Fim din Kwana Casa’in, wato shirin Hausa dirama ne da a ke nunawa a tashar talabijin ta AREWA24, inda zubi da tsarin labarin ya sha bamban da finafinan da mu ka saba kallo, wanda ba su wuce tunanin yaro karami ba.
Labarin ya na magana ne a kan siyasar kasar nan da irin abubuwan da ke faruwa a jami’o’inmu da ma rayuwa ga bakidaya.
Tuntuni ya kamata a rika zakulo irin wadannan matsaloli, saboda su ne damuwarmu, amma sai finafinan da a ke kira na Hausa su ka duge ga rawa da waka da gasar nuna jiki da matsattsun wanduna.
A ciikin Kwana Casa’in, tsarin hoto kansa na daban ne, domin ya sha bamban da irin tsarin hoton da mu ka saba gani, saboda an yi amfani da na’urar daukar hoto mai matukar inganci ta yadda mai kallo zai ga kamar a gabansa abubuwan ke faruwa.
Wuraren da a ka yi amfani da su irinsu asibitoci, ofisoshi, gidaje, makarantu ko gidan rediyo, nan ma abin jinjinawa ne, domin kuwa an yi amfani da wuraren da su ka dace ta yadda duk wanda ba dan kasa ba, idan ya kalla, zai ga tsantsar kama da gaskiya a cikin labarin, wanda hakan ma iyawa ce. Idan na nutsu Ina kallon Kwana Casa’in sai na ji tamkar gaske ne. Yadda masu mulki ke rayuwa da rayuwar talaka a wannan zamani da yadda a ke amfani da talaka, domin kama madafun iko duk an bayyanar da shi. Ina da yakinin kafin labarin ya kare mutane da dama za su dauki darasin rayuwa. Lokacin da na ga hotunan wasu jaruman Kannywood a cikin Kwana Casa’in kafin na fara kallon fim din, sai da na ji jiki na ya yi sanyi, saboda Ina tsoron kar su bata dirimar ta yadda za mu rika kallon ta kamar shirme, amma abin da ya burge ni shi ne yadda su ka shiga su ka bata a cikin shirin ba tare da kawo mishkila ko mayar da abin wasan yara ba. Hakan ya nuna ma ni kenan da za su sami labari mai inganci da kayan aiki, sannan su sako masu ilimin a cikin nasu shirye-shiryen, kila su ma za su samu su mike a Kannywood din kenan. Yadda jaruman su ka nuna dagiya da tsantsar kwarewa sosai, ya yi kyau matuka ta yadda ko wadanda su ka saba kallon finafinan kasashen ketare za su jinjina masu domin kasashen da su ka cigaba su na shirya dirama mai dogon zango ko finafinai kan matsalar da su ke fuska a kasar fiye da shirme irin wanda a ke yi a finafinan da mu ka saba gani. Da alama dai Kwana Casa’in shi ne labarin da ya ke kokarin taushe shirin dadin Kowa na Arewa 24 din dai, domin kamar yadda a ka kasa samun wani shirin dirama da zai yi karo da Dadin Kowa daga masana’antar Kannywood, watakila AREWA24 din ce dai kadai za ta iya yin karo shi da wannan sabon shiri tsararre na Kwana Casa’in. Tsawon lokacin da na dauka Ina kallon shirin Hausa na Kannywood lallai na gano wa Kannywood makarantar da za su kara ilmi. Sannu a hankali AREWA24 za ta maye gurbin shirin Hausa dirima, saboda su ne su ke tattauna abinda ya dame mu a kasa, ba rawa da juyi gaban allunan talabijin ba. Fadila H Aliyu Kurfi marubuciya ce mai sharhi kan al’amuran yau da kullum kuma ’yar gwagwarmaya.
Za a iya samun ta a imel: fadilakurfi@gmail.com ,
Facebook: Fadila H Aliyu Kurfi.
Read More at: https://hausa.leadership.ng/2019/04/18/ina-ma-kwana-casain-na-arewa-24-yazama-abin-koyi/