Kyautata Rayuwa

Wasan Kwaikwayo ne mai dogon zango wanda ke bayyana matsaltsalun da iyalai ke fuskanta, da kuma yawan sake-saken aure da ake fama da shi, musamman ma a kasar Turkiya.

Ko wane kashi na cikin shirin na mayar da hankali ne a kan wasu iyalai daban da ke fuskantar matsaloli, wanda a koda yaushe, ke daf da rabuwa, haka zalika da kokarin manyan jaruman shirin su uku wadanda suka kasance ma’aikatan Kungiya ta Musamman da ke taimakawa iyalan dake cikin damuwa: Nazli, Mai bada shawarwarin da suka shafi aure, Yusuf, shi ne mai bada shawarwarin da suka shafi shari’a, sai kuma ‘Nisa’ ita ce mai sasantawa.

A yayin da mutane ukun ke taimakawa, ya zama dole su magance matsaltsalolin irinsu ‘rashin kudi’ da al’amuran sirri da kuma sauran matsaltsalun rayuwarsu da suke fuskanta.

About the Author
A Website Developer and Digital Content Creator, CloudOps Engineer, Web Developer & Tech Community Lead
Scroll to top