron Dan Adam cikin harshen Hausa Wadda kuma aka sadaukar da ita don nishadantar da iyali, Tashar AREWA24 ta Mayar da hankalin wajen bunkasa da yada shirin talabijin da harshen Hausa, domin cike gibin da masu magana da harshen Hausa ke fuskanta a fadin duniya, wadanda da yawansu ke dawowa kallon Tashar AREWA24 ta hanyar amfani da Manhajar Yanar Gizo a matsayin wata hanya da zata sada su da Al’adunsu da kuma Al’ummun Duniya.

Ana saka Shirye-shiryen Tashar AREWA24 a kowanne mako a kan shafin Youtube.com/Arewa24channel, haka kuma tashar tana samun matukar karuwa ta hanyar tattaunawa da masu kallonta a shafukanta na sada zumunta kamar Arewa24.com da Facebook.com/AREWA24 da Instagram.com/AREWA24channel da kuma twitter.com/AREWA24channel

Don karin bayani, sai ku tuntubemu a info@arewa24.com

About the Author
A Website Developer and Digital Content Creator, CloudOps Engineer, Web Developer & Tech Community Lead
Scroll to top