By Musa Abdullahi Sufi
Cutar sikila, matsala ce da ta addabi duniya, da miliyoyin mutane ke fama da ita a faɗin duniya. Kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta bayyana, kimanin yara dubu 300 ake haihuwa da cutar sikila a kowacce shekara, kuma mafi yawa an fi samun masu cutar a yankin Sahara na Afirka.
A Najeriya kaɗai, kimanin yara dubu 150 ake haihuwa da wannan cuta a kowacce shekara, wadda hakan ya sa ta zamo kasar da wannan cuta ta fi addaba a faɗin duniya. Yankin Arewacin Najeriya shi ne ya fi ɗaukar kaso mafi yawa, da kimanin kaso 20-30 cikin ɗari na yawan al’ummar da ke ɗauke da gadon cutar a jininsu.
Sikila na ci gaba da kasancewa wata matsananciyar matsala a Najeriya, wadda miliyoyin mutane ke fama da ita, musamman a cikin al’ummar da ke magana da Harshen Hausa. Domin daƙile wannan matsala, AREWA24, tashar talabijin ta Hausa da ke kan tauraron ɗan’adam mafi girma, ta ɗauki wani gagarumin shirin wayar da kai da kuma ilimantar da ɗaukacin masu kallonta, ta yin wani gangamin wayar da kai na tsawon wata guda da ta ware domin tattauna batun da ya shafi cutar ta sikila.
A tsawon watan Oktoba, AREWA24 ta mayar da hankali wajen nuna jerin shirye-shirye domin wayar da kai game da cutar sikila. Baƙi na musamman sun haɗa da likitoci, ma’aikatan jinya, masu larurar sikila, iyaye, shugabannin addinai, wakilan gwamnati, da kuma kwararru a harkar lafiya da sauransu, waɗanda za su kasance a cikin sanannun shirye-shirye daban-daban domin tattauna haƙiƙanin yadda rayuwa da cutar sikita take, da kuma mahimmancin gano cutar da wuri da kulawar da ta dace.
Wannan gangamin wayar da kai, yunƙuri ne na kawo sauyi a rayuwa, kasancewar miliyoyin masu magana da harshen Hausa a fadin duniya za su samu ilimi mai mahimmanci bisa yadda za a kaucewa cutar da kuma yadda za a kula da wannan larura da ake gado a cikin jini. Yawan masu fama da cutar a wannan yanki yana da alaƙa ne da ƙarancin kayan aikin kula da lafiya, da ƙarancin wayar da kai, da kuma ƙalubalen al’adu, waɗanda suka sa yake da mahimmaci a yaƙi wannan cuta ta hanyar wayar da kai, kamar irin wannan Gangamin wayar da kai na AREWA24 a watan Oktoba.
Wannan gangamin wayar da kai, za a yi shi ne domin wayar da kan al’umma, da samar musu bayanai na ceton rai, da fito da yadda za a yi gawaje-gwaje da kuma dabarun da za yi amfani da su da wuri wajen rage tasirin cutar ta sikila a Arewacin Najeriya.
Ilimantar da Miliyoyin al’umma: Gangamin wayar da kai na AREWA24 domin ceton rai, wani aiki ne da zai kawo sauyi a yaƙin da ake yi da larurar ta sikila. Yawan al’ummar da wannan tasha ke kaiwa garesu, yana tabbatar da cewa miliyoyin mutane, a Najeriya da ma fadin duniya, za su ilimantu game da mahimmancin da ke akwai game da buƙatar yin gwaji kafin aure. Iyalai da dama da suke fama da larurar sikila ba su da wayewar kai game da mahimmancin gwaji kafin aure domin kaucewa yaɗuwar cutar.
Wannan gangamin wayar da kai, zai cike wannan giɓin, ya kuma bawa masu kallo ilimin da zai taimaka musu wajen yanke hukuncin da zai iya ceto ‘ya’yan da za a haifa a nan gaba daga ƙalubalen da ke da alaƙa da cutar.
Bugu da ƙari, shirye-shiryen AREWA24 za su samar da mahimman bayanai a kan yadda za a kula da waɗanda ke fama da cutar ta sikila. Kasancewar kwararru a harkar lafiya cikin shirye-shirye, kamar Gari Ya waye, da Mata A Yau, zai tabbatar da cewa masu kallo sun ilimantu dangane da tallafin da ake buƙata ta fuskar kiwon lafiya da damuwar masu cutar, domin kyautatwar ingancin rayuwar masu ɗauke da cutar ta sikila.
Kama daga raɗadin da suke fuskanta lokaci bayan lokaci, zuwa fahimtar mahimmancin duba lafiyarsu akai-akai, waɗannan shirye-shirye za su gabatar da shawarwari a aikace waɗanda za su iya kawo tabbataccen sauyi a rayuwar mutane.
Faɗakar da al’ummu ta hanyar shawarar ƙwararru: Abin da ya sa wannan gangamin wayar da kai ya zamo na musamman shi ne, shigo da baƙi daban-daban cikin wannan shiri. Kama daga likitoci da ma’aikatan jinya da za su dinga bada shawarwari na kiwon lafiya ga masu ɗauke da cutar ta sikila da kuma iyalansu, suna masu bayyana abubuwan da suka fuskanta.Gangamin zai yi duba a kowanne ɓangare na haƙiƙanin yadda rayuwa da cutar sikila take.
Shugabannin addinai suma suna taka wata mahimmiyar rawa wajen wayar da kai, ta hanyar ƙarfafa mahimmancin kula da lafiya da kuma alhakin da ke kan al’umma wajen tabbatar da lafiya da kuma jin dadin yaran da za a haifa a nan gaba ta hanyar yin gwaji kafin aure.
Kwararru a harkar lafiya da kuma wakilan gwamnati za su ƙarawa shirin armashi ta hanyar bayar da ƙarin haske a kan irin ƙalubalen da ake da shi wajen shawo kan cutar sikila da kuma haska dokoki da shirye-shiryen da aka yi domin inganta hanyoyin samun kiwon lafiya.
Wannan gangami na wayar da kai bai tsaya iya wayar da kai ba kawai, zai kuma yi wkira domin a samar da tsarin kula da lafiya kyauta ga wadanda cutar ta sikila ta shafa, wanda wani babban mataki ne na magance matsalar tattalin arziki da zamantakewa da wasu majinyatan da dama ke fama da ita wajen neman magani.
Wannan wani mahimmin mataki ne na kawo ƙarshen yaɗuwar cutar sikila: Mahimmancin wayar da kai game da cutar sikila ba zai misaltu ba. A sassan Najeriya, musamman Arewa, har yanzu akwai ƙarancin fahimtar wannan cuta, wanda ke kaiwa ga yaɗuwar bayanai na ƙarya da nuna ƙyama.
Iyali da dama ba su san wajabcin neman shawarwari dangane da gadon kwayoyin halitta da kuma gwaji kafin aure ba, wanda hakan zai yi matuƙar rage yaɗuwar wannan cuta.
Gangamin wayar da kai na AREWA24 wani mahimmin taimako ne, kasancewar kai tsaye yana cike gibi ta fuskar ilimi da kuma samar da wata farfajiya don tattaunawa ta gaskiya kuma a bayyane game da cutar sikila.
Ta hanyar aiwatar da wannan gangamin ilimantarwa kyauta, AREWA24 tana yiwa al’umma hidima ne. Ƙoƙarin tashar game da harkokin kiwon lafiya, musamman a bangarorin da ba a fiya basu mahimmanci ba, yana nuna irin sadaukarwarta wajen sauke nauyin al’umma da kuma kyautata rayuwarsu. Yayin da Jaruman majinyatan da ke fama da cutar sikila da iyalansu ke amfana da wannan gangami, abu ne a zahiri cewa wannan gangami zai yi tasiri sosai a rayuwar milyoyin mutane.
Labarun jaruman da ke fama da cutar sikila, da shawarwarin kwararru daga likitoci, da kuma samun kwarin guiwa daga shugabannin addninai, duk za su hadu su samar da wani gagarumin saƙo da zai ceto rayuka.
Ƙari a kan wayar da kai, wannan gangami zai kuma zaburar da al’umma domin ɗaukar mataki. Baƙin, za su tattauna game da shirye-shiryen da suke gudana a yanzu haka, waɗanda aka tsara su domin samar da tsarin kula da lafiya kyauta ga majinyata masu larurar sikila, wanda zai ci gaba da ƙarfafar rawar da AREWA24 ta taka a matsayin wadda ta kawo sauyi mai amfani. Wannan shiri yana nufin ceto rayuka, da kyautata rayuwa ga jaruman da ke fama da cutar ta sikila, da kuma kare yaran da za a haifa a nan gaba daga fukantar irin wannan ƙalubale.
Rufewa: Wani shiri gangami wayar da kai a watan Oktoba na AREWA24 domin Jarumai masu larurar sikila, wani gagarumin aiki ne a yaƙin da ake yi da cutar sikila. Ta hanyar hada kwararru a harkar lafiya, da shugabannin al’umma, da kuma iyalan da abin da ya shafa, ba iya wayar da kai kaɗai tashar ke yi ba, bar ma da sauya rayuwar al’umma.
Jaruman da ke fama da cutar ta sikila da kuma iyalansu suna matuƙar godiya da wannan shiri, wanda zai basu fata, ya kuma ƙarfafesu ta inda aka fi buƙatar hakan.
Wannan gangamin wayar da kai na tsawon wata guda, wata shaida ce da ke nuna jajircewar da AREWA24 ke yi wajen amfani da tashar don yin abin alkhairi. Kada masu kallo su bari wannan dama ta musamman ta koyon ilimi, da tattaunawa, da kuma ɗaukar mataki a kan yaƙi da cutar sikila ta wuce su. Ta hanyar ilimantarwa da wayar da kai, duk za mu iya bayar da gudunmawa wajen ceto rayuka da kuma gina al’umma mai cike da ƙoshin lafiya.