Shiri ne mai nishadantarwa dake yin sharhi da kuma tunawa da fitattun wakokin masana’antar Kannywood.
28 ga watan Yuni, 2021 – Tashar AREWA24, tashar talabijin da ke kan gaba a fagen shirye-shirye na harshen Hausa masu nishadantarwa da tsarin rayuwa, kuma take da dakin daukar shirye-shirye a Najeriya da ke Yammacin Nahiyar Afirka, tana bukin cika shekaru bakwai da kafuwa, ta hanyar kawowa masu kallonta babban jadawalin sabbin shirye-shirye na harshen Hausa da ba a taba irinsa ba a tarihin tashar. Sabon jadawalin shirye-shiryen na tashar AREWA24 zai fara aiki ne a watan Yuli, kunshe da sabbin wasannin kwaikwayon tashar, da sabon shirin tattaunawa na mata, da sabbin shirye-shiryen yara don “Ilimantarwa da nishadantarwa” masu dogon zango, da sabbin shirye-shiryen wasan kwallon kafa, tare da sauran shahararrun wasannin kwaikwayon tashar AREWA24 da kuma sauran shirye-shiryen da take gabatarwa. Da yawa daga cikin wadannan shirye-shirye za kuma su kasance a kan manhajar AREWA24 On Demand nan take, manhajar tashar da ke bawa iyalai masu Magana da harshen Hausa da ke fadin duniya damar kallon shirye-shiryen Arewacin Najeriya masu nishadantarwa, da al’adu da kuma tsarin rayuwa. A halin yanzu ana ci gaba da daukar sabbin zangon shahararrun wasannin kwaikwayo masu dogon zango na tashar, wato Kwana Casa’in da Dadin Kowa, kuma za a fara nuna su a watan Oktoba.
Sabbin wasannin kwaikwayo na Hausa guda uku ne ke kan gaba a cikin sabon jadawalin shirye-shiryen AREWA24: Buka Africana, wani wasan barkwanci da aka shirya a wani gidan cin abinci da ke yankin Arewa ta tsakiya, ko “Buka.” Labarina-zango na-3, sabon zangon daya daga cikin shahararrun wasannin kwaikwayo masu dogon zango na Arewacin Najeriya da kuma Sirrin Boye, wani sabon wasan kwaikwayo da ya kunshi rudani da muggan laifuka. Haka kuma a watan Yuli, tashar AREWA24 za ta fara nuna wani gagarumin sabon shiri tattaunawa na mata, mai suna “Mata A Yau” (Today’s Woman), wanda ya kunshi masu gabatarwa mutum hudu da suka zo daga bangarori daban-daban na rayuwa, kuma masu shekaru daban-daban, da za su tattauna mahimman batutuwan da mata ke fuskanta a halin yanzu a Arewacin Najeriya.
Shugaban Tashar AREWA24, Jacob Arback, yayin da yake bayani game da cigaban da kamfanin ya samu tsawon shekaru bakwai, ya yabawa hukumar gudanar da kuma ma’aikatan kamfanin bisa gagarumin kwazon da suke nunawa a fagen talabijin, da kafafen yada labarai da kuma fasahar kirkira a Arewacin Najeriya. “Mutane da dama ba su fahimci cewa akwai mutane masu magana da harshen hausa sama da milyan 80 a Arewacin Najeriya da kuma yankin Sahel ba, kuma yankin na cike da matasa masu basira a ko’ina. Arback ya kara da cewa, “Sai dai, abin da na fi alfahari da shi, shi ne yadda hukumar gudanarwa da ma’aikatanmu suka tattaru daga bangarori na rayuwa daban-daban, da addinai, da kabilu, da kuma yankunan Najeriya daban-daban suka kasance ma’aikata a Jahar Kano a Najeriya, domin shirya kayatattun shirye-shiryen da ke fitowa daga nahiyar Afirka a yau.”
Tashar AREWA24 tana kuma fadada shirye-shiryenta na yara masu Ilimantarwa da kuma nishadantarwa a watan Yuli, A karon farko, an fassara shirin “Sesame Street Friends,” da ya lashe lambobin yabo da dama zuwa harshen Hausa, da dukkanin ‘yan wasan shirin da kuke so, da wasannin barkwanci, da zane mai motsi da kuma wasannin ‘yartsana. Haka kuma shirin Super Sema zai zo a tashar AREWA24 da harshen hausa, wanda shi ne shirin zane mai motsi na jaruman Afirka na farko mai dogon zango da aka shirya shi game da wata matashiyar yarinya da ta ke yin wani aiki na musamman don kare kauyensu da ke Afirka daga wani Azzalumi mara Imani da sojojinsa na butum-butumi masu naci. Jarumar da ta lashe lambar yabo ta Oscar, Lupita Nyong’o, tana daga cikin wadanda aka yi amfani da muryoyinsu a shirin na Super Sema mai dogon zango sannan kuma abokiyar hulda ce ga kamfanin kasar Kenya, Kukua da ya shirya shirin Super Sema. Domin faratawa ‘yan Najeria magoya bayan wasan kwallon kafa, Tashar AREWA24, a jadawalin shirye-shiryenta na watan Yuli, za ta fara nuna wasu sabbin shirye-shiryen wasanin kwallon kafa masu dogon zango, wato “Homage, da “Perfection.”
GAME DA TASHAR AREWA24: An kafa Tashar AREWA24 a shekarar 2014 domin cike wawakeken gibin da ake da shi a fagen shirye-shiryen nishadi da tsarin rayuwa da ake shiryawa da harshen Hausa, wadanda ke nuni da abubuwan da ake alfahari da su a rayuwar Arewacin Najeriya, da al’adu, da kade-kade, da fina-finai, da fasaha, da girke-girke da kuma wasanni. A yau, tashar AREWA24 tana kaiwa ga mutane sama da milyan 40 a Najeriya da kuma yammacin Afirka ta tauraron dan dan’adam na Eutelsat na kyauta, da da kafar tauraron dan adan na StarTimes da ake biya (tasha mai lamba 138), da kafafen tauraron dan’adam na kamfanin Multichoice guda biyu da ake biya, wato DSTV (tasha mai lamba 261) da kuma Gotv (tasha mai lamba 101), da kafar tauararon dan’adan ada ake biya ta TSTV (Tasha mail amba 361) da kuma ta Canal+ da ake biya (tasha mai lamba #285) a kasashen Nijar, Chadi da kuma Kamaru. Tashar AREWA24 na amfana da masu kasancewa da ita a dukkanin shafukanta na sada a kan adreshin AREWA24.com, facebook.com/AREWA24, da kuma Instagram.com/AREWA24channel.
Domin yin rijista da tsarin kallo a ko’ina a duniya, wato AREWA24 ON DEMAND, sai ku ziyarci http://tv.arewa24.com ko kuma ku sauke manhajar daga IOS App Store, ko Google Play, ko Apple TV, ko Roku Channel Store da kuma Amazon Fire TV.
Domin Karin bayani sai ku tuntubemu a wannan adreshi: info@arewa24.com
Wasan kwaikwayo ne da aka gina shi a kan tarka-tirkar siyasa da cin hanci da rashawa. Labarin yana faruwa ne a wani kirkirarren gari mai suna Alfawa.
Shirin “The 77 Percent” – Shirin Talabijin ne da DW ta shirya domin matasa – wanda tashar AREWA24 da ke Najeriya ta fassarashi zuwa harshen Hausa. Kamar yadda masu daukar nauyin shirin suka bayyana a ganawar su da manema labarai, tashar AREWA24 za ta nuna wannan shirin da harshen Hausa a lokutan da aka fi kallon tashar.
Shirin “The 77 Percent” ya samo sunansa ne daga kason matasan Afirka ‘yan kasa da shekaru 35, sannan aka tsara shi domin nuna rayuwarsu tare da “labarun mahimman abubuwan da suka fuskanta a rayuwarsu”. Shirin na tsawon mintuna 30, an taba nuna shi ne a baya da harsunan turanci da Portuguguese.
Shugaban tashar AREWA24 Jacob Arback, yayin da yake bayani game da karbar shirin, ya bayyana cewa,”Kara shirin “The 77 Percent” a cikin tsarin jadawalin shirye-shiryenmu wata babbar dama ce ga tashar AREWA24 wajen nuna batutuwa na zahiri, da kalubale da labarum nasarori daga matasa a kowanne bangare na fadin wannan nahiya. Muna alfahari da farin ciki da hadin guiwa tare da DW da kuma sadar da wannan shiri mai inganci ga matansamu masu magana da harshen Hausa da kuma iyalansu.”
Daraktan shirye-shiryen Afirka na DW, Claus Stacher, yayin da yake bayani game da kaiwar shirin kashi na 50 a wannan, ya bayyana cewa: “Mun tsara shirinmy ta yadda rukunin matasan da muka yi wannan shiri domin su za su fahimci shirin a matsayin shiri mai kayatarwa, da tsari sannan kuma an yi shi don ‘yan asalin nahiyar Afirka. Tsarin ‘yan Afirka, da tattaunawa da kuma samo mafita yana kara daraja ga abokan hadin guiwarmu na kafafen yada labarai na zamani, da radiyo da talabijin a wannan yanki. Muna da da tabbacin cewa wannan hadin guiwa da tashar talabijin kamar tashar AREWA24 zai kara budede kofofin samun hadin guiwa a nan gaba.
Tushi: DW.COM
Shirine domin fitattun jaruman wasannin kwallon kaf ana duniya, irin rawan da suka taka da kuma gudun mawar da suke badawa.
Shiri ne da yake nuna masu was an motsa jiki na bangare daban daban kama daga kwallon kafa, kwallon Kwando , hockey.
Shrin Dan Birni an dora alhakin wata annoba a kan mai maganin gargajiya, sannan aka yiwa matarsa barazana
Kaddarar Rayuwa wani shirin wasan kwaikwayo ne a kan yadda kaddara ta yi tasiri a rayuwar wasu ‘yanmata biyu ‘yan’uwan juna.
Shirine da ya kunshi labaru da fashin baki daga wannan nahiya game da batutuwan da a ka fi damuwa dasu.