News

AREWA24 ZA TA FAƊAƊA ADADIN ƘASASHEN DA TAKE YAƊA SHIRYE-SHIRYENTA TARE DA CANAL+, ZA TA FAƊAƊA ZUWA ƘARIN ƘASASHEN YAMMACIN AFIRKA HUƊU: BENIN REPUBLIC, BURKINA FASO, MALI AND TOGO

15 ga Oktoba, 2024 – AREWA24, tashar talabijin da ke kan gaba wajen yada shirye-shirye da harshen Hausa, masu nishadantar da iyali da nuna tsarin rayuwa, wadda ke da ofishin daukar shirye-shiryenta a Yammacin Afirka, tare da hadin guiwar CANAL+ International, tana mai farin cikin sanar da gagarumin aikin faɗaɗa yaɗa shirye-shiryenta zuwa ƙarin kasashe huɗu: Benin Republic, Burkina Faso, Mali da Togo, a kan CANAL+ tasha mai lamba CH 297, wanda hakan zai ƙaru zuwa kasashen taƙwas (8) a Yammacin Afirka da ake kallon AREWA24, waɗanda suka haɗar da Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi.

Wannan mahimmin aikin faɗaɗawa, yana nuna mahimmanci da tasirin alaƙar da ke tsakanin CANAL+ International da AREWA24 ke da shi, bisa ‘yancin samun bayanai da shirye-shiryen nishaɗi masu inganci a faɗin nahiyar Afirka. Wannan cigaba zai bawa AREWA24 wata dama ta musamman wajen samar da ingantattun shirye-shirye ga sabbin miliyoyin masu kallonta a faɗin Jamhuriyar Benin, Burkina Faso, Mali da Togo. Da wannan aiki na faɗaɗawa domin kaiwa ga ƙarin masu kallon Talabijin, AREWA24 za ta ci gaba da ƙoƙarinta wajen nuna al’adu na alfahari, na masu magana da Harshen Hausa a fadin duniya, ta hanyar nuna shirye-shirye masu inganci da ke faɗakarwa, nishaɗantarwa da kuma zaburarwa.

“Muna farin cikin ganin shirye-shiryenmu sun kai ga sabbin miliyoyin masu kallo a Jamhuriyar Benin, Burkina Faso, Mali da Togo, tare da haɗin guiwar CANAL+ International” a ta bakin Celestine Umeibe, Mataimakin Shugaban AREWA24 kuma Babban Shugaban Sashen tallace-tallace da kasuwanci. Wannan wata gagarumar nasara ce ga ƙoƙarin da AREWA24 ke yi na kasancewa kafar yaɗa shirye-shirye da ke kan gaba a Nahiyar Afirka. Wannan zai sa mu ci gaba da yin ƙarfi a mataki na duniya, da haɗa kan harsuna da al’adu a faɗin Yammacin Afirka, a lokaci guda kuma muna buɗe mahimman damarmaki ga masu tallace-tallace da kamfanoni domin kaiwa ga masu kallo a gagarumar kasuwar Yammacin Afirka.”

Jadawalin AREWA24 da ya ƙunshi shirye-shirye daban-daban, kamar wasannin kwaikwayo masu dogon zango; wato Dadin Kowa, Kwana Casa’in da Gidan Badamasi, da sannanen shirin na matasa, wato Arewa Gen-Z, da shirin mata, wato Mata A Yau, da shirinta da ke zuwa kowacce rana wato shirin Gari Ya Waye, da ƙoƙarin da take na ci gaba da samar da shirye-shirye masu inganci a mataki na duniya, da kuma samar da shirye-shirye na cikin gida da ke abubuwan al’ada na alfahari, sun sa ta zamo amintacciyar hanyar nishaɗantar da iyali da harshen Hausa.

GAME DA AREWA24 (https://arewa24.com/company-overview/):  AREWA24 da Bangarenta na samar da shirye-shirye, An fara gabatar da shiryen shiryen AREWA24 a shekarar 2014 domin cike wawakeken gibin da ake da shi a fagen shirye-shiryen nishadi da tsarin rayuwa da ake shiryawa da harshen Hausa masu inganci, wadanda ke nuni da abubuwan da ake alfahari da su a rayuwar Arewacin Najeriya, da al’adu, da kade-kade, da fina-finai, da fasaha, da girke-girke da kuma wasanni. A yau, tashar AREWA24 tana kaiwa ga mutane sama da milyan 40 masu magana da harshen Hausa a Najeriya da kuma Yammacin Afirka a kan tauraron dan dan’adam na Eutelsat da ke kan tsarin kallo kyauta, da kuma kan tauraron dan adam na StarTimes da ke kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba 138), da kafafen tauraron dan’adam na kamfanin Multichoice guda biyu da ke kan tsarin biya kudi, wato DSTV (tasha mai lamba 261) da kuma Gotv (tasha mai lamba 136), da kuma tauraron dan adam na Canal+ a kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba #297) a Jamhuriyar Nijar, da Chadi da kuma Kamaru, AREWA24 na amfana da masu kallo da ke kasancewa da dukkanin shafukanta na yanar gizo a kan AREWA24.com, facebook.com/AREWA24, da Instagram.com/AREWA24channel. Haka kuma AREWA24 tana yada shirye-shiryenta a tsarin kallo kai tsaye a ko ina a duniya a kan AREWA24 On Demand tare da hadin guiwar Vimeo.

Domin samun damar kallo kai tsaye a ko ina a duniya a kan AREWA24 ON DEMAND, ku shiga http://tv.arewa24.com ko ku sauke manhajar daga kan IOS App Store, ko Google Play, ko Apple TV, ko Roku Channel Store da kuma Amazon Fire TV.

Domin karin bayani, sai ku tuntubi: info@arewa24.com

Gangamin Wayar da kai na AREWA24 a watan October: Sauya rayuwa da tattauna ƙalubale game da cutar Sikila.

By Musa Abdullahi Sufi

Cutar sikila, matsala ce da ta addabi duniya, da miliyoyin mutane ke fama da ita a faɗin duniya. Kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta bayyana, kimanin yara dubu 300 ake haihuwa da cutar sikila a kowacce shekara, kuma mafi yawa an fi samun masu cutar a yankin Sahara na Afirka.

A Najeriya kaɗai, kimanin yara dubu 150 ake haihuwa da wannan cuta a kowacce shekara, wadda hakan ya sa ta zamo kasar da wannan cuta ta fi addaba a faɗin duniya. Yankin Arewacin Najeriya shi ne ya fi ɗaukar kaso mafi yawa, da kimanin kaso 20-30 cikin ɗari na yawan al’ummar da ke ɗauke da gadon cutar a jininsu.

Sikila na ci gaba da kasancewa wata matsananciyar matsala a Najeriya, wadda miliyoyin mutane ke fama da ita, musamman a cikin al’ummar da ke magana da Harshen Hausa. Domin daƙile wannan matsala, AREWA24, tashar talabijin ta Hausa da ke kan tauraron ɗan’adam mafi girma, ta ɗauki wani gagarumin shirin wayar da kai da kuma ilimantar da ɗaukacin masu kallonta, ta yin wani gangamin wayar da kai na tsawon wata guda da ta ware domin tattauna batun da ya shafi cutar ta sikila.

A tsawon watan Oktoba, AREWA24 ta mayar da hankali wajen nuna jerin shirye-shirye domin wayar da kai game da cutar sikila. Baƙi na musamman sun haɗa da likitoci, ma’aikatan jinya,  masu larurar sikila, iyaye, shugabannin addinai, wakilan gwamnati, da kuma kwararru a harkar lafiya da sauransu, waɗanda za su kasance a cikin sanannun shirye-shirye daban-daban domin tattauna haƙiƙanin yadda rayuwa da cutar sikita take, da kuma mahimmancin gano cutar da wuri da kulawar da ta dace.

Wannan gangamin wayar da kai, yunƙuri ne na kawo sauyi a rayuwa, kasancewar miliyoyin masu magana da harshen Hausa a fadin duniya za su samu ilimi mai mahimmanci bisa yadda za a kaucewa cutar da kuma yadda za a kula da wannan larura da ake gado a cikin jini. Yawan masu fama da cutar a wannan yanki yana da alaƙa ne da ƙarancin kayan aikin kula da lafiya, da ƙarancin wayar da kai, da kuma ƙalubalen al’adu, waɗanda suka sa yake da mahimmaci a yaƙi wannan cuta ta hanyar wayar da kai, kamar irin wannan Gangamin wayar da kai na AREWA24 a watan Oktoba.

Wannan gangamin wayar da kai, za a yi shi ne domin wayar da kan al’umma, da samar musu bayanai na ceton rai, da fito da yadda za a yi gawaje-gwaje da kuma dabarun da za yi amfani da su da wuri wajen rage tasirin cutar ta sikila a Arewacin Najeriya.

Ilimantar da Miliyoyin al’umma: Gangamin wayar da kai na AREWA24 domin ceton rai, wani aiki ne da zai kawo sauyi a yaƙin da ake yi da larurar ta sikila. Yawan al’ummar da wannan tasha ke kaiwa garesu, yana tabbatar da cewa miliyoyin mutane, a Najeriya da ma fadin duniya, za su ilimantu game da mahimmancin da ke akwai game da buƙatar yin gwaji kafin aure. Iyalai da dama da suke fama da larurar sikila ba su da wayewar kai game da mahimmancin gwaji kafin aure domin kaucewa yaɗuwar cutar.

Wannan gangamin wayar da kai, zai cike wannan giɓin, ya kuma bawa masu kallo ilimin da zai taimaka musu wajen yanke hukuncin da zai iya ceto ‘ya’yan da za a haifa  a nan gaba daga ƙalubalen da ke da alaƙa da cutar.

Bugu da ƙari, shirye-shiryen AREWA24 za su samar da mahimman bayanai a kan yadda za a kula da waɗanda ke fama da cutar ta sikila. Kasancewar kwararru a harkar lafiya cikin shirye-shirye, kamar Gari Ya waye, da Mata A Yau, zai tabbatar da cewa masu kallo sun ilimantu dangane da tallafin da ake buƙata ta fuskar kiwon lafiya da damuwar masu cutar, domin kyautatwar ingancin rayuwar masu ɗauke da cutar ta sikila.

 

Kama daga raɗadin da suke fuskanta lokaci bayan lokaci, zuwa fahimtar mahimmancin duba lafiyarsu akai-akai, waɗannan shirye-shirye za su gabatar da shawarwari a aikace waɗanda za su iya kawo tabbataccen sauyi a rayuwar mutane.

Faɗakar da al’ummu ta hanyar shawarar ƙwararru: Abin da ya sa wannan gangamin wayar da kai ya zamo na musamman shi ne, shigo da baƙi daban-daban cikin wannan shiri. Kama daga likitoci da ma’aikatan jinya da za su dinga bada shawarwari na kiwon lafiya ga masu ɗauke da cutar ta sikila da kuma iyalansu, suna masu bayyana abubuwan da suka fuskanta.Gangamin zai yi duba a kowanne ɓangare na haƙiƙanin yadda rayuwa da cutar sikila take.

Shugabannin addinai suma suna taka wata mahimmiyar rawa wajen wayar da kai, ta hanyar ƙarfafa mahimmancin kula da lafiya da kuma alhakin da ke kan al’umma wajen tabbatar da lafiya da kuma jin dadin yaran da za a haifa a nan gaba ta hanyar yin gwaji kafin aure.

Kwararru a harkar lafiya da kuma wakilan gwamnati za su ƙarawa shirin armashi ta hanyar bayar da ƙarin haske a kan irin ƙalubalen da ake da shi wajen shawo kan cutar sikila da kuma haska dokoki da shirye-shiryen da aka yi domin inganta hanyoyin samun kiwon lafiya.

Wannan gangami na wayar da kai bai tsaya iya wayar da kai ba kawai, zai kuma yi wkira domin a samar da tsarin kula da lafiya kyauta ga wadanda cutar ta sikila ta shafa, wanda wani babban mataki ne na magance matsalar tattalin arziki da zamantakewa da wasu majinyatan da dama ke fama da ita wajen neman magani.

Wannan wani mahimmin mataki ne na kawo ƙarshen yaɗuwar cutar sikila: Mahimmancin wayar da kai game da cutar sikila ba zai misaltu ba. A sassan Najeriya, musamman Arewa, har yanzu akwai ƙarancin fahimtar wannan cuta, wanda ke kaiwa ga yaɗuwar bayanai na ƙarya da nuna ƙyama.

Iyali da dama ba su san wajabcin neman shawarwari dangane da gadon kwayoyin halitta da kuma gwaji kafin aure ba, wanda hakan zai yi matuƙar rage yaɗuwar wannan cuta.

Gangamin wayar da kai na AREWA24 wani mahimmin taimako ne, kasancewar kai tsaye yana cike gibi ta fuskar ilimi da kuma samar da wata farfajiya don tattaunawa ta gaskiya kuma a bayyane game da cutar sikila.

Ta hanyar aiwatar da wannan gangamin ilimantarwa kyauta, AREWA24 tana yiwa al’umma hidima ne. Ƙoƙarin tashar game da harkokin kiwon lafiya, musamman a bangarorin da ba a fiya basu mahimmanci ba, yana nuna irin sadaukarwarta wajen sauke nauyin al’umma da kuma kyautata rayuwarsu. Yayin da Jaruman majinyatan da ke fama da cutar sikila da iyalansu ke amfana da wannan gangami, abu ne a zahiri cewa wannan gangami zai yi tasiri sosai a rayuwar milyoyin mutane.

Labarun jaruman da ke fama da cutar sikila, da shawarwarin kwararru daga likitoci, da kuma samun kwarin guiwa daga shugabannin addninai, duk za su hadu su samar da wani gagarumin saƙo da zai ceto rayuka.

Ƙari a kan wayar da kai, wannan gangami zai kuma zaburar da al’umma domin ɗaukar mataki. Baƙin, za su tattauna game da shirye-shiryen da suke gudana a yanzu haka, waɗanda aka tsara su  domin samar da tsarin kula da lafiya kyauta ga majinyata masu larurar sikila, wanda zai ci gaba da ƙarfafar rawar da AREWA24 ta taka a matsayin wadda ta kawo sauyi mai amfani. Wannan shiri yana nufin ceto rayuka, da kyautata rayuwa ga jaruman da ke fama da cutar ta sikila, da kuma kare yaran da za a haifa a nan gaba daga fukantar irin wannan ƙalubale.

Rufewa: Wani shiri gangami wayar da kai a watan Oktoba na AREWA24 domin Jarumai masu larurar sikila, wani gagarumin aiki ne a yaƙin da ake yi da cutar sikila. Ta hanyar hada kwararru a harkar lafiya, da shugabannin al’umma, da kuma iyalan da abin da ya shafa, ba iya wayar da kai kaɗai tashar ke yi ba, bar ma da sauya rayuwar al’umma.

Jaruman da ke fama da cutar ta sikila da kuma iyalansu suna matuƙar godiya da wannan shiri, wanda zai basu fata, ya kuma ƙarfafesu ta inda aka fi buƙatar hakan.

Wannan gangamin wayar da kai na tsawon wata guda, wata shaida ce da ke nuna jajircewar da AREWA24 ke yi wajen amfani da tashar don yin abin alkhairi. Kada masu kallo su bari wannan dama ta musamman ta koyon ilimi, da tattaunawa, da kuma ɗaukar mataki a kan yaƙi da cutar sikila ta wuce su. Ta hanyar ilimantarwa da wayar da kai, duk za mu iya bayar da gudunmawa wajen ceto rayuka da kuma gina al’umma mai cike da ƙoshin lafiya.

AREWA24 na sanar da sabon jadawalin shirye-shirye na wasannin kwaikwayo da take shiryawa, da fina-finai, da shirye-shiryenta na cikin gida a yayin da kamfanin ke cika shekaru 10 da kafuwa

AREWA24, tashar talabijin da ke kan gaba wajen yaɗa shirye-shirye masu nishaɗantar da iyali da tsarin rayuwa cikin harshen Hausa, wadda ke da ofishin samar da shirye-shirye a Najeriya da yammacin Afirka, tana sanar da wani gagarumin sabon jadawali na shirye-shirye, da fina-finai da wasannin kwaikwayo da take shiryawa da kuma karɓar wasannin kwaikwayo na Hausa masu dogon zango domin nuna su a mahajarta ta kallo kai tsaye, wato AREWA24 On Demand.

Domin bukin murnar cikar AREWA24 shekaru 10, tashar ta kaddamar da sabon shirinta na matasa, wato, “Arewa Gen-Z,” wanda aka shirya domin matasan Arewacin Najeriya masu ɗinbin yawa. Matasa ne ke shirya wa, kuma gabatar da shirin “Arewa Gen-Z”, wanda ke mayar da hamkali a kan irin ƙalubalen da a yanzu matasa ke fama da shi kowacce rana. Shirin na mintuna 30 da ake gabatarwa a kowanne mako, zai dinga kawo labarun nasarori, da fasaha, da waƙe-waƙe, da kuma al’adun matasa. Shirin zai kasance wata farfajiya domin abubuwan da aka san matasa da shi domin jawo hankalin matasa a faɗin Arewacin Najeriya.

Haka kuma nan ba da daɗewa ba AREWA24 za ta fito da fim ɗinta na farko mai gajeren zango, mai sunan, “The Jaru Road,” wani labari mai ƙayatarwa kuma na asalin Arewacin Najeriya, wanda aka shirya da harshen Turanci, kuma domin masu kallo dake fadin Afirka da ma sauran sassa na duniya. Kamfanin ya tsara shirya ƙarin wasu fina-finai huɗu a 2024 – 2025, wasu da harshen Hausa domin masu kallo a Najeriya da kuma Yammacin Afirka, wasu kuma da harshen Turanci domin masu kallo a dukkanin faɗin Afirka da duniya baki ɗaya. Bugu da ƙari, AREWA24 za ta ƙaddamar da shirin “Climate Change Africa,” wani shiri da zai yi duba kan tasirin da sauyin yanayi yake yi a Najeriya, da faɗin Afirka, da sauran sassan duniya baki ɗaya.

“Waɗannan sabbin shirye-shirye suna nuna irin yadda AREWA24 ta mayar da hankali wajen samar da shirye-shiryenta na cikin gida da suke da alaƙa da halin da al’umma ke ciki, da wasannin kwaikwayo, da kuma fina-finai, sannan bisa matakin ingancin shirye-shirye a duniya.” A ta bakin Shugaban Sashen Kasuwanci da Tallace-tallace kuma Mataimakon Shugaban AREWA24, Celestine Umeibe, ya bayyana cewa “waɗannan sabbin shirye-shirye suna nuna yadda muke iya samar da shirye-shirye masu ƙayatarwa domin masu kallonmu na cikin gida, da kuma shirye-shiryen da za su kai har zuwa kasahen duniya, da kuma nunawa sauran masu kallo na nahiyar Afirka da faɗin duniya yadda asalin rayuwar Arewacin Najeriya da Yammacin Afirka take.”

Tashar AREWA24 za ta cigaba da samar da sabbin zango na fitattun wasannin kwaikwayonta da take shiryawa, wato “Kwana Casa’in da kuma “Dadin Kowa,” sannan tana kan aikin samar da wasu sabbin wasannin kwaikwayo masu dogon zango guda uku da za fito a ƙarshen shekarar 2024 da kuma cikin shekarar 2025. Na farko a cikin sabbin wasannin kwaikwayon masu dogon zango shi ne, “Jos Chronicles,” wanda aka tsara a yankin jahohin tsakiyar kasarnan a Birnin Jos, kuma za a shi ne da Harsunan Turanci da kuma Hausar Jos. Shirin wasan kwaikwayo ne da ya ƙunshi barkwanci – wanda zai mayar da hankali a kan alaƙa mai sarƙaƙiya da ke tsakanin wasu abokai biyar, kuma ana sa rai zai jawo hankalin masu kallo daga yankin jahohin tsakiyar Najeriya. Haka kuma AREWA24 za ta dora wannan wasan kwaikwayo na “Jos Chronicles” a kan mahajarta ta kallo kai tsaye domin masu kallo talabijin a faɗin Afirka da kuma duniya baki ɗaya.
Haka kuma, AREWA24 tana aikin haɗin guiwa da manyan masu shirya fina-finan Hausa na Kannywood da dama domin ɗora wasannin kwaikwayonsu masu dogon zango a kan manhajar AREWA24 ON Demand da kuma tashar AREWA24 television network.

GAME DA AREWA24 (https://arewa24.com/company-overview/): AREWA24 da Bangarenta na samar da shirye-shirye, An fara gabatar da shiryen shiryen AREWA24 a shekarar 2014 domin cike wawakeken gibin da ake da shi a fagen shirye-shiryen nishadi da tsarin rayuwa da ake shiryawa da harshen Hausa masu inganci, wadanda ke nuni da abubuwan da ake alfahari da su a rayuwar Arewacin Najeriya, da al’adu, da kade-kade, da fina-finai, da fasaha, da girke-girke da kuma wasanni. A yau, tashar AREWA24 tana kaiwa ga mutane sama da milyan 40 masu magana da harshen Hausa a Najeriya da kuma Yammacin Afirka a kan tauraron dan dan’adam na Eutelsat da ke kan tsarin kallo kyauta, da kuma kan tauraron dan adam na StarTimes da ke kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba 138), da kafafen tauraron dan’adam na kamfanin Multichoice guda biyu da ke kan tsarin biya kudi, wato DSTV (tasha mai lamba 261) da kuma Gotv (tasha mai lamba 136), da kuma tauraron dan adam na Canal+ a kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba #297) a Jamhuriyar Nijar, da Chadi da kuma Kamaru, AREWA24 na amfana da masu kallo da ke kasancewa da dukkanin shafukanta na yanar gizo a kan AREWA24.com, facebook.com/AREWA24, da Instagram.com/AREWA24channel. Haka kuma AREWA24 tana yada shirye-shiryenta a tsarin kallo kai tsaye a ko ina a duniya a kan AREWA24 On Demand tare da hadin guiwar Vimeo.

Domin samun damar kallo kai tsaye a ko ina a duniya a kan AREWA24 ON DEMAND, ku shiga http://tv.arewa24.com ko ku sauke manhajar daga kan IOS App Store, ko Google Play, ko Apple TV, ko Roku Channel Store da kuma Amazon Fire TV.
Domin karin bayani, sai ku tuntubi: info@arewa24.com

Aljazeera Presents

Shiri ne da zai ke kawo muku labarai daban-daban daga kowanne sako na duniya domin tattaunawa, da ilimantarwa, sannan kuma da zaburarwa.

My Better World

Labari ne na wasu matasa ‘yan Afrika yayın da suke gaggwarmaya da kalubale daban-daban irin na makaranta, da na iyali, da kuma na abota.

Bino & Fino

Fino & Bino shirin yara mai ilimantarwa akan labarin Fino da Bino da kuma malam bude mana littafi mai ban al’ajabi yayın da suke koyun tarihi da al’adun nahiyar Afrika.

Buka Africana

Wata jajirtacciyar uwa, da ‘yarta da ba ta da gogayyar rayuwa da kuma ma’aikatanta masu juriyar da ajizanci, yayın da suke fuskantar kalubale tare.

Sirrin Boye

Shirine na wata yarinya mai suna Amira ‘yar shekaru 12 da ke da baiwar sani da fahimtar idan kwanan mutum ya zo karshe in ta hadu dashi.

Tashar AREWA24 Tana Sanar Da Kaddamar Da Sabon Sashen Wasannin Kwaikwayo Da Fina-Finai Da take Shiryawa

AREWA24, tashar talabijin da ke kan gaba wajen yada shirye-shiryen nishadantar da iyali da tsarin rayuwa, wadda ke da ofishin daukar shirye-shiryenta a Najeriya a Yammacin Afirka, tana sanar da kaddamar da sabon sashen wasannin kwaikwayo da fina-finan da take shiryawa. Sabon sashen shirye-shiryen kamfanin zai samar da rubutun labaru da kuma shirya sabon jadawalin sabbin wasannin kwaikwayo masu dogon zango da kuma daidaikun fina-finai, don bada labarun Afirka na asali daga Arewacin Najeriya da kuma Yammacin Nahiyar Afirka da harshen Hausa da kuma na harshen Turanci zalla.

Ofishin samar da shirye-shiryen tashar AREWA24, ya kasance yana shiryawa da kuma yada kayatattu kuma shahararrun wasannin kwaikwayo masu dogon zango na Hausa a Arewacin Najeriya da Yammacin Afirka, wato “Dadin Kowa” wanda a halin yanzu ya kai zango na 25, da kuma wasan kwaikwayon tashar da ya kunshi siyasa, wato “Kwana Casa’in” (“90 Days”), wanda aka kammala daukar zango na 7 a kwanannan. Ana kan shirya wasu wasannin kwaikwayon masu dogon zango da dama, kuma wannan kamfani zai fara nuna shirin fim mai gajeren zango da ya shirya na farko a zango na hudu a shekarar 2022.

“AREWA24” ta kasance tana daga darajar wasu daga cikin kwararrun marubutan Najeriya, da masu shirya fina-finai, da daraktoci, da masu tace hotuna da kuma jarumai tun bayan kafuwar tashar shekaru takwas da suka gabata. Shugaban tashar AREWA24 Jacob Arback, ya bayyana cewa, “A halin yanzu muna matsayin babban kamfanin samar da shirye-shirye na ‘yan Afirka, mai samar da tsararrun shirye-shirye masu inganci na Afirka – domin ‘yan Najeriya, da ‘yan Afirka da kuma masu kallo da ke yammacin duniya, wadanda ke kara jin dadin kallon irin wadannan labaru masu kayatarwa da aka tsara su da inganci cikin wasannin kwaikwayo da fina-finai daga wannan nahiya”.

Shugaban sabon sashen wasannin kwaikwayon da fina-finai shi ne Evans Ejioju, wani gogagge kuma kwararre, da ya kasance a matsayin babban mai shirya shirin wasan kwaikwayon nan mai dogon zango na Kwana Casa’in tun daga zango na farko. Salisu Balabare, wanda ke bada umarni a shirin na Kwana Casa’in kuma wanda ya dade yana bada umarni a shirin wasan kwaikwayo nan mai dogon zango na Dadin Kowa, shi ne zai jagoranci bangaren kirkira na wannan sabon sashe. Bob Reid, sanannan da ya lashe lambar yabo ta Emmy-award a matsayin babban mashiryin shirin nan na kamfanin Discovery Networks, kuma tsohon mai kula da kimar ma’aikata (EVP), kuma babban shugaban sashen shirye-shirye a tashar The Africa Channel da ke kasar Amurka, shi ne zai kasance a matsayin mashawarci kuma babban mashiryin shiri na wasannin kwaikwayo da fina-finan da tashar AREWA24 ke shiryawa.

Samar da wannan sabon sashen na wasannin kwaikwayo da fina-finai, zai sa tashar AREWA24 ta amfani kwarewa da kuma kayan aikin shirye-shirye da ta tattara, sannan kuma ta nemi abokan hulda masu kaifin basira daga dukkanin fadin duniya, da kuma manyan kamfanonin da ke aikin yada shirye-shirye kai tsaye ta yanar gizo (streaming services) a duniya, domin bunkasawa da shirya rubutattun shirye-shirye.

“Manufarmu ita ce, shirya karin fitattu kuma kayatattun wasannin kwaikwayo domin masu kallonmu da ke magana da harshen Hausa”. Arback ya ce, “Wasu daga cikin shirye-shiryen da za mu samar, ba lallai a fara nuna su a tashar AREWA24 ba.  A nan gaba, mun shirya samar da jadawalin shirye-shirye da suka dace da masu kallo a fadin nahiyar Afirka da kuma sauran sassa na duniya. Sabon sashen shirye-shiryen zai bamu dama mu tsara shirye-shiryenmu domin su dace da dukkanin masu kallo. Don yin hakan, mun tsara shirya shirye-shirye na ‘yan Afirka masu inganci da harshen Turanci da kuma harshen Hausa kuma mu tabo karin batutuwan da ke ciwa mutane tuwo a kwarya a cikin nau’ikan shirye-shirye da dama.”

GAME DA TASHAR AREWA24: Tahsar AREWA24 da bangaren shirye-shiryenta, an kafa Tashar AREWA24 a shekarar 2014 domin cike wawakeken gibin da ake da shi a fagen shirye-shiryen nishadi da tsarin rayuwa da ake shiryawa da harshen Hausa, wadanda ke nuni da abubuwan da ake alfahari da su a rayuwar Arewacin Najeriya, da al’adu, da kade-kade, da fina-finai, da fasaha, da girke-girke da kuma wasanni. A yau, tashar AREWA24 tana kaiwa ga mutane sama da milyan 40 masu magana da harshen Hausa a Najeriya da kuma yammacin nahiyar Afirka a kan tauraron dan dan’adam na Eutelsat da ke kan tsarin kallo kyauta, da kuma kan tauraron dan adam na StarTimes da ke kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba 138), da kafafen tauraron dan’adam na kamfanin Multichoice guda biyu da ke kan tsarin biya kudi, wato DSTV (tasha mai lamba 261) da kuma Gotv (tasha mai lamba 101), da kuma tauraron dan adam na Canal+ a kan tsarin biyan kudi (tasha mai lamba #285) a Jamhuriyar Nijar, da Chadi da kuma Kamaru.  AREWA24 na amfana da masu kallo da ke kasancewa da dukkanin shafukanta na yanar gizo a kan AREWA24.comfacebook.com/AREWA24Instagram.com/AREWA24channel. AREWA24 tana kuma yada shirye-shirye kai tsaye ta yanar gizo a duniya a kan manhajar nan ta, AREWA24 On Demand tare da hadin guiwar kamfanin Vimeo.

Domin yin rijista da manhajar kallon shirye-shirye kai tsaye ta yanar gizo a kan manhajar AREWA24 ON DEMAND, sai ku ziyarci http://tv.arewa24.com ko kuma ku sauke manhajar daga IOS App Store, Google Play, Apple TV, Roku Channel Store da kuma Amazon Fire TV.

Domin karin bayani, sai ku tuntubi: info@arewa24.com

Scroll to top