AREWA24 ZA TA FAƊAƊA ADADIN ƘASASHEN DA TAKE YAƊA SHIRYE-SHIRYENTA TARE DA CANAL+, ZA TA FAƊAƊA ZUWA ƘARIN ƘASASHEN YAMMACIN AFIRKA HUƊU: BENIN REPUBLIC, BURKINA FASO, MALI AND TOGO
15 ga Oktoba, 2024 – AREWA24, tashar talabijin da ke kan gaba wajen yada shirye-shirye da harshen Hausa, masu nishadantar da iyali da nuna tsarin rayuwa, wadda ke da ofishin daukar shirye-shiryenta a Yammacin Afirka, tare da hadin guiwar CANAL+ International, tana mai farin cikin sanar da gagarumin aikin faɗaɗa yaɗa shirye-shiryenta zuwa ƙarin kasashe huɗu: Benin Republic, Burkina Faso, Mali da Togo, a kan CANAL+ tasha mai lamba CH 297, wanda hakan zai ƙaru zuwa kasashen taƙwas (8) a Yammacin Afirka da ake kallon AREWA24, waɗanda suka haɗar da Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi.
Wannan mahimmin aikin faɗaɗawa, yana nuna mahimmanci da tasirin alaƙar da ke tsakanin CANAL+ International da AREWA24 ke da shi, bisa ‘yancin samun bayanai da shirye-shiryen nishaɗi masu inganci a faɗin nahiyar Afirka. Wannan cigaba zai bawa AREWA24 wata dama ta musamman wajen samar da ingantattun shirye-shirye ga sabbin miliyoyin masu kallonta a faɗin Jamhuriyar Benin, Burkina Faso, Mali da Togo. Da wannan aiki na faɗaɗawa domin kaiwa ga ƙarin masu kallon Talabijin, AREWA24 za ta ci gaba da ƙoƙarinta wajen nuna al’adu na alfahari, na masu magana da Harshen Hausa a fadin duniya, ta hanyar nuna shirye-shirye masu inganci da ke faɗakarwa, nishaɗantarwa da kuma zaburarwa.
“Muna farin cikin ganin shirye-shiryenmu sun kai ga sabbin miliyoyin masu kallo a Jamhuriyar Benin, Burkina Faso, Mali da Togo, tare da haɗin guiwar CANAL+ International” a ta bakin Celestine Umeibe, Mataimakin Shugaban AREWA24 kuma Babban Shugaban Sashen tallace-tallace da kasuwanci. Wannan wata gagarumar nasara ce ga ƙoƙarin da AREWA24 ke yi na kasancewa kafar yaɗa shirye-shirye da ke kan gaba a Nahiyar Afirka. Wannan zai sa mu ci gaba da yin ƙarfi a mataki na duniya, da haɗa kan harsuna da al’adu a faɗin Yammacin Afirka, a lokaci guda kuma muna buɗe mahimman damarmaki ga masu tallace-tallace da kamfanoni domin kaiwa ga masu kallo a gagarumar kasuwar Yammacin Afirka.”
Jadawalin AREWA24 da ya ƙunshi shirye-shirye daban-daban, kamar wasannin kwaikwayo masu dogon zango; wato Dadin Kowa, Kwana Casa’in da Gidan Badamasi, da sannanen shirin na matasa, wato Arewa Gen-Z, da shirin mata, wato Mata A Yau, da shirinta da ke zuwa kowacce rana wato shirin Gari Ya Waye, da ƙoƙarin da take na ci gaba da samar da shirye-shirye masu inganci a mataki na duniya, da kuma samar da shirye-shirye na cikin gida da ke abubuwan al’ada na alfahari, sun sa ta zamo amintacciyar hanyar nishaɗantar da iyali da harshen Hausa.
GAME DA AREWA24 (https://arewa24.com/company-overview/): AREWA24 da Bangarenta na samar da shirye-shirye, An fara gabatar da shiryen shiryen AREWA24 a shekarar 2014 domin cike wawakeken gibin da ake da shi a fagen shirye-shiryen nishadi da tsarin rayuwa da ake shiryawa da harshen Hausa masu inganci, wadanda ke nuni da abubuwan da ake alfahari da su a rayuwar Arewacin Najeriya, da al’adu, da kade-kade, da fina-finai, da fasaha, da girke-girke da kuma wasanni. A yau, tashar AREWA24 tana kaiwa ga mutane sama da milyan 40 masu magana da harshen Hausa a Najeriya da kuma Yammacin Afirka a kan tauraron dan dan’adam na Eutelsat da ke kan tsarin kallo kyauta, da kuma kan tauraron dan adam na StarTimes da ke kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba 138), da kafafen tauraron dan’adam na kamfanin Multichoice guda biyu da ke kan tsarin biya kudi, wato DSTV (tasha mai lamba 261) da kuma Gotv (tasha mai lamba 136), da kuma tauraron dan adam na Canal+ a kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba #297) a Jamhuriyar Nijar, da Chadi da kuma Kamaru, AREWA24 na amfana da masu kallo da ke kasancewa da dukkanin shafukanta na yanar gizo a kan AREWA24.com, facebook.com/AREWA24, da Instagram.com/AREWA24channel. Haka kuma AREWA24 tana yada shirye-shiryenta a tsarin kallo kai tsaye a ko ina a duniya a kan AREWA24 On Demand tare da hadin guiwar Vimeo.
Domin samun damar kallo kai tsaye a ko ina a duniya a kan AREWA24 ON DEMAND, ku shiga http://tv.arewa24.com ko ku sauke manhajar daga kan IOS App Store, ko Google Play, ko Apple TV, ko Roku Channel Store da kuma Amazon Fire TV.
Domin karin bayani, sai ku tuntubi: info@arewa24.com