Tashar AREWA24 za ta nuna shirin “77 Percent” na DW da Harshen Hausa

Shirin “The 77 Percent” – Shirin Talabijin ne da DW ta shirya domin matasa – wanda tashar AREWA24 da ke Najeriya ta  fassarashi zuwa harshen Hausa. Kamar yadda masu daukar nauyin shirin suka bayyana a ganawar su da manema labarai, tashar AREWA24 za ta nuna wannan shirin da harshen Hausa a lokutan da aka fi kallon tashar.

Shirin “The 77 Percent” ya samo sunansa ne daga kason matasan Afirka ‘yan kasa da shekaru 35, sannan aka tsara shi domin nuna rayuwarsu tare da “labarun mahimman abubuwan da suka fuskanta a rayuwarsu”. Shirin na tsawon mintuna 30, an taba nuna shi ne a baya da harsunan turanci da Portuguguese.

Shugaban tashar AREWA24 Jacob Arback, yayin da yake bayani game da karbar shirin, ya bayyana cewa,”Kara shirin “The 77 Percent” a cikin tsarin jadawalin shirye-shiryenmu wata babbar dama ce ga tashar AREWA24 wajen nuna batutuwa na zahiri, da kalubale da labarum nasarori daga matasa a kowanne bangare na fadin wannan nahiya. Muna alfahari da farin ciki da hadin guiwa tare da DW da kuma sadar da wannan shiri mai inganci ga matansamu masu magana da harshen Hausa da kuma iyalansu.”

Daraktan shirye-shiryen Afirka na DW, Claus Stacher, yayin da yake bayani game da kaiwar shirin kashi na 50 a wannan, ya bayyana cewa: “Mun tsara shirinmy ta yadda rukunin matasan da muka yi wannan shiri domin su za su fahimci shirin a matsayin shiri mai kayatarwa, da tsari sannan kuma an yi shi don ‘yan asalin nahiyar Afirka. Tsarin ‘yan Afirka, da tattaunawa da kuma samo mafita yana kara daraja ga abokan hadin guiwarmu na kafafen yada labarai na zamani, da radiyo da talabijin a wannan yanki. Muna da da tabbacin cewa wannan hadin guiwa da tashar talabijin kamar tashar AREWA24 zai kara budede kofofin samun hadin guiwa a nan gaba.

Tushi: DW.COM

About the Author
A Website Developer and Digital Content Creator, CloudOps Engineer, Web Developer & Tech Community Lead
Scroll to top