Shiri ne domin matasan Afirka, da ya kunshi labaru, muhawara, da fashin baki kai tsaye daga wannan nahiya game da batutuwan da aka fi damuwa da su. Kaso saba’in da bakwai cikin dari na al’ummar Afirka suna da shekaru kasa da talatin da biyar. Amma sai dai kuma kididdiga ta nuna cewa basa samun wakilci yadda ya kamata. Lokaci ne da ya kamata a ji muryoyinsu kasancewar su ne makomar Nahiyar Afirka. Muna kawo muku rahotanni masu matukar mahimmanci, labarun mutane, a kuma tattaunawa kai tsaye daga wannan nahiya kan batutuwan da suka fi ciwo al’umma tuwo a kwarya.